Makubar Maman Tarba-tarba (1)
Maman tarba-tarba Makamar masu karba-karba Mama tai kasassba A wajen kurbar romon jaba Ta fifita wani sabanin Baba Kai ku mulmulo mata teba Ta ci ta kara teba Ga miya nan ki ta sharba A siyasar Baba An tabbatar mini babu gaba Mama ta sake uba Tai makwalwar kurba-kurba Ta shafa dangwali yaba […]
Maman tarba-tarba
Makamar masu karba-karba
Mama tai kasassba
A wajen kurbar romon jaba
Ta fifita wani sabanin Baba
Kai ku mulmulo mata teba
Ta ci ta kara teba
Ga miya nan ki ta sharba
A siyasar Baba
An tabbatar mini babu gaba
Mama ta sake uba
Tai makwalwar kurba-kurba
Ta shafa dangwali yaba
Zabi-sonka an son kwaba
Mun san uba a gida shi ne babba
Mama ta lailaye da makuba
Tana juyin sauka bisa turba
Siyasarta ta karkace mazahaba
Gwamna ta so yi a Tarba-tarba
Uwargada ta iya zuba
Jiki magayi shan tabar dan Korau
Ai ta kada banbaro
Da taka rawar dan bararo
Babu shanu an afka sharo
Kutu-kutun karajin kerau
Maman makwalshe
Ta cumuimiye bandashe
Tande-tande da lashe-lashe
Ta jajujubo mana kwashe-kwashe
Ki tallata manufa a kowane sashe
Ta yi uwa da makarbiya
Cikin jam’iyya
Mai mulkin Haurobiya
Ga wata nai muku jayayya
A sauke mata nauyin kaya
‘Yar Lasan
Kin yi kidan gangan
Gangan-gangan
kalan-kalan
Dambarwarki zanzan-zanzan
’Yar adawa
Na tallar daddawa
Tantagaryar kalwa
Ta shiga kasuwa
Za ta sake kasawa
Shahon sansani
Ya gargadi masu gani-gani
Uwargada aikinki yai tsanani
Uban siyarta ne tsani
Baba to ka gani
Kasuwar bukata
Babu sabani ga wanda ya tsinta
kuliyar kwararo ba ta kulle
sai a sake lale
mun fasko ku mabarnata
Taka na zumbude
Taka na zumbude
Raye-raye da kade-kade
Rawar gada wata ta baude
Tsallaka titin babur ya kade
Gwamna el-Rusau
Ya furta a yaren Hau-hau
’Yar lasan kar ai mata nadau
Ta fara tauna marau-marau
Gyadar gadar gyadau
Damo-da-kura-da-diyya
Dama-damar kurdar tsiya
Gulbi ya tsiyaya
A share miyagu da tsintsiya
Kar ai tsiya-tsiya
A kalkale-a kalkale
Mama tai kyale-kyale
An barta tana ta jele
Mama ta ci alale
Inna kinyi male-male
Dubu karamin laujen sili nunin kasa
Kina so Baba ya ba ku kasa
Kun nemi amincewar sassa
Me ya kawo sa-in-sa
A fasa kowa ya rasa
Mama mai kankamba
Batunki ba ya kan gaba
Kodayake nasan kin caba
Shirinki kakaba mana ja-gaba
Wai ubangidanta ne shagaba
Haurobiyawa ban da wargi
A daina magagi
Ragamar Baba tai kugi
Mun fara fita kangi
Matsaloli an sa musu waigi
Maganin masu kwashi-kwaraf
Da suka yi wa lalita karkaf
Sunkurun saraf-na-sadaf
Kuntungwila daf-da-daf
A karkabe su kakaf
Sana’ar na-duke
Talakawa a mike
Mu daina lakakin duke-duke
Ko makircin sake-sake
Baragurbi sun noke
An ingiza uwargada
Dabarbaru ta ganganda
Manufar mamaya ta yada
Mai kantu a ruwa ya fada
Ku ciro mana ita ta dan zakuda
Ko kin iya makarde
Ki daina yi wa Baba murgude
Ki zauna gida ki yi tankade
Ko kin fi so a ce ranki ya dade
A halin yanzui kin baude
Zankade-zankaden Zankadaziyya
Zilliyar Zillaziyya
Zanzaron zawaran zirya
Zabarin zaburar zugar zangarniya
Zaman zauracen kece rainin tsiya
Mu yi wa Mama rangwame
Kar a kwada mata gungume
Ta taka kasa ta zame
Ta koma kame- kame
Ta kinkime
Tsintsiya madaurinki guda
Sharar tsaye ban da gargada
kiyayi gada-gadar gudun gada
Kife mai sandon sungumar gwanda
Ta tafi daji ta tsunko tsada
Baba ko za ka ba ta na tsuntsun miya
Da damin gero ta dama kunun tsamiya
Ka dai hanata kamuya-muya
Shi ya sa take hargowa da taratsin karya
Shigar sunkuru da sarkakiya
***