Makiyaya sun yi taron kara dankon zumunci da Yarbawa
Fulani makiyaya a karkashin jagorancin shugabansu nta miyatti Allah a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello da sarakunan gargajiya na Yarbawa sun yi taron kara dankon zumunci a tsakaninsu, taron da ya gudana a zauren karamar Hukumar Igbora a Jihar Oyo a karshen makon da ya gabata. A cewar Babban Basaraken Yarbawa na yankin Oba Samuel […]
Fulani makiyaya a karkashin jagorancin shugabansu nta miyatti Allah a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello da sarakunan gargajiya na Yarbawa sun yi taron kara dankon zumunci a tsakaninsu, taron da ya gudana a zauren karamar Hukumar Igbora a Jihar Oyo a karshen makon da ya gabata.
A cewar Babban Basaraken Yarbawa na yankin Oba Samuel Adewunyi Adeleye Onidofun na Idofunyi Yarbawa a yankin sun dade suna zaune lafiya da Fulani makiyaya shekaru da dama da suka shude. Ya ce hakan ne ma ya sanya da dama daga cikin Fulanin yankin da harshen Fulatanci da Yarbanci kadai suke iya magana, sannan zumunci da ke tsakaninsu ya fi gaban wasa.
“ Kyakyawar dangantakarmu ce ta sanya ka ganmu tare,” inji shi.
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello ya shaida wa Aminiya cewa kungiyar na yin rangadi a daukacin kananan hukumomin jihar ne don kyautata zaman lafiya a tsakaninsu da abokan zamansu, tare da kyautata alakarsu da inganta tsaro a tsakanin al’ummar jihar.
“Domin haka ne ka ga mun yi wannan taro a nan zauren karamar Hukumar Ibgora da daukacin shugabannin yankin da jami’an tsaro wadanda suka hada da kungiyoyin sa kai na ‘yan kato da gora, wadanda suke dafa wa rundunar ‘yan sanda wajen yakar miyagun ayyuka kamar sata shanu da garkuwa da jama’a,” inji shi.
kungiyar Fulanin ta miyyati Allah ta kaddamar da shugabanta na karamar Hukumar Igbora Alhaji Muhammad Lawal, wanda ya sha alwashin ci gaba da kokarin ganin a ci gaba da zaman lafiya a tsakanin Fulanin yankin da abokan zaman su Yarbawa. Don haka ya ce nan ba da jimawa ba za su kafa kwamiti tuntubar juna a tsakaninsu da abokan zamansu Yarbawa, kana ya yi kira ga Fulanin yankin da su ba su goyon baya domin ci gaban yankin da kasa baki daya.