Makon fallasa: Wadanda ake zargi da cin kudin sayo makamai na kara fitowa

ce gaba da na shafi na uku Ana zargin Dasuki da amso Dala miliyan 47 (kimanin Naira biliyan tara da miliyan 400) daga Babban Bankin Najeriya domin rarraba wa mambobin Jam’iyyar PDP.A martanin da Sanata Iyorchia Ayu ya mayar ya ce ya karbi Naira miliyan 345 daga Kudin sayo makaman da ake takaddama, a matsayin […]

Makon fallasa: Wadanda ake zargi da cin kudin sayo makamai na kara fitowa
Makon fallasa: Wadanda ake zargi da cin kudin sayo makamai na kara fitowa

ce gaba da na shafi na uku

Ana zargin Dasuki da amso Dala miliyan 47 (kimanin Naira biliyan tara da miliyan 400) daga Babban Bankin Najeriya domin rarraba wa mambobin Jam’iyyar PDP.
A martanin da Sanata Iyorchia Ayu ya mayar ya ce ya karbi Naira miliyan 345 daga Kudin sayo makaman da ake takaddama, a matsayin kudin tuntuba kan matsaloli masu wahala.
Sanata Ayu wanda ya fito daga Jihar Benuwai ya ce lokacin da ya yi aiki a Majalisar Tsaro ta kasa a matsayinsa na Ministan Harkokin Waje, ya ilimantu da wasu sassa na harkar tsaro. Ya ce duk kudin da aka tura wa asusun kamfanin domin tuntuba ne kan harkokin tsaro da na zabe. Kuma lokacin da Kanar Sambo Dasuki ya kama aiki a shekarar 2012 ya tunkare shi kan ya taimaka bisa lura da cewa shi malamin kimiyyar rayuwa ne da kuma rawar da ya taka a baya a gwamnati.
Ya shaida wa Aminiya cewa ya bayar da shawarar da ta kamata a duk lokacin da aka tuntube shi kan al’amura masu wahala. “Kuma ya san ina da ilimi kan harkokin siyasar kasar nan da kwarewa kan gasa a tsakanin jam’iyyun siyasa. Wannan ne ya sanya a 1999, Janar Olusegun Obasanjo ya nada ni Darakta Janar na kamfe dinsa,” inji shi.
Ofishin Mataimakin Shugaban kasa Muhammd Namadi ma an zarge shi da cewa ya rika karbar Naira miliyan 20 duk wata daga ofishin Dasuki.
Tsohon akanta na biyu Ibrahim Idris Wambaine ya bayyana haka, inda ya ce wasu mukarraban Shugaban kasa ma sun ci gajiyar wannan watanda daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro da aka yi amfani da kamfanoni biyar ana bayar da kudi ga wasu daga ofishin.
A takardar rantsuwar da aka gabatar gabatan Babban Kotun Tarayya da ke Abuja, ya ce: “A Disamban 2014, na dauki tsabar kudi Naira miliyan hudu zuwa gidan Kanar Madaki (mai ritaya) da ke Wuse II a Abuja. Na kai kudi da dama ga Doyin Okupe da Ahmad Idris mai tallafa wa Dasuki da dogarin matar tsohon Shugaban kasa Patience Jonathan a matsayin alawus-alawus din gudanar da aiki na wata-wata.
Shi kuwa Sanata Jim Nwobodo musanta karbar Naira miliyan 100 daga tsohon Minista Bashir Yuguda.
Wata sanarwa da Kakakinsa John Okoreni, ya fitar ya ce babu gaskiya a rahoton da ke cewa maigidansa ya karbi kudi daga tsohon Ministan.
Nwobodo shi ne Shugaban Kwamitin Tuntuba na Kmfe din takarar Shugaban kasa a Kudu maso Gabas da suka hada da jihohin Abiya da Anambra da Ebonyi da Enugu da Imo.Ya ce kudin da kawai da kwamitin ya karba don gudanar da ayyukansa shi ne Naira miliyan 100 daga Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Dokta Adamu Mu’azu.
Shi ma shugaba kuma Babban Editan Jaridun Thisday, Nduka Obaigbena, ya ce tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Tsaro Sambo Dasuki, ya biya shi Naira miliyan 670 a matsayin diyya kan hare-haren da aka kai wa ofisoshin jaridunsa a Abuja da Kaduna a shekarar 2012. Kuma ya karbi Naira miliyan 120 a madadin kungiyar Masu Gidajen Jaridu ta Najeriya (NPAN) da gidajen jaridu 12 da suka nemi a biya su diyya kan “kame musu jaridu ba bisa doka ba da hana jaridunsu isa kasuwa da sojoji suka yi Abuja da wasu birane,” inji shi.
Ya ce a matsayinsa na Shugaban NPAN ya yi haka ne don ya dakile yunkurin da wasu jaridu suka yin a kai gwamnati kotu kan hakan.
Sai dai gidan jaridar Guardian ya musanta karbar Naira miliyan 10 da aka ce an ba gidajen jaridun, inda ya ce asarar Naira dubu 450 ya yi don haka ba zai karbi Naira miliyan 10 a matsayin tallafi ba. Shi kuma Kamfanin Buga Jaridun Daily Trust da Aminiya ya ce asarar Naira miliyan 11 na jaridun da aka buga inda sojojin suka hana a sayar. “Shugaban NPAN ya gaya mana cewa an amince a biya mu Naira miliyan 10 sakamakon shiga tsakani da NPAN ta yi kuma tana kokarin neman kudi don fara ayyukanta, don haka aka yanke Naira miliyan daya domin amfani kungiyar aka biya kamfaninmu Naira miliyan tara a matsayin diyya,” inji wata sanarwa dauke da sanya hannun Babban Editan Kamafin Malam Mannir dan Ali.
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi II, wanda aka zarga da ba ofishin Dasuki Naira biliyan 40 lokacin yana Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya musanta zargin. Lokacin da kafar labarai ta TheCable ta tuntube shi a ranar Litinin kan lamarin Sarki Sanusi II ya ce: “Wannan ba gaskiya ba ne. Na san dokokin almundahana da kudin gwamnati, kuma babban laifi ne. Babban Banki ne babban mai sa ido da aka dora wa alhakin tabbatar da an kawo karshen almundahanar kudade,” inji shi.
Ita ma fadar Shugaban kasa ta wanke Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga zargin da ofishin Dasuki ya yi na cewa ya ba shi kyautar Dalar Amurka dubu 300(kimanin Naira miliyan shida) daga cikin kudin da ake zarginsa da almubazzarantawa.
Kakakin Buhari Mista Femi Adesina ya ce Buhari ya shaida wa Hukumar EFCC cewa shi ba a ba shi ko anini ba, amma dai ya san Dasuki ya ba shi motoci biyu, daya mai sulke da kuma wata lokacin da Boko Haram suka kai masa hari a garin Kaduna.
Saboda haka Adesina ya ce Dasuki soki burutsunsa kawai yake amma bai ba Buhari ko kwabo ba.
Wadanda ake zargi da cin gajiyar kudin sayo makamai:
1. Naira biliyan 1.25 ga Kamfanin Acacia Holdings Limited
2. Naira biliyan 2.120 ga Kamfanin DAAR Inbestment and Holding Company Limited
3. Naira miliyan 90 ga Kamfanin Brains & Hammers Ltd don sayen gidan kasaita mai dakuna bakwai.
4. Naira miliyan 380 domin tallafa wa sake zaben wakilan Majalisar Wakilai.
5. Naira miliyan 750 ga asibitin Reliance Referral Hospital Limited domin addu’a ta musamman.
6. Naira 670 an biya mawallafin jaridun ThisDay Publisher, Nduka Obaigbena.
7. Naira miliyan 260 ga Tony Anenih.
8. Naira miliyan 345 ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Iyorchia Ayu.
Da sauransu da dama