Makon yaki da ciwon ido na Gilakoma

A yanzu dai za a iya cewa Kannywood ta rabu biyu a dangane da ’yan takarar shugabancin kasa wato Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da kuma Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP. Akwai bangaren jarumi kuma mawaki Sani Danja da kuma na darakta Ishak Sidi Ishak.Al’amarin ya taso ne dalilin wani taro na musamman da […]

Makon yaki da ciwon ido na Gilakoma
Makon yaki da ciwon ido na Gilakoma

A yanzu dai za a iya cewa Kannywood ta rabu biyu a dangane da ’yan takarar shugabancin kasa wato Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da kuma Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP.

Akwai bangaren jarumi kuma mawaki Sani Danja da kuma na darakta Ishak Sidi Ishak.
Al’amarin ya taso ne dalilin wani taro na musamman da matar shugaban kasa Dame Patience ta shirya wa kungiyoyin daban-daban na masana’antar fina-finan Najeriya, don yaba gudunmuwar da suka bayar a kasar nan, inda kungiyoyin da suka halarci bikin cikin har da Kannywood suka yi wa Goodluck Jonathan alkawarin kuri’unsu.
An gabatar da taron ne a Fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Asabar, inda taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a masana’antar fina-finan kasar nan- Kannywood da kuma Nollywood.
kungiyoyin da suka halarci bikin sun hada da Kannywood da kungiyar Mawaka ta Najeriya (PMAN) da kungiyar Jarumai ta Najeriya (AGN) da kungiyar Daraktoci ta Najeriya (DGN) da kuma kungiyar Furodusoshi da Dillalan fina-finai ta Najeriya, inda shugabannin wadannan kungiyoyi suka yi wa Jonathan alkawarin kuri’unsu.
Dalilin da ya sa muke goyon bayan Jonathan- Sani Danja
A lokacin da Sani Musa Danja wanda ya jagoranci ’yan Kannywood yake jawabi a wurin taron ya bayyana cewa suna tare da Jonathan ne saboda irin gudunmuwar da yaba masana’antar fina-finai musamman ma ta Kannywood.
“Wadansu daga cikinmu sun je Indiya yin kwas, an ba wadansu kudi don shirya fim, ana kuma ci gaba da wannan tsarin. Don haka za mu ci gaba da mika godiyarmu ga wannan gwamnati.” Inji Danja.
A cikin ’yan fim din Hausa da suka halarci taron akwai Yakubu Muhammad da Abba Miko da Usman Uzee da Nazifi Asnanic da Yasin Auwal da Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau da Rahama Hassan da Ubale Wanke-wanke da Halima Atete da sauransu.
A yayin taron ne aka bukaci mutane biyu daga Kannywood su yi magana da Hausa, inda aka ba Salisu Mohammed Ofisa da Halima Atete dama, su kuma suka mika godiyarsu ga gwamnatin tarayya bisa tallafin da take ba su.
“Muna gode wa wannan gwamnati saboda goyon baya da take ba mu, ta nuna cewa sana’ar da muke yi sana’a ce mai kyau, sannan akwai abubuwa na karuwa da ta yi wa industiri dinmu a Kano, mun gode. Allah Ya saka da alheri.” Inji Ofisa.
Halima Atete ta mika godiyarta ga wadanda suka shirya bikin.
Sai dai kwana biyu bayan wannan taron sai ga shi ’yan fim sun yi wa Janar Muhammadu Buhari talla a cikin faifan bidiyo.
A cikin wadanda suka gudanar da tallar akwai Ali Nuhu da Adam A Zango da Hamisu Iyantama da Rabi’u Rikadawa da Nafisa Abdullahi da Halima Atete da Baban Chinedu da Daushe da Dauda Kahutu Rarara da Ibrahim Maishinku da Nura Hussain da Ladin Saima da Jamila Nagudu da Falalu dorayi da sauransu.
Ba da yawunmu suka yi hakan ba- Iyantama
Aminiya ta tuntubi daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin tallar takarar Buhari, wato Hamisu Lamido Iyantama inda ya bayyan cewa ba da yawunsu su Sani Danja suka je fadar shugaban kasa ba, sannan sun yanke hukuncin yi wa Buhari kamfen ne saboda kyawawan halayensa da kuma dubi da shi ne suke tsammanin zai kawo kyakkyawan canji a kasar nan.
Ya ce: “Ishak Sidi Ishak ne ya jagoranci ’yan Kannywood zuwa ofishin Jam’iyyar APC da ke Abuja a kwanakin baya, mun kuma yanke hukuncin yi wa Buhari kamfen ne saboda tabarbarewar komai a Najeriya, musamman ma faduwar darajar Naira da faduwar farashin man fetur da cin hanci da rashawa, ga rashin aikin yi, ga matsalar tsaro da sauransu. Bayan mun yi nazari ne muka fahimci idan batun canji ne to Buhari ne zai kasance jagora. Abin da zan sanar da kai shi ne ba yawunmu su Sani suka je fadar shugaban kasa ba.”
Adam Zango ya bayyana wa kafar yada labarai ta Premium Times cewa kwarin gwiwar da suke da shi a kan Buhari zai kawo canji a kasar nan ya sa suke yi masa kamfen, ba kuma kudi aka ba su ba kamar yadda wadansu suke zargi.
Aminiya ta tuntubi Furodusa Abba Miko dalilin zuwansu fadar shugaban kasa.
“Ba wani abu ba ne ya kai mu fadar shugaban kasa face an gayyace mu. A matsayinmu na ’yan kasa sai matar shugaban kasa ta gayyace mu, dole za mu je, idan muka ki zuwa za a ci gaba da barin Kannywood a baya. Idan ba ka manta ba kwanakin baya mutanenmu 19 suka dawo daga Indiya, sannan aka ba wadansu miliyoyin Naira don su shirya fim, idan muka ce za mu noke a ina za mu ci gaba da samun tallafin?” inji shi.
Aminiya ta tambayi daya daga cikin wadanda suka halarci bikin adadin kudin da aka ware wa Kannywood, sai ya ce “Mun je bikin ’yan fim, amma babu wani kudi da aka ware wa Kannywood ko Nollywood, taro ne da matar shugaban kasa ta shirya don yaba wa masana’antar fina-finai a Najeriya, an dai ba mu kudin jirgi da hotel da abinci. Wadansu sun samu Naira dubu 500, wadansu fiye da haka.” Inji majiyar.
Sai dai abin da yake daure kai shi ne, Halima Atete da Nafisa Abdullahi sun yi talla a zabi Buhari, sun kuma je fadar shugaban kasa a lokacin da Sani Danja ya jagorance su.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa