Makiyaya Sun Yanke Hannuwan Manomi A Gonarsa A Borno

Wasu da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne sun sare hannuwan wani manomi bayan sun shiga gonarsa da dabbobinsu a Jihar Borno.

Makiyaya Sun Yanke Hannuwan Manomi A Gonarsa A Borno

Yadda makiyaya a Yobe ke asarar

Wasu da ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne sun yanke hannuwan wani manomi da suka shiga gonarsa da dabbobinsu a Jihar Borno.

Shigar makiyayan da dabboninsu da kuma aika-aikan da suka yi wa manomin ya faru ne bayan arangama da mai gonar da misalin karfe 1.30 na ranar Juma’a.

Majiyar Zagazola Makama ta ce manomin ya yi yunkurin kore makiyayan daga gonarsa, amma suka yi turjiya, inda daya daga cikinsu ya far masa, ya sare masa hannawa biyu.

Sakamakon haka aka garzaya da manomin zuwa Asibitin Gubio, daga bisani aka wuce da shi Asibitin Maiduguri domin ci gaba da kula da lafiyarsa.

Bayan afkuwar lamarin, al’ummar yankin sun kasance cikin zaman dar-dar, inda aka yi gargadin cewa jama’a su guji kauyen Bassam Galomari.

An kuma umarci hukumomin tsaro su dauki mataki da nufin shawo kan rikicin.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS