Makon gobe shari’ar cocin Synagogue za ta kare
Shari’ar da ake yi tsakanin shugaban cocin Synagogue, TB Joshua da Gwamnatin Jihar Legas ta zo karshe, inda kotun da ke sauraren shari’ar ta sanya ranar 8 ga watan Yuni na bana domin yanke hukunci. Alkalin kotun mai shari’a Oyetade Komolafe ya sanya ranar ne bayan da bangarorin da ke jayayya da juna suka gabatar […]
Shari’ar da ake yi tsakanin shugaban cocin Synagogue, TB Joshua da Gwamnatin Jihar Legas ta zo karshe, inda kotun da ke sauraren shari’ar ta sanya ranar 8 ga watan Yuni na bana domin yanke hukunci.
Alkalin kotun mai shari’a Oyetade Komolafe ya sanya ranar ne bayan da bangarorin da ke jayayya da juna suka gabatar da hujjojinsu na karshe kan dalilan da suka janyo rushewar ginin cocin, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 116 wadanda mafi yawancinsu ’yan kasar Afirika Ta Kudu ne da na kasar Zimbabuwe.
Gwamnatin Jihar Legas ce ta kafa kotun a karkashin dokar gine-gine don ta gano musababbin rushewar ginin cocin kuma kotun ta yi fiye da watanni takwas tana zama.
Jim kadan da rushewar ginin, hukumar cocin ta yi ikirarin cewa ginin ya rushe ne sakamakon wani jirgi da ya rika shawagi a saman cocin jim kadan kafin rushewar ginin.
To amma Gwamnatin Jihar Legas ta dage a kan cewa ginin da cocin ta yi ba bisa ka’ida ba shi ya janyo rushewar ginin. Shaidu iri-iri wadanda suka hada da kwararru kan harkar gine-gine da shaidun gani da ido sun bayyana a gaban kotun suka bayar da bahasi kan dalilin da ya janyo rushewar ginin mai hawa shida.
Lauyoyi bangarorin biyu da kwararru sun yi zazzafar muhawara yayin da suke bayar da hujjojinsu a ciki da wajen kotun.
Sai dai jama’a sun zura ido suga zuwan ranar da kotun za ta yanke hukunci don ganin wainar da za a toya a ciki da wajen kotun.