Makomar ’yan Najeriya a mahangar almajiran Malam Zakzaky

A yau kuma, muna gabatar muku da wani tsokaci ko sharhi daga alkalamin MALAM TANKO MANI (08062216811), wanda ya wallafa shi a turakarsa ta Facebook. Irin muhimmanci da tasirin tsokacin a wannan lokaci, shi ya sanya muka ga cewa ya dace mu gabatar da shi a nan. Ga abin da yake cewa: A yau, a […]

Makomar ’yan Najeriya a mahangar almajiran Malam Zakzaky
Makomar ’yan Najeriya a mahangar almajiran Malam Zakzaky

A yau kuma, muna gabatar muku da wani tsokaci ko sharhi daga alkalamin MALAM TANKO MANI (08062216811), wanda ya wallafa shi a turakarsa ta Facebook. Irin muhimmanci da tasirin tsokacin a wannan lokaci, shi ya sanya muka ga cewa ya dace mu gabatar da shi a nan. Ga abin da yake cewa:

A yau, a tsakanin ’yan Najeriya, babu mai tababar tabarbarewar al’amuran kasar nan ta dukkan fuskokin rayuwar da aka san dan Adam da ita. Shin ta fuskar tattalin arziki za a kalli lamarin ko ta siyasa? Shin ta fuskar tsaro za a kalla ko ta harkokin yau da kullum? Ko ma dai ta wace fuska ce za a kalla, gaskiyar magana ita ce, komai na kasar nan ya tabarbare.
A irin wannan yanayi ne lokacin zabe ya kunno kai, dama ta samu ga ’yan Najeriya wacce za su iya sauya gwamnatin da suke gani tana da hannu a tabarbarewar dukkan al’amuransu. Don haka sai kowa yake ta murna, musamman saboda ganin cewa shugaban sabuwar gwamnatin da ake so a sauyata domin gazawarta, mutum ne da aka shaide shi da gaskiya da rikon amana da rashin wargi da jajircewa a kan aikin ci gaban jama’a.
A kan haka sai kusan dukkan ’yan Najeriya, musamman talakawansu suka tattara hankalinsu ga wannan bawan Allah, suka yi tanade-tanadensu da suke ganin cewa za su tabbatar da shi a matsayin sabon shugabansu a lokacin zabe. Dare da rana, kowa fata yake yi da burin zuwan wannan rana ta zabe, domin ya bi kadin hakkinsa wanda tafarkin dimokuradiyya ya ba shi, wato zaben wanda yake so ya shugabance shi ko ya wakilce shi a matakin jiha ko tarayya.
Wani abu mai ban sha’awa game da wannan zabe shi ne, babu la’akari da addini, kabila, bangare ko kungiya. Kusan kowa yana buri da fatan samun wannan sauyi, ba kuma komai ya haifar da hakan ba face yadda aka samu gwamnati mai ci da hannu dumu-dumu cikin abubuwan da ke jaza wa jama’a wahalar rayuwa. Don haka sai aka wayi gari, da dan Shi’a da dan Izala da dan darika da Musulmi da Kirista da dan Arewa da dan Kudu da Bahaushe da Inyamuri da Bayarabe, kusan kowa yana kewa da zumudin son zuwan wannan rana ta zabe, don kawai ya fanshe haushinsa na rashin yi masa aiki ta hanyar zaben wadanda yake da tabbacin za su fi na baya kamantawa.
Wannan zaman tsimaye da ’yan Najeriya suke yi, suna yi ne saboda wata hanya mai sauki ta sauyin gwamnati ba ta bayyana gare su ba zuwa yanzu. Don haka iyakar abin da za su iya yi ke nan, wato su jefa kuri’unsu ga wani shugaban, ba wannan ba bisa ga yadda tafarkin dimokuradiyya ya tanadar musu.
Akwai juyin mulkin soja, wanda suke ganin yana da illoli saboda dabi’arsa ta karan-tsaye wurin mulkin jama’a. Kuma yana haifar da kashe-kashe, on haka ba sa la’akari da shi wurin sauyin sabuwar gwamnati.
Akwai kuma juyin-juya-hali, wanda rashin manhaja kyakkyawa da rashin shugaba nagari, tare da rashin daidaton tunanin ’yan Najeriya a kan yawancin al’amuran da suka shafi rayuwarsu sakamakon rabe-raben kabilunsu da kungiyoyinsu da yankunansu sun sa babu ma mai tunanin yiwuwarsa; domin ba zai magance matsalar kasar ba, sai ma ya sake rura wata sabuwa.
Don haka suka samu yakinin cewa, sassaukar hanya guda tal ta sauya gwamnati, ita ce dai wannan dama ta sake zabe a bayan kowace shekara hudu.
A cikin irin wannan lokaci na jira da fata da buri ne, kwatsam sai aka samu almajiran Malam Zakzaky, wadanda aka sani da babatun son kawo sauyin gwamnati fiye da kowa, suna ganin wannan hankoron zaben da ’yan Najeriya suke yi domin kawo sauyi, ba komai ba ne face aikin banza. Suna da dalilai biyu zuwa uku da suke kafawa a matsayin hujjarsu.
Na daya, wasunsu suna ganin tsarin dimokuradiyya, tsari ne na kafirci. Me ya kafirta shi? Ba su iya yi mana bayani ba.
Na biyu, wasunsu kuma suna ganin wai saboda ba a yin zaben tsakani da Allah ne. Wai ba wanda ya ci ake ba ba.
Na uku, wasunsu kuwa gayya ce kawai suke bi ga ra’ayin masu rinjaye, tunda uwar kungiyarsu ba ta yi, to su ma ba za su yi ba.
A tashin farko dai, Malam Nasir Jafar ya yi kokarin fitar musu da fatawowin malaman Shi’a na duniya da ke halasta zabe a karkashin tsarin da ba na Allah ba, don ya zama amsa ga masu kafa dalili na farko. Amma maimakon su fahimta kuma su yarda, a’a, sai suka karkata ga cewa, to wai a fito musu da inda aka wajabta zaben. Wai su ba su ce dama ba halal ba ne, a’a, wai tambayarsu ita ce, ta yaya ya zama wajibi?
Bayan nan, malamin ya yi kokarin nuna musu cewa, koda ya kasance ba wanda aka zaba ake ba mukamin ba, to dai duk da haka yana da kyau su fito zaben domin barranta kansu daga wanda suke cewa shi ne ya kashe ’ya’yan malaminsu kuma yake shirin kashe musu shi kansa malamin. Ya yi kokarin kafa musu hujjojin hankali masu yawa don dai kawai su gane cewa, za su taimaki Najeriya in har suka yi amfani da tarin yawansu a wurin dakushe yiwuwar nasarar shugaban da suka yi ittifakin cewa azzalumi ne. Kazalika bisa ga dogaro da abubuwan da ke aukuwa a kasar, alamu na nuna cewa, a wannan karon, zabe ne na sosai za a yi. Wannan ne ma ya sa, hankalin ’ya’yan jam’iyya mai mulki ya tashi ainun. Amma duk da haka, wadannan almajirai na Malam Zakzaky suka yi kememe, suka tubure.
Salon da suke bi wurin tuburewa da rashin kallon alherin wannan lamari da ya shafi makomar kasar nan, ya isa sanya mai kulafuci tambayar, to wai shin, mene ne wadannan almajirai na Zakzaky suke da shi ne wanda ya fi wannan din? Shin wane sauyi ne za su iya kawo wa kasar nan wanda ya dama wannan ya shanye? To a nan fa gizo ke sakar, domin dai wannan tambaya tana da kamar wuya a gare su.
Amma an ga yawancinsu da suka yi ta ’yar tankiya da mujahid Nasir Jafar, suna cewa wai su za su samar da sauyi ne irin wanda Imam Khumaini ya samar a kasar Farisa. Yaya za a yi su iya samar da sauyin? Ba su ce komai a kai ba.
A ka’idar sauyi irin na juyin-juya-hali, masana sun ce ba ya samuwa sai da ababe guda biyar: Na farko, hazikin shugaba mai iya jagoranci. Na biyu, wani adadi mai dan yawa na jajirtattun waziran shugaban, wadanda suke da makamanciyar hazakarsa da kuma nagartacciyar sadaukarwa a kan juyin. Na uku, kammalalliyar manhajar da za a yi aiki da ita yayin da aka samar da juyin. Na hudu, kyakkyawar niyyar son samar da juyin daga wurin shugaba da waziransa.
Na biyar, amincewar akasarin jama’ar kasar da za a samarwa da juyin.
Mai karatu kalli wadannan ka’idoji biyar, kuma ka auna su da gwagwarmayar Malam Zakzaky wanda a yau ya kai shekara 36, shin don Allah, an samu daidaito a cikin awon ko ba a samu ba? Shin za ka iya fitar da ka’idoji biyu zuwa uku cikin biyar din nan wadanda kake da tabbacin lalle za a iya samun su a cikin gwagwarmayar Malam Zakzaky? Duba da kyau ka gani!
Tabbas, za ka ga cewa gwagwarmayar ba ta da komai a zahirinta da badininta. Jagorancinta bai da wata masaniya ta jagorancin al’umma face dauke-dauken hotuna da fararen malamai a kasashen ketare. Waziran kuwa, jagorancin da kansa ya yi shaidarsu da cewa “sun fi azzaluman kasar nan zama dagutu.” Ka ga kuwa babu wata sadaukarwa da masu dabi’ar “dagutu” za su iya bayarwa bare har a samu juyin-juya-hali. Game da manhaja kuwa, ya isa zama nakasun wannan gwagwarmaya, a ce yau shekararta 36, amma babu rubutaccen littafin da zai zamar wa ’ya’yanta alkiblar bi. A cikin gwagwarmayar, babu littafi mai kamar kawa’idi na ‘Laa ina ma’anar Laa.’ Kyakkyawar niyya kuwa, ayyukan mutum ke tabbatar da ita. In kuma har haka ne, to akwai katuwar alamar tambaya game da wannan batu. Domin babu yadda za a yi hankula su aminta da kyakkyawar niyyar jagoran da kiri-kiri yana ji, yana gani amma ya tsallaka ya yi tafiyarsa kasashen ketare da iyalinsa a daidai lokacin da raunanan mabiyansa ke neman tallafin asusun dan abin hasafin da zai maida musu da komadar rayuwa daga wuju-wujun da gwagwarmayar ta sabbaba musu. Akwai abin tambaya a nan kam amma ga mai hankali. Game da amincewar ’yan kasa ga juyin da wannan gwagwarmaya take son samarwa kuwa, shi kam, babu batun ne ma sam-sam, domin yaushe jagorancin wannan gwagwarmaya ya daina jin dadin tafarkin “Dibide and Rule” a tsakanin ’yan malam sak da umara’u, bare har ya iya dinke barakar kabilanci da kungiyanci da bangaranci da suka addabin kasar?
Da duk wannan nake hattamawa a takaice da cewa, hakikanin abin da ke cikin mahangar almajiran Malam Zakzaky game da makomar kasar nan, ba sauyi ba ne, a’a! Kawai dai ci gaba ne da daskarewa a cikin wannan hali na ni-’ya-su da jama’a suke ciki ba tare da sun samar da wata mafita ba face ta kira zuwa ga bin jagorancin da bai da cikakken ikon kuzarin sarrafa hatta gidansa. Allah Ya sauwake!