Makon fallasa: Wadanda ake zargi da cin kudin sayo makamai na kara fitowa

A ciki mako guda da ya gabata an rika samun fallashe-fallashe dangane da karkatar da kudin sayen makamai zuwa harkokin siyasa da ake zargin ofsihin tsohon Mashwarcin Shugaban kasa Sambo Dasuki da yi, inda aka ruwaito cewa tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Bashir Yuguda ya shaida wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki […]

Makon fallasa: Wadanda ake zargi da cin kudin sayo makamai na kara fitowa

A ciki mako guda da ya gabata an rika samun fallashe-fallashe dangane da karkatar da kudin sayen makamai zuwa harkokin siyasa da ake zargin ofsihin tsohon Mashwarcin Shugaban kasa Sambo Dasuki da yi, inda aka ruwaito cewa tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Bashir Yuguda ya shaida wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) cewa ya bayar da Naira miliyan 600 ga shugabannin kwamitocin tuntuba na Jam’iyyar PDP  don zaben 2015.
Ya jero wadanda suka karbi kudin da cewa su ne; Bode George (Kudu maso Yamma) da Ambasada Yerima Abdullahi (Arewa maso Gabas) da Peter Odili (Kudu maso Kudu) da Attahiru Bafarawa (Arewa maso Yamma) da Jim Nwobodo (Kudu maso Gabas) da kuma Ahmadu Ali (Arewa ta Tsakiya).
Ya ce ya umarci kamfanin Jabbama Limited ya tura Naira miliyan 300 zuwa kamfanin kadarori na BAM Properties da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Alhaji Bello Haliru ya ba shi asunsunsa.
Yuguda, wanda ya yi wadannan zarge-zarge a bayanin shaida da ya rubuta tare da rantsuwa ya ce ya aike da Naira miliyan 200 ga tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kebbi a karkashin Jam’iyyar PDP, Bello Sarkin Yaki.
Ya ce tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi, ya samu Naira miliyan 100.
Yuguda yana fuskantar shari’a ne tare da tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa da dansa Sagir Attahiru da kamfanin Dalhatu Inbestment Limited.
Ana sa ran tsohon Ministan ya yi bayani kan Naira biliyan uku da miliyan 50 ciki har da Naira biliyan daya da miliyan 100 na kudin da suka fito daga ofishin Dasuki da kuma wasu kudin Gwamnatin Tarayya da ya tura wa kamafanin Jabbama Ada Global Serbices.
Ya ce, an ba kowane shugaban kwamitin tuntuba kan zaben Naira miliyan 100, kuma ya bayar da kudin ne tare da rakiyar Farfesa Rufa’i Alkali wanda tsohon Mashawarcin Shugaban kasa ne kan Harkokin Siyasa. Kuma Ya umarci Kamfanin Jabbama Limited, ya tura Naira miliyan 100 ga Kamfanin Dalhatu Limited bisa bukatar hakan daga Attahiru Bafarawa.
“Ina son in kara da cewa a wani lokaci cikin watan Fabrairun bana, na umarci Kamfanin Jabbama ya tura Naira miliyan 300 ga Kamfanin Kadarori na BAM Properties. Halliru Bello daya daga cikin mutanen da NSA ya ce in bai wa kudi ne ya ba ni asusun. Kuma na tuna Mahmud Aliyu Shinkafi ma an aike masa da Naira miliyan 100 bisa umarnin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan tsaro.”
 Ya ce bai san daraktocin Kamfanin Dalhatu Inbestment Limited ba, amma ya tura wa asusun kamfanin Naira biliyan daya da rabi bisa umarnin dalhatu Bafarawa wanda Kamfanin Jabbama ya karbo daga tsohon mashawarcin Shugaban kasa kan tsaro.
Ana tuhumar Kanar Sambo Dasuki da Shu’aibu Salisu tsohon Daraktan Kudi da Mulki a Ofishin Dasuki da  Bashir Yuguda da karkatar da wadannan kudi domin yi wa PDP kamfe a zaben 2015, wanda laifin ne da za a iya hukunta su a karkashin sashi ne 315 na dokar Final Kod, doka mai lamba Cap 532, Kundi na 4, LFN 2004.
Tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa ya amince cewa ya karbi Naira miliyan 100 daga Yuguda ta hannun Sagir Attahiru. A bayaninsa ga Hukumar EFCC, ya ce ya san Bashir Yuguda, kuma ya kira shi ya gaya masa cewa akwai kudin da aka bayar ga kwamitin kamfe na Arewa maso Yamma inda ya tambaye shi nawa ne ya ce Naira miliyan 100, sai ya nemi ya ba Sagir inda ya yi haka, kuma an aike da kudin ga kwamitocin kamfe na jihohi a ranakun 20 da 21 ga Fabrairu, 2015 don yi wa PDP kamfe din babban zaben. “Amma bai shaida min daga ina kudin ya fito ba, kuma ban tambaye shi daga ina kudin ya fito ba. Sagir dana ne kuma na umarci Sagir ya aike da kudin ga shugabannin kwamitocin jihohi na kwamitin kamfe na PDP na Arewa maso Yamma.”
Bafarawa da dansa, Sagir Attahiru da kuma Kamfanin Dalhatu Inbestment Limited ana so ne su yi bayani kan sama da Naira biliyan 18 da miliyan 90, inda ake zargin wani bangare na kudin an ba PDP ne a karkashin shirin “Shirin Kame Arewa maso Yamma.” Kuma kudin ba su hada da Dala miliyan tara da dubu 809 da ake zargin tsohon Minista Yuguda ya karba daga ofishin Dasuki a tsakanin 23 ga Disamban, 2014 da 10 ga Fabrarirun 2015.
A martanin tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Cif Bode George, ya bayyana Bashir Yuguda, da makaryaci, inda ya ce sabanin abin da aka ruwaito cewa Yuguda ya ba shi Naira miliyan 100 a matsayinsa na shugaban kwamitin tuntuba ba Jam’iyyar PDP a Kudu maso Yamma, Dala dubu 30 (kimanin Naira miliyan shida) aka ba su 18. Ya ce, idan aka raba Dala dubu 30 ga mutum 18 kowannensu ya samu Dala 1,666, kuma an bayar da kudin ne a matsayin kudin sufuri da dakunan kwana da abinci ga wakilan kwamitin.
Ci gaba a shafi na shida