Maku ya taimaka wajen faduwar PDP a zaben Gwamnan Nasarawa – Yunanah Iliya

Mista Yunanah Iliya shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa, a zantawarsa da wakilinmu a Lafiya, ya ce ficewar Labaran Maku daga PDP da kuma siyasar addini na cikin abubuwan da suka sa jam’iyyar ta sha kaye a zabubbukan da suka gabata: Aminiya: Me za ka ce kan zabubbukan da aka yi, kuma me […]

Maku ya taimaka wajen faduwar PDP a zaben Gwamnan Nasarawa – Yunanah Iliya
Maku ya taimaka wajen faduwar PDP a zaben Gwamnan Nasarawa – Yunanah Iliya

Mista Yunanah Iliya shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa, a zantawarsa da wakilinmu a Lafiya, ya ce ficewar Labaran Maku daga PDP da kuma siyasar addini na cikin abubuwan da suka sa jam’iyyar ta sha kaye a zabubbukan da suka gabata:

Aminiya: Me za ka ce kan zabubbukan da aka yi, kuma me kake ganin ya jawo muku faduwa?
Yunanah: Kodayake zabe ya zo ya wuce, ba shakka ya bar baya da kura da ka iya zamewa cikas ga ci gaban kasar nan. Na bayyana haka ne domin a duk zabe dole ne a samu wanda ya yi nasara da wanda ya fadi. A nan Jihar Nasarawa kamar yadda aka sani jam’iyyarmu PDP ta yi iya kokarinta don tabbatar da ta lashe zabubbukan. Amma abin takaici shi ne yadda Hukumar Zabe ta kasa wato INEC ta nuna karara cewa tana goyon bayan Jam’iyyar APC a lokacin zabubbukan. Ba zan iya cewa haka lamarin yake a kasa baki daya ba, na san wanda ya shafe ni ne a jihar nan kawai. Misali an gudanar da zaben Shugaban kasa tare da na sanatoci da ’yan Majalisar Tarayya a ranar 28 ga watan Maris. Mun lashe wadannan zabubbuka a nan jihar. A mazabun Majalisar Dattawa guda 3 mun lashe duka na ’yan Majalisar Tarayya, ma mun lashe zabubbukan duka, amma a lokacin bayyana sakamako, sai hukumar zabe ta umurci wadanda ke bayyana sakamakon cewa kada su bayyana sunayen wasu ’yan PDP a wasu wurare da muka yi nasara. Bayan zaben kuma hukumar zaben ta bayyana wasu dalilai marasa tushi wadanda a cewarta hakan ya hana a gudanar da zabe a wasu kananan hukumomi a wasu mazabu da dama inda daga bisani ta bayyana ’yan takarar Jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka lashe zabubbukan wuraren. Sun yi haka ne da nufin cewa koma mene ne dai za a hadu a kotu. Hukumar zaben tana murdiyar tana bayyana cewa duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba ya kai kara a kotu. Amma abin mamaki da takaici shi ne wadanda suka aikata laifin bayyana sunayen wadanda ba su yi nasara ba a matsayin wadanda suka yi nasara babu hukuncin da aka yi musu har yanzu da muke magana. Haka aka yi a lokacin zaben ’yan Majalisar Tarayya, misali a mazabar tarayya ta Nasarawa da Toto, ba a gudanar da zabe a wata mazaba ba, amma hukumar zaben ta bayyana cewa APC ta samu kuri’a dubu tara. Akwa adalci a nan? To a ma bari cewa an gudanar da zabe a wurin, dokar zabe ta bayyana cewa a duk inda aka gano cewa yawan kuri’ar da aka samu ya fi yawan wadanda aka tantance ya kamata a bayyana wannan zabe a matsayin wanda ba a kammala ba, hukumar zabe ba ta yi haka ba. Haka a mazabar tarayya ta Obi da Lafiya inda muka lashe zaben, abin mamaki mai bayyana sakamakon zabe ya bayyana cewa ba a kammala zaben ba don a cewarsa an samu wasu kura-kurai a daya daga cikin mazabun wato mazabar Ciroma. A cewar INEC jami’in da ke wajen ya kara yawan kuri’a da guda dubu 17, kuma an kama shi. Idan gaskiya ne maimakon a tsare shi a hukunta shi hukumar zabe ba ta yi haka ba, ta bayyana cewa ba a kammala zaben ba, wannan sata ce a fili, wannan ba zabe na gaskiya ba ne.
A zaben Gwamna kuma saboda abin da ya faru a zaben farko a lokacin da zababben Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar nan da tawagarsa inda ya gana da sarakunan gargajiya inda ya gaya musu dalilan da a cewarsa suka sa ya zame musu dole su zabi APC. Ya gaya musu cewa idan suka zabi PDP jam’iyyar za ta zama ta adawa ne kawai a kasa don ya riga ya ci zabe. Saboda haka sai mutane suka ji maganarsa suka zabi APC.
Na uku kamar yadda ka sani akwai batun Jam’iyyar APGA. Akwai wasu da suka lura cewa wasu ’yan PDP sun kada wa Buhari kuri’a saboda addini. Saboda haka ne ma wasu ’yan PDP Kiristoci suka yanke shawarar kada wa APGA kuri’arsu a zaben Gwamna saboda dan takaranta Labaran Maku Kirista ne. Wadannan abubuwa ne da wasu da dama suka shafi PDP a jihar nan wanda hakan ya sa hakarmu a wannan karo ta kasa cimma ruwa kamar yadda muka yi a lokacin zaben Shugaban kasa.
Aminiya: Wasu na zargi cewa dan takararku na Gwamna wato Alhaji Yusuf Agabi ya zabi Buhari maimakon Jonathan, me za ka ce kan haka?
Yunanah: Babu shakka na ji wasu ’yan jam’iyyarmu suna wannan zargi. Amma abin tambaya wadannan mutane suna da hujjojin zargin? Mu dai mun san inda wannan zargi yake fitowa, yana fitowa ne daga wurin wasu mutane da suka so su fake da addini su kawo mana rudani kuma sun samu nasarar yin haka wajen rudin wadanda ba su san mece ce siyasa ba, suka sa suka yarda cewa dan takarar Gwamna na PDP ya zabi Buhari maimakon Jonathan wanda hakan ko kadan ba gaskiya ba ne. Kuma a shirye nake in kare shi a koyaushe dangane da wannan zargi, domin mun zaga cikin jihar nan baki daya tare muna kamfen kuma na san taimakon da Jonathan ya ba shi a wancan lokuta. Don me zai ci amanansa, ya kada wa Buhari kuri’a?
Aminiya: Ko canja sheka da Labaran Maku ya yi daga PDP zuwa APGA ya taimaka wajen faduwarku?
Yunanah: Ba shakka canja sheka da ya yi ya jawo mana gagurumar faduwa a lokacin zabubbukan. Babbar matsalar ma ke nan don ya kwashe jama’a da dama da ya kamata su kada wa PDP kuri’a zuwa APGA. Kamar yadda na bayyana a baya akwai Kiristoci da dama ’yan PDP da suka zabi APGA don Labaran Maku Kirista ne, wanda hakan ya kawo cikas ga jam’iyyarmu a wannan lokaci sosai. Saboda haka kodayake ba na so in ce komai game da Labaran Maku, a takaice dai canja shekarsa ba shakka ya jawo mana gagarumar faduwa. Haka shi ma kansa hakan ya jawo masa faduwa don shi ma ai ya fadi.
Aminiya: A karshe wane mataki za ku dauka game da sakamakon zabubbuka da ka bayyana marasa adalci?
Yunanah: A halin yanzu dai mun hakura da sakamakon zaben Gwamna da na Shugaban kasa a jihar nan. Amma na ’yan majalisar dokoki da na tarayya da na sanatoci da sauransu da aka yi mana magudi tuni mun kai kara kotu mun dauki lauyoyi ana nan ana shari’a a halin yanzu.