Mako 1 da fara yaki, ’yan Ukraine miliyan 1 sun fice daga kasar

Mako daya da fara gwabza yaki, mutum miliyan daya sun fice daga Ukraine, miliyan 12 za su rasa muhallansu

Mako 1 da fara yaki, ’yan Ukraine miliyan 1 sun fice daga kasar

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ’yan kasar Ukraine akalla miliyan daya ne suka tsere daga kasar tun bayan da sojojin Rasha suka kutsa cikinta da yaki a makon da ya wuce.

Shugaban hukumar kula da ’yan gudun hijira ta majalisar, Filippo Grandi, ya bayyana alakaluman ne mako guda bayan barkewar yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine.

Grandi, wanda ya bukaci a tsagaita wuta a tashin hankalin domin tallafa wa miliyoyin jama’ar Ukraine da suke bukatar agaji a cikin kasar, ya ce suna hasashen cewa rikicin na iya raba mutane kusan miliyan 12 da muhallansu a fadin kasar.

Rusha ta bayyana aniyarta ta tattaunawar tsagaita wuta tare da Ukraine bayan da dakarunta suka kai munanan hare-hare a wasu biranen kasar, yayin da rahotanni suka ce ana fada gaba da gaba a titunan birnin Khirkov.

Ukraine ta ce tawagar wakilanta sun kama hanyar zuwa wurin tattaunawa da Rasha a kusa da iyakar kasar Poland, sai dai kuma Ministan Harkokin Wajen kasar, Dmytro Kuleba, ya ce ba za su lamunci a gindaya musu sharuda ba.

Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan mutane sun mutu a sakamakon yakin da ake gwabzawa, yayin da dubbai ke ci gaba da tserewa suna barin kasar domin samun mafaka a wasu kasashe.