Makiyaya za su samu Naira dubu 350 kan duk saniya a sabon shirin kiwo na NLTP
Kimanin mako biyu da suka wuce Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa (NEC) ya amince da wani tsari da aka yi wa take da shirin sauya tsarin harkar kiwon dabbobi na kasa (National Libestock Transformation Plan – NLTP), wanda ake sa rai zai lashe makudan kudade har Naira biliyan 91. A baya an samu rigingimu tsakanin manoma […]
Kimanin mako biyu da suka wuce Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa (NEC) ya amince da wani tsari da aka yi wa take da shirin sauya tsarin harkar kiwon dabbobi na kasa (National Libestock Transformation Plan – NLTP), wanda ake sa rai zai lashe makudan kudade har Naira biliyan 91.
A baya an samu rigingimu tsakanin manoma da makiyaya a sassan kasar nan. Wannan sabon shirin tsari ne na hadin gwiwa a tsakanin Ma’aikatar Gona da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa da Mataimakin Shugaban Kasa ke jagoranta tare da gwamnoni 36 na kasar nan da kuma wasu ministoci da suka hada da Ministan Birnin Tarayya da na Tsare-Tsare a matsayin mambobin kwamitin.
Idan har sabon shirin ya fara aiki kamar yadda aka tsara, ana sa ran zai habaka tattalin arzikin kasa da kwatankwacin ribar Naira tiriliyan biyu kuma zai samar da ayyukan yi masu dimbin yawa da masu zuba hannun jari da manoma za su samu kudin shiga.
Daga nan zuwa karshen shekarar 2028 kamar yadda aka tsara, hukumar za ta samu kwatankwacin Naira tiriliyan 8.16 wanda ke wakiltar kashi 2.56 daga matsayin da take kai na Naira tiriliyan 2.9 a ma’aunin tattalin arzikin kasa (GDP) yadda abin zai yi aiki game da shirin sauya tsarin kiwon dabbobi na kasa (NLTP) daga shekarar 2019-2028. A matakin farko sabon shirin zai tallafa wa ci gaban makiyaya a kowace jiha daga cikin jihohin da aka kebe don gwaji, wato Adamawa da Benuwai da Kaduna da Nasarawa da Filato da Taraba da Zamfara wadanda suka sha wahalar zubar da jini a baya.
Haka za a yi amfani da gidajen gona guda hudu (karami da tsaka-tsaki da manya) a kowane gidan gona.
Masu gidajen gona da kananan makiyaya da masu zuba hannun jari za su iya kawo shanunsu zuwa wadannan wurare inda za a ciyar da su da abincin mai kyau za a kuma samar masu da ruwan sha har tsawon kwana 150 wanda zai sa nauyin shanun ya karu daga kashi 200 zuwa 250 zuwa kashi 450 zuwa 500.
Har ila yau za a sayar da shanun da aka kiwata ga mayankar da ke kusa da gidan gona ko a cikin killataciyyar makiyaya.
Kowane wurin kiwon shanun zai iya daukar shanun da yawansu ya kai dubu 3 inda kuma za a yi hakan sau biyu a shekara. Kowace saniya za ta rika samun karuwar nauyi daga kilo 1.2 zuwa 2.5 a kullum ya danganta da yanayin kiwonta.
A mayanka kuma ana sa ran nauyin saniyar zai kai 400 zuwa 450 wato bayan ta shafe tsawon kwana 150 a wurin kiwo wannan shi zai ba manomi damar samun kimanin Naira dubu 350 idan aka sayar da kowane kilo nama a kan Naira 900.
A sabon tsarin za a samar da wasu kudade don kashewa wajen ciyar da shanun, a duk yayin da shanun suka shiga cikin tsarin ciyarwar, mai shanun zai rattaba hannu a kan yarjejeniya tare da mai bayar da bashi don bayar da damar sayar da dukan shanun a kan tsayayyen nauyinsu.
Da zarar an sayar mai bin bashin zai fara rage wani abu na kudin ciyarwar na daga abin da aka sayar na ainihi shi kuma mai shanun zai ajiye abin da ya yi saura a matsayin riba, wannan zai rage yawan fadawa hadari da kuma rashin tabbas na zuba hannun jari.
Dokta Andrew Kwasari shi ne mai bayar da shawara kan shirin agaza wa harkar noma a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa ya ce za a fara gudanar da shirin ne nan ba da dadewa ba.
Ya kara da cewa, masu ruwa- da-tsaki da masu zuba hannun jari sun gana a babban dakin taro na ofishin Shugaban Kasa don tattaunawa a kan lamarin.