Makonnin lakume rayuka a Arewa Maso Gabas

Makonni biyar da suka gabata sun kasance makonnin lakume rayuka a shiyyar Arewa maso Gabas inda hare-haren da ake jingina su ga kungiyar Boko Haram suka jawo mutuwar daruruwan jama’a da kone garuruwa da dama tare da sanya dubban jama’a yin hijira zuwa wasu garuruwa da kuma kasar Nijar.kungiyar Boko Haram ta kaddamar da miyagun […]

Makonnin lakume rayuka a Arewa Maso Gabas

????????????????????????????????????

Makonni biyar da suka gabata sun kasance makonnin lakume rayuka a shiyyar Arewa maso Gabas inda hare-haren da ake jingina su ga kungiyar Boko Haram suka jawo mutuwar daruruwan jama’a da kone garuruwa da dama tare da sanya dubban jama’a yin hijira zuwa wasu garuruwa da kuma kasar Nijar.
kungiyar Boko Haram ta kaddamar da miyagun hare-harenta ne ta hanyar fara karya kummalo da wani hari da ta kai a wani coci a Jihar Adamawa a ranar 28 ga Janairun  da ya gabata, inda mutum 30 suka halaka
Bishop din Yola, Dami Stephen, ya ce ’yan bindiga sun rufe kofar cocin da ke kauyen Waga Chakawa ana gab da kammala addu’o’i inda suka karkashe mutane.
Kuma a wannan rana cikin dare wayewar washegari, kungiyar Boko Haram ta kai wani hari a kauyen Kawuri da ke karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno, inda bayanai suka nuna cewa, an hallaka mutum 83 a harin, yayin da aka raunata wasu. A lokacin harin an banka wa gidajen kauyen baki daya da masallatai biyar da ke kauyen wuta suka kone kurmus.
Gwamnan jihar, Kashim Shettima ya zayarci kauyen Kawuri da wasu masu rufa masa baya, inda ya duba irin barnar da aka yi kuma ya ba da tallafin kayan abinci ga al’ummar dkauyen da suka saura.
Ana cikin jimamin wannan hari na kauyen Kawuri ne sai maharan suka fada garin Konduga a ranar 11-2-14, inda suka kashe mutum 34 tare da jikkata da dama da kuma kone gidaje masu yawa.
Nan ma Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya ziyarci garin Konduga don yin ta’aziyya ga al’ummarsa inda ya yi alkawarin tallafa musu.
Kuma duk da cewa gwamnatin jihar ta tabbatar da mutuwar mutum 34 a harin ne, wani mazaunin garin ya shaida wa gidan rediyoon BBC cewa an kashe akalla mutum 40 a unguwa daya kadai. Harin ya bar ma’aikata agaji da aikin kwashe wadanda aka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri. Kuma wani jami’in kungiyar Agaji ta Red Cross da ke Konduga, Kwamared Bukar Mai Rembe ya shaida wa BBC cewa ’yan bindigar sun bude wuta ne a bangarori daban-daban na garin ciki har da kasuwanni.
Kwatsam a ranar 15-2-14 sai wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka auka wa garin Izge da ke Jihar Borno inda suka kashe sama da mutum 106.
An yi janaizar fiye da mutum 60 da aka kashe a harin na ranar Asabar da daddare, kuma wadanda suka tsira daga harin sun ce maharan sun tara mutane kamar 30 kana suka bude masu wuta. Daga bisani kuma suka yi ta bi gida-gida suna harbe mutane, yayin da suka yi wa wasu da dama yankan rago. Wannan hari ya tilasta wa kimanin mutum dubu 10 yin hijira daga garin zuwa karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa.
A ranar Laraba 19-2-14 zuwa washegari Talata maharan da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kashe mutum 60 a wani hari da suka kai garin Bama da ke Jihar Borno, bayan kashe mutanen ’yan bindigar nan ma sun banka wa gidaje da sauran gine-ginen wuta.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno, Lawal Tanko ya tabbatar da cewa an kai harin ne a ranar Laraba, kuma jami’an tsaro sun kai dauki daga bisani inda suka kashe ’yan Boko Haram din ta hanyar luguden wuta ta sama.
A ranar Larabar ce kuma Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani faifan bidiyo inda ya ce kungiyarsu ce ta kai hare-haren na Borno da sauransu kuma ita ce ta kashe, Sheikh Muhammad Auwal Albani na Zariya.
Sannan a ranar 27-2-14 ’ya bindiga sun kai hari a garuruwan Michika da Shuwa inda suka kashe mutum 28, kuma wani mazaunin ƙauyen Shuwa ya shaida wa gidan rediyon BBC cewa sun kirga gawar mutum 24, kuma wasu da dama sun jikkata. A garin Michika kuma shaidu sun ce, sun ga gawar mutum uku. Harinya firgita mutane da dama da suka bazama cikin daji domin tsira, inda da suka kwana a cikin daji da kan duwatsu.
Wani harin da ya daga hankalin jama’a ciki har da kasashen waje shi ne wanda aka kai ranar 24-2-14 a wata makaranta a garin Buni Yadi da ke Jihar Yobe, inda aka kashe dalibai 59, sai dai Kakakin Gwamnan Jihar Yobe Abdullahi Bego ya ce dalibai 29 aka kashe.
 An kashe wasu daliban ne ta hanyar yi masu yankan rago, wasu kuma sun kone kurmus bayan da maharan sun cinna wa makarantar wuta. Rahotanni sun ce baki ɗayan makarantar an kone ta.
Kuma jama’ar garin sun ce an kai wannan hari ne ’yan sa’o’i bayan jami’an tsaro da ke kusa da makarantar sun janye. Ana zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan hari.
A ranar Asabar 1 ga Maris an kashe mutum 25 a yankin Askira a wani harin bama-bamai ta sama da dakarun Najeriya suka kai garin Daglun da ke karamar Hukumar Askira Uba, kuma yawancin wadanda suka mutu tsofaffi ne.
Sannan a ranar Asabar da dare zuwa washegari Lahadi 2 ga Maris, mutanen garin Mainok da ke Jihar Borno suka yin jijjifi da harin da ake zargin Boko Haram da kaiwa garinsu. A wannan hari an kashe kimanin mutum 47, sannan an ji wa da dama munanan raunuka tare da kine gidaje da dama. Wani wanda ya tsira daga harin ya ce ’yan bindigar sun shiga kauyen ne sanye da kayan sojoji, suka bude wa jama’a wuta da manyan bindigogi.
Kuma a ranar Lahadin ne aka samu fashewar wasu bama-bamai a unguwar Bintu Suga a Ngomari cikin birnin Maiduguri wadand suka yi sandiyyar mutuwar  fiye da mutum 50.Harin na Maiduguri an kai shi ne a wani gidan kallon wasan kwallon kafa a lokacin yake cike makil da jama’a.
A ranar Litinin 3-3-14 kuma an kashe mutum 35 a garin Mafa da ke Jihar Borno a ci gaba da hare-haren da ake jinginawa ga Boko Haram. Rahotanni daga garin Mafa sun nuna cewa an yi jana’izar mutane fiye da 30 bayan harin da ’yan bindiga suka kai cikin dare, kuma an ce wasu soja sun ɓata.
Alƙaluma na nuna cewa, daga ranar Juma’ar da ta gabata zuwa Lahadi an kashe akalla mutum 117 a sassan Jihar Borno kadai da suka hada da Maiduguri da Daglun da kuma Mainok.
Kuma a ranar Litinin din a wani hari a kauyen Jakana da ke Jihar Borno ya lakume rayukan mutum 11 wadanda suka kone kurmus, a harin da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin.
Sanata Khalifa Zannan daga Jihar Borno wanda yankin Jakana ke cikin mazaba sa, ya shaida wa BBC cewa, tun a ranar Litinin da yamma mazauna garin na Jakana suka ji labarin maharan sun taru a kusa da garin. Kuma hakan ya sa duk wadanda za su iya gudu daga garin suka gudu, aka bar tsofaffi da mata da sauran wadanda ba za a iya gusawa da su ba.
Kuma da maharan suka shiga garin da misalin karfe 8:30 na daren a ranar Litinin din sun kone kusan kashi daya ciki uku na garin, amma sojoji sun kai dauki suka fatattaki maharan.

Tarzoma a Maiduguri
An yi tarzoma a Maiduguri bayan matasan da ake kira ‘Cibilian JTF’ sun yi arangama da soja a wani wuri da ake kira Sector 2, kusa da Kwalejin Koyon Aikin Gona. Matasan ’yan gora da ke binciken ababen hawa ne suka kama wasu mutum biyar dauke da bidigogi a cikin motar haya sanye da fararen kaya. Bayan an je ofishin sojoji sai aka ce, mutanen sojoji ne na gaskiya, nan ne matasan suka fara guna-guni lamari da ya jawo sojojin suka yi harbi kuma suka jikkata mutum uku.
Rayuwa cikin fargaba
Jama’a a kusan duk sassan Jihar Borno na ci gaba da rayuwa cikin zullumi da rashin tabbas, ganin yadda hare-haren Boko Haram suke dada tsananta a jihar duk da dokar ta-baci da aka kafa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.