Makomar kungiyoyin Firimiyar Ingila a kaka ta gaba
Aston Villa dai ta kammala gasar ta Firimiyar bana a matsayin ta 7 teburi.
An kammala wasannin gasar Firimiyar Ingila a ranar Lahadi, wanda ke nuna zakarar gasar Manchester City da ta kammala da maki 89 da kuma Arsenal mai maki 84 kana Manchester United mai maki 75 da Newcastle mai maki 71 ne za su wakilci Ingila a gasar Kofin Zakarun Turai.
Bangaren Europa kuwa kungiyoyin Liverpool da ta kammala a matsayin ta 5 da maki 67 da kuma Brighton mai maki 62 a matsayin ta 6 ne za a ga haskawarsu a gasar ta biyu mafi girma a nahiyar Turai.
- Gudun yamutsi ne ya hana ni zuwa rantsar da Abba —Ganduje
- Yadda Kwankwaso ya shiga filin bikin rantsar da Abba Gida-Gida
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta kafa tarihin samun gurbi a gasar Europa Conference league karon farko da za ta samu haskawar a gasar bayan shekaru 13 nasarar da ke zuwa bayan doke Brighton da kwallaye 2 da 1 a wasansu na karshe karkashin gasar ta Firimiya a ranar Lahadi.
Aston Villa dai ta kammala gasar ta firimiyar bana a matsayin ta 7 teburi kuma nasarar ta ranar Lahadi ce ta bata damar tsallake Tottenham wadda a baya ake ganin ita za ta haska a Europa Conference league inda tottenham din ta kammala gasar a matsayin ta 8 bambanci maki 1 kacal tsakaninta da Villa.
Aston Villa wadda ta lashe kofin Europa a shekarar 1982 rabon da a ga kafarta a gasar tun a shekarar 2010 lokacin da Rapid Vienna ta Autria ta doke ta da kwallaye 4 da 3.
Kungiyoyi ukun karshe a teburin na Firimiya da suka kunshi Leicester City da Leeds United da kuma Southampton kai tsaye za su koma doka gasar Championship a kaka mai zuwa wato gasa ta biyu mafi girma a Ingila bayan Firimiya.