Maku na kokarin haddasa rikici ne a Nasarawa – Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar a inuwar Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku yana kokarin haddasa wani rikicin kabilanci ne a jihar bayan ta samu zaman lafiya, inda Gwamnan ya zargi Maku da taimakawa wajen rura wutar rikicin kabilanci da jihar ta yi fama da […]

Maku na kokarin haddasa rikici ne a Nasarawa – Al-Makura
Maku na kokarin haddasa rikici ne a Nasarawa – Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce tsohon Ministan Labarai kuma dan takarar Gwamnan Jihar a inuwar Jam’iyyar APGA Mista Labaran Maku yana kokarin haddasa wani rikicin kabilanci ne a jihar bayan ta samu zaman lafiya, inda Gwamnan ya zargi Maku da taimakawa wajen rura wutar rikicin kabilanci da jihar ta yi fama da shi a lokacin da yake Minista maimakon shawo kanta.

A martanin da Gwamna Al-Makura ya mayar kan zargin da Labaran Maku ya yi a hira da ’yan jarida a mako jiya na cewa Gwamnan ne yake hadasa rigirgimu a jihar tare da zargin Gwamnan da hayar ’yan ta’adda suna shigowa jihar inda suke kashe mutane ba gaira ba dalili. Kuma ya zargi Gwamnan da kasa shawo kan rashin tsaro a jihar da sauransu, Gwamnan ya ce wadannan kalamai soki burutsu ne irin na siyasa kawai.
Gwamna Al-Makura ta bakin Daraktan Labaransa, Alhaji Ahmed Tukur ya ce abin kunya ne a ce Labaran Maku da a cewarsa sau da yawa a lokacin da jihar ke fuskantar wadannan rigirgimu shugabannin al’ummomin jihar da kuma gwamnati sukan gayyace shi ya zo don a samar da hanyoyin zaman lafiya a amma yana kin amsa gayyatar, amma yau an waye gari yana zargin Gwamna Al-Makura ba gaira ba dalili, bayan gwamnatinsa ta shawo kan rashin tsaro a jihar da dadewa.
Gwamnan ya ce batun ta’addanci da rikicin kabilanci da jihar ta fuskanta a baya sun yi tsanani ne sakamakon karuwar makamai da a cewarsa Maku ya rika raba wa wasu a jihar don su rika kashe mutane a lokacin da yake rike da mukamin Ministan tsaro. Ya ce ya kamata Maku ya yaba wa Gwamna Al-Makura dangane da namijin kokari da ya yi don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a jihar baki daya.
Ya ce “Kowa ya san cewa jihar nan ba ta taba samu mummunan wakilci a Majalisar Zartarwa ta kasa ba, sai a lokacin Maku. Maimakon ya wakilci jihar yadda ya kamata, sai ya yi ta lalata sunanta da ma sauran jihohin Arewa, a wurin tsohon mai gidansa Goodluck Jonathan ba gaira ba dalili.”
Gwamna Al-Makura ya kuma zargi tsohon ministan cewa ya hana yawancin ayyukan ci gaba da ya kamata jihar da sauran jihohin Arewa su amfana da su a lokacinsa saboda hadama da son kai. Daga nan sai ya shawarci Labaran Maku ya dawo gida ya su hada hannu don kai jihar tudun mun tsira maimakon ya ci gaba da zama a Abuja yana furta kalaman da ka iya haddasa rigima a jihar.
Idan za a iya tunawa jim kadan bayan Labaran Maku ya gabatar da shaidunsa ne a kotun da ke sauraren kararrakin zaben Gwamnan Jihar da ke Lafiya kan shari’arsa da Gwamna Al-Makura ne ya gana da manema labarai inda ya zargi Gwamnan cewa shi yake haddasa rigirgimun jihar da ta’addanci da sauransu.