Makon da manya suka kwanta dama
A cikin mako daya Najeriya ta yi asarar wasu daga cikin manyan ’ya’yanta da suka hada da fitaccen masanin shari’ar nan, tsohon Babban Jojin Jihar Imo, kuma tsohon Alkalin Kotun koli, Mai shari’a Chukwudifu Oputa, wanda ya rasu yana da shekara 91. Sai dai iyalan mamacin ba su bayar da cikakkiyar sanarwa game da mutuwarsa […]


A cikin mako daya Najeriya ta yi asarar wasu daga cikin manyan ’ya’yanta da suka hada da fitaccen masanin shari’ar nan, tsohon Babban Jojin Jihar Imo, kuma tsohon Alkalin Kotun koli, Mai shari’a Chukwudifu Oputa, wanda ya rasu yana da shekara 91. Sai dai iyalan mamacin ba su bayar da cikakkiyar sanarwa game da mutuwarsa ba.
Mai shari’a Oputa, shi ne mahaifin shararren mawakin nan Charley Boy, ya kuma shahara ne a lokacin da ya jagoranci kwamitin binciken keta haddin dan Adam da gwamnatin Obasanjo ta kafa.
An haifi marigayin a 1923, a karamar Hukumar Oguta da ke Jihar Imo.
Shi ma tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kwara Alhaji Adamu Attah ya rasu a cikin makon. Alhaji Adamu Attah ya rasu ne a gidansa da ke Abuja, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. Ya kuma rasu yana da shekara 88.
Tuni aka yi jana’izar marigayin a garin Okene da ke Jihar Kogi, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Marigayi Alhaji Adamu Attah, wanda ya zama Gwamnan Jihar Kwara a 1979, a karkashin Jam’iyyar NPN, ya zama Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya a 1967, sannan ya zama dan majalisar gyaran kundin tsarin mulki a 1976.
Gwamnonin Jihohin Kogi da Kwara sun aika wa iyalansa ta’aziyya.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Legas Michael Otedola ya rasu yana da shekara 88. Bayanan da manema labarai suka samu, sun bayyana cewa ya rasu ne sanadiyyar cutar shanyewar barayin jiki a kauyensu Odoragushin da ke karamar Hukumar Epe.
Marigayin shi ne mahaifin hamshakin dan kasuwar nan Femi Odetola, Shugaban Kamfanin Harkar Mai na Zenon.
Uwargidan mamacin Doja Otedola ta bayar da sanarwar rasuwarsa, inda ta ce za a sanar da ranar jana’izarsa nan gaba.
A can zauren taron kasa kuwa, daya daga cikin wakilansa, Dokta Muhammad Jumare daga Jihar Kaduna ne ya rasu. Jumare ya rasu ne a ranar Litinin a Abuja, kuma tuni aka yi jana’izarsa bisa ka’idojin adddinin Musulunci. Daga cikin wadanda suka halarci jana’izarsa akwai Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero da Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, sai Farfesa Mahmood Yakubu, Mataimakin Sakataren Kudi da Harkokin mulki da ya wakilci shugabannin taron. Kakakin taron, Akpandem James ya ce marigayin ya rike mukamai da dama a jiha da tarayya.
Daga Yola kuma Alhaji Halilu Ahmed Chiroma,surukin Janar Muhammadu Buhari ne Allah Ya yi wa rasuwa. Marigayin mahaifin matar Buhari, A’isha Halilu Buhari, ya rasu ne yana da shekara 81, bayan ya kwanta barci a daren ranar Larabar makon jiya.
Marigayi ya rasu ya bar ’ya’ya 24 da jikoki 44, da suka hada da Chubado Halilu na Babban Bankin Najeriya a Kaduna da Ahmad Halilu na Bankin Zenith da Muhammadu Halilu.
An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Daga cikin wadanda suka halarci zaman ta’aziyarsa akwai Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Janar Muhammadu Buhari.