Makomar Najeriya: Zabi ya rage wa al’umma
Ranar 15 ga wannan wata na Janairu, rana ce da ke tuna wa ‘yan Najeriya mummunan al’amarin da ya wakana shekaru 49 da suka shude na kisan manyan shugabannin kasar nan, wadanda su ne suka yi fafutukar kwato ma kasar ‘yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. A jerin shugabannin da aka yi […]
Ranar 15 ga wannan wata na Janairu, rana ce da ke tuna wa ‘yan Najeriya mummunan al’amarin da ya wakana shekaru 49 da suka shude na kisan manyan shugabannin kasar nan, wadanda su ne suka yi fafutukar kwato ma kasar ‘yanci daga hannun Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya. A jerin shugabannin da aka yi wa kisan gillar, sun hada da Cif Samuel Ladoke Akintola, Firimiyan yankin Yamma da Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Kur Mohammed da Manjo Zakari Maimalari da sauransu. daukacin wadannan mutane da aka jero sunayensu, babu dan kabilar ibo ko daya, duk kuwa da cewa, shugaban kasa na wancan lokaci Dokta Nnamdi Azikwe Ibo ne, kodayake bai hana aiwatar da wancan juyin mulkin ba.
Masana tarihi na bada hujjojin musababbin faruwar juyin mulkin. Kuma sun kasa dalilan gida biyu: Tattalin arziki da dalilan siyasa.
Dalilin tattalin Arziki: A nan ana batun mallake arzikin danyen man fetur da ke dankare a yankin Neja-Delta. Samuwar wannan arziki yasa Ojuku da sauransu ke ganin za su iya dogaro da kansu ba tare da sauran yankunan Najeriya ba. Wasu kasashe kamar Faransa sun mara wa Ojuku baya, domin su ma in an kafa kasar Biyafara su ci moriyar wannan arzikin gurbataccen fetur. Masu wannan tunani, sun ce hadama da zalama ta kabilar Ibo na son mallake wancan yanki, shi ne, dalilin da ya sa aka shiga yakin.
Masu cewa ai dalilai na siyasa ne suka haddasa wancan juyin mulki da ya rikide ya koma yakin basasa,suna kafa hujja da rikice-rikice masu nasaba da siyasa da suka afku kafin faruwar juyin mulkin.Wadanan rikice-rikice sun hada da rikicin kidaya na shekarun 1962/63, da rikicin jam’iyyar AG da rikicin zaben majalisar tarayya na 1964 da na zaben Kudu maso Yamma na 1965. Sauran dalilan sun hada da siyasar a mutu ko ai rai, musamman salon siyasar Jam’iyyar AG.To koma mene ne dalilin rikicin, juyin mulkin da ma yakin basasa da ya biyo baya, bai magance komai ba, maimakon haka sai ma illoli da ya kara haifar wa Najeriya.
Daga cikin illolin da juyin mulkin da yakin basasar suka haifar, sun hada da asarar dubban rayuka, ciki har da yara da mata, kamar yadda wani marubuci Chinua Achebe ya rubuta a littafinsa na “Wata kasas,” inda ya ce gwamnatin tarayya ta yi amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, inda ya ce dubban daruruwan yara sun mutu a yankin Kudu maso Gabas sakamakon yunwa.
Ya ce saboda yunwa, sai da naman kadangare ya zama tamkar turare dan goma.Yakin ya haddasa asarar dukiyoyi da ba su lissaftuwa. Uwa uba, baya ga rusa tsarin dimokuradiyya, yakin ya kara raba kawunan ‘yan Najeriya, kawunan da duk da shirin Gowon na kirkiro da aikin hidimar kasa (NYSC) da gina makarantun gwamnatin tarayya na hadin kai ba su hadu ba. Har yau da muke kawunan ‘yan Najeriya a rarrabe suke. Kowa yana ganin wata kabila da ba tashi ba banza. Kowa ba ya ganin kowa da gashin arziki.
Ga shi mun shigo shekarar 2015, shekarar da aka yi hasashen kasar za ta wargaje, za a yi kaza da kaza duk marasa dadi, za mu iya cewa ke nan har yanzu al’ummar Najeriya ba mu koyi wani darasi daga yakin basasar watanni 30 da muka yi ba? Za mu iya cewa har yanzu bayan wadannan shekaru, wasu ‘yan Najeriya na kiraye-kirayen a raba kasar? Shin yake-yaken da ke faruwa a Sudan da wanda suka faru tsakanin Eriteria da Ethiopia, wacce tsiya suka haifar masu? Shin a lokacin da Arewacin Amurka da Kanada ke kokarin hadewa, lokacin da Tarayyar Turai ke kara dunkulewa, mu kuma sai kokarin kiran ai gutsin-gutsin da kasar ake.Ana kafa hujja da sunan addini da kabilanci, shin idan muka rugurguza tarayyar,shin hakan zai kawo karshen kabilanci da bangaranci a sababbin kasashen da za mu kafa? A Katsina kawai,z aka ji wasu ‘yan siyasa na batun yankin ‘Karaduwa’ ko Daura’ ko cikin Ganuwa,’ shin wannan bai isa ya nusar da mu cewa karya ce rusa Najeriya, domin yin haka ba zai magance komai
ba, sai dai ma ya kara kirkiro da wasu sababbin matsaloli da a da ba mu san da su ba.
Ko mun ki ko mun so, abubuwan da suka hada mu, sun fi abubuwan da suka raba yawa.
Na Farko mu duka muna a nahiya daya, yankin Afirika ta Yamma, mu bakake ne, harsunanmu suna kamanceceniya da juna, sana’oinmu iri daya, wato nomad a kiwo da kasuwanci. Mun yi auratayya har ma mun hayayyafa. Akwai Hausawan Yarbawa a Legas da Shagamu, kamar yadda wasu Yarbawa suka zama Katsinawa a Funtuwa. Duk wadannan ba su isa mu yi hakuri mu zauna tare cikin mutunci da girmama juna ba, sai mun tarwatse? Yau Rasha tana kokarin kwace Kirimiya daga Ukraine ta hade su, mu yi kuma mun bar yankin Barno da Yobe sun koma karkashin kungiyar Boko Haram. Kullum sai maganganun kabilanci da addini ya dame mu.
Daga karshe zan rufe da kalaman Martin Luther King Junior, ya ce kodai mu zauna tare a matsayin ‘yan uwa, kuma tsintsiya madaurinki daya, ko kuma mu zabi tarwatsewa. Zabi ya rage gare mu.
Bishir Dauda, Babban Sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa ne. 08165270879.