Faransa ta fara kwashe ’yan kasarta daga Nijar

Gwamnatin sojin Nijar ta bude iyakokinta kasar; Farasan da kwashen ‘yan kasarta

Faransa ta fara kwashe ’yan kasarta daga Nijar

Faransa ta fara kwashe ’yan kasarta daga Jamhuriyar Nijar, mako guda bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, wanda magoya bayansa suka yi zanga-zangar kyamar Faransa a sassan kasar.

Ministar harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, ta ce jirgin farko ya isa filin jirgi na Roissy Charles de Gaulle da ke birnin Paris a safiyar Larabada dauke da fararen hula 262 ’yan kasar da kuma ’yan kasashen Portugal da Belgium da Lebanon da Habasha da mutum biyu ’yan Nijar.

Ta ce an yi haka ne domin guje wa rikici da rufe sararin samaniya da ke iya ritsawa da ’yan kasar a Nijar; duk da ce a ranar Talata sabuwar gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ta bude iyakokin kasar makwabtanta biyar na Afirka.

Faransa ta fara kwashe ’yan kasar nata ne bayan gwamnatocin sojin da suka yi juyin mulki a Mali da Burkina Faso masu makwabtaka da Nijar sun yi barazanar yakar duk kasar da ta yi kokarin yi wa sabuwar gwamnatin sojin Nijar katsalandan.

Kasashen biyu sun yi gargadin ne bayan kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen Yamma sun yi barazanar amfani da karfin soji domin murkushe juyin mulkin Nijar da kuma dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan karaga.

A ranar Litinin kuma gwamnatin sojin Nijar ta zargi Faransa da neman daukar matakin soji a kasar, zargin da Faransar, wadda dakaruna mutum 1,500 suke Nijar din ta musanta.

Bayan nan ne sojoji masu mulkin Mali da Burki Faso suka sanar cewa a shirye suke su yaki duk wani yunkuri na yi wa takwarorinsu na Nijar katsalandan.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukanta na jin kai a Nijar saboda adawa da juyin mulkin, a yayin da ita babbar kawar Nijar, wato Faransa da dangoginta suka janye duk tallafin da suke ba wa matalauciyar kasar.

Bazoum, wanda babban abokin kasashen Turai irin su Faransa da Amurka dai na tsare a gidansa a hannun sojojin da suka hambarar da shi, tun ranar Laraba da dakarun rundunar tsaron shugaban kasar suka yi masa juyin mulki.

Bayan juyin mulkin ranar Laraba a Nijar ne dai wasu al’ummar kasar suka gudanar da zanga-zangar kyamar Faransa, wadda a ranar Talata ta sanar da fara kwashe kasarta daga Nijar.

Sai dai ta ce duk da haka ba ta da niyyar janye dakarunta da ke aikin samar da tsaro da kuma yakar ‘yan ta’adda a can.

A halin yanzu dai, bayan Nijar da aka yi juyin mulki sau biyar daga shekarar 1960 da ta samu ‘yancin kai, a makwabciyarta Burkina Faso sojoji sun yi juyin mulki sau biyu a cikin shekara guda.

Haka ma sojoji sun yi juyin mulki a sauran makwabtan Nijar irinsu Mali da Chadi da kuma Guinea.