Makon ruwan bama-bamai a Arewa
A wannan makon tun daga ranar Lahadi zuwa Talatar da ta gabata yankin Arewa ya ga tashin hankali saboda tashe-rashen bama-bamai da aka samu a gururruwan Potiskum da Jos da Kano da Zariya, inda mutane da dama suka rasa rayukansu wadansu kuma suka jikkata, al’amarin da jefa daukacin al’ummar kasar nan cikin halin firgici da […]

A wannan makon tun daga ranar Lahadi zuwa Talatar da ta gabata yankin Arewa ya ga tashin hankali saboda tashe-rashen bama-bamai da aka samu a gururruwan Potiskum da Jos da Kano da Zariya, inda mutane da dama suka rasa rayukansu wadansu kuma suka jikkata, al’amarin da jefa daukacin al’ummar kasar nan cikin halin firgici da juyayi da kuma tsoron abin da zai iya faruwa.
Mutum 25 suka mutu a Zariya
A ranar talatar makon nan da misalin karfe goma na safe wani dan kunar bakin wake ya tada bom da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 20 kuma 35 suka jikkata a wajen aikin tantance ma’aikata da yake gudana a harabar sakatariyar karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna.
Wani wanda ya tsira da ransa amma yake kwance a asibiti (ABUTH) Shika Zariya, mai suna Adamu Hussaini Lere, ya shaida wa Aminiya cewa, “ina kan layin karbar cekin kudina, domin ni an riga an tantance ni tun ranar Asabar, abin da ya rage mini in amshi cekin dina, kuma nine nafarko a kan layi, sai wani yaro ya shigo cikin jama’a amma ban gamsu da motsinsa ba, sai na sanar da dan sanda don ya binciki yaron amma sai shi yaron ya kauce, nan da nan sai yaron ya tayar da bom, ni kawai sai na ji an yi wurgi da ni. Wannan shi ne abin da zan iya tunawa.”
Jim kadan da faruwar lamarin, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i tare da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Umar Usman Shehu suka ziyarci da abin ya faru inda gwamnan ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, tare da jawo hankalin al’umma da su rika kula da yanayin zirga-zirgar jama’a, idan suka ga abin da ba su amince da shi ba su yi kokarin sanar da hukumomin tsaro. Ya kuma sha al’washin daukar matakan da suka dace a duk wurin taron jama’a da sauran wuraren zirga-zirgar jama’a.
Shugaban asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya, Farfesa Muhammed Lawal Khalid ya bayyana wa Aminiya cewa sun karbi gawawwaki guda 25 tare da marasa lafiya guda 35, a inda mutane 2 daga cikinsu suka fi samun mummunan raunuka, amma duk haka suna samun sauki. Ya kara da cewa, suna bukatar gudunmuwar jini a wurin al’umma, musamman matasa. Kuma likitocin asibitin sun janye yajin aikin da suke yi domin taimakawa.
Kwamisinan ‘yan sandan jihar Kaduna Umar Shehu Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wani yaro ne ya tada bom din kuma mutane 21 suka rasu, wadansu kuma suka samu raunuka.
Mutum shida sun mutu a Potiskum
Wani harin bom da dan kunar bakin wake ya kai a cikin wani coci a Unguwar Jigawa cikin garin Potiskum a Jahar Yobe ya yi sanadiyyar hallaka Fasto da ‘ya’yansa 4 da kuma shi kansa dan kunar bakin waken.
Wani mazaunin Unguwar ta Jigawa da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa, dan kunar bakin waken ya tada bom din ne da misalin karfe 9.30 na safe, don a lokacin shi yana gida ne yana shirin zuwa kasuwa, sai kawai ya ji karar fashewar wani abu mai karfin gaske a gab da yankinsu, nan da nan ya firgita ya ruga waje da gudu don sanin me ya faru. Sai ya ji mutane na kururuwa suna cewa ai lalle bom ne ya fashe a Cocin Redeemed da ke kusa da su, don sun ga hayaki da kura sun turnuke wurin, to shine fa suka ruga wurin don kai dauki, da isarsu sai suka ga gawar dan kunar bakin waken a gefe ta yi kaca-kaca, yayin suka tarar da gawar Faston cocin da iyalensa 3 da kuma mace daya daga cikin iyalen nasa a kwance tana numfashi sama-sama, daga bisani ita ma ta cika a asibiti.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ASP Toyin Gbadegesin ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin, tare da karin hasken cewa maharin ya shiga majami’ar Redeemed da ke Unguwar Jigawa cikin garin na Potiskum a matsayin shi ma ya je sujada ne ta mako-mako, tun da ranar lahadi ne, shi ne ya tada bom din da ke jikinsa. A cewarsa, mutum 6 ne suka halaka har da dan kunar bakin waken.
‘Yar kunar bakin wake ta kashe kanta a Kano
A ranar litinin da misalin karfe 9.30 na dare ne wata ‘yar kunar bakin wake ta yi jigida da bam ta nufi wani masallaci da ke kusa da shatalttalen Dangi a Kano da nufin ta tayar da bam din amma Allah bai yarda ba, a karshe dai sai bam din ya tarwatsa ta ita kadai, amma wadansu sun samu raunuka.
Wata majiya ta ce, matar ta nemi shiga masallci ta kofar da maza ke shiga ne amma aka hana ta aka ce ta je ta bi kofar da mata ke bi, a can ne aka nemi a caje ta sai ta ki yarda, daga nan ta koma da baya sai bam diin da ke jikinta ya tashi ita.
Jama’atu ta yi Allah wadai da hare-haren
kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a wuraren ibada a garurruwan Maiduguri da Potiskum da kuma Jos.
Ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Babban Sakatarenta, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu. Ta yi nuni da cewa, abin matukar bakin ciki shi ne yadda harinya ke faruwa cikin wata mai albarka na Ramadan. “Abu ne da ya bai wa Jama’atu mamaki a ce har yanzu abu irin hakan zai iya cigaba da faruwa, musamman idan aka yi la’akari da irin matakan da gwamnatin tarayya ta ce ta dauka a yanzu.
“Aikata irin wannan aiki shaidanci ne domin ba shi da asali a musulunci, kuma masu aikata hakan bata-gari ne kawai, saboda haka dole ne a kama su a bayyana wa jama’a. Sai dai game da harin na Maiduguri akwai ayar tambaya, domin za mu so jin abin da ya hana jami’an tsaro kai dauki a yankin cikin lokaci, duk kuwa da cewa an kira su.
“Muna ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Filato da Zamfara. Wannan lamari abin bakin ciki ne. Don haka muna kira ga musulmi su yi amfani da sauran kwanaki goma na Azumi wajen neman gafarar Allah da taimakonSa domin Ya kawo mana karshen wannan fitina a kasar nan.”
El-Rufa’i ya haramta bara da talla a Kaduna
Gwamnar jahar kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya haramta yin barace-barace da tallace-tallace a kan titituna a wani mataki na inganta tsaro a fadin jahar baki daya.
Gwamnan ya bayar da umurnin hakan ne ‘yan sa’i’o kadan da tada wani bamb a Sabon Garin Zariya.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Kakakin gwamna, Samuel Aruwan, ta yi gargadin cewa idan aka ga duk wani mabaraci ko mai talla za a kama shi. Don haka ya nemi wadanda abin ya shafa da su bi doka har zuwa lokacin da za a sassauta masu ita.
Gwamnan ya kuma yaba wa jama’ar jahar a kan sanya ido da suke yi a kan al’amuran da suka shafi tsaro tare da kuma goyan baya da suke bai wa jami’an tsaro a jihar baki daya.
Har ila yau, gwamnatin ta sake jadda wa jama’a cewa dokar hana yin achaba tananan daram, kuma za a kara zafatata ne.
Daga nan gwamnan ya nemi jama’a da su rika sanar da jami’an tsaro duk wani da ba su yarda da shi ba. Sannan su cigaba da bai wa jami’an tsaro goyan baya domin gudanar da aikinsu.