Makon lafiya: Kano ta raba maganin zazzabin cizon sauro kyauta
Gwamnatin Jihar Kano ta nanata niyyarta ta kyautata kiwon lafiya ga jama’ar jihar inda ta raba maganin zazzabin cizon sauro kyauta ga jama’a a lokacin bikin makon lafiya a kan abin da ya shafi mata masu juna ko biki da kuma jarirai. A lokacin da yake kaddamar da shirin a garin Indabo a karamar Hukumar […]
Gwamnatin Jihar Kano ta nanata niyyarta ta kyautata kiwon lafiya ga jama’ar jihar inda ta raba maganin zazzabin cizon sauro kyauta ga jama’a a lokacin bikin makon lafiya a kan abin da ya shafi mata masu juna ko biki da kuma jarirai. A lokacin da yake kaddamar da shirin a garin Indabo a karamar Hukumar Wudil, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati da hadin gwiwa abokan huldarta a wannan bangare sun samar da abubuwan da ake bukata don ganin an samu cikakkiyar nasara. A jawabin Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Abubakar Labaran Yusuf ya ce ma’aikatarsa za ta rarraba kayayyakin da suka shafi maganin zazzabin cizon sauro a cibiyoyin lafiya da ke jihar. A jawabin Hakimin Wudil Alhaji Sarki Ibrahim Abdul ya gode wa gwamnatin jihar ne bisa zabar Wudil a matsayin wurin kaddamar da shirin, inda ya yi alkawarin ba da goyon bayan al’ummar yankin ga shirye-shiryen gwamnati, musamman wadanda suka shafi harkar lafiya.