Makunnin Nukiliya na kan teburina – Shugaban Koriya ta Arewa

…Nawa ya fi naka girma – Shugaba Trump Shugaban Koriya ta Arewa ya ce shi fa yana da makunnin nukiliya a kan teburinsa kuma zai bayar da umarnin amfani da makaman ne in har kasarsa ta fuskanci barazana kamar yadda kafar labarai ta BC ta ruwaito. A sakonsa na sabuwar shekara da aka watsa ta […]

Makunnin Nukiliya na kan teburina – Shugaban Koriya ta Arewa

…Nawa ya fi naka girma – Shugaba Trump

Shugaban Koriya ta Arewa ya ce shi fa yana da makunnin nukiliya a kan teburinsa kuma zai bayar da umarnin amfani da makaman ne in har kasarsa ta fuskanci barazana kamar yadda kafar labarai ta BC ta ruwaito.

A sakonsa na sabuwar shekara da aka watsa ta gidajen talabijin, Shugaba Kim Jong-un ya zolayi Amurka da kawayenta inda ya ce ba abu ne mai wahala ya yi raga-raga da daukacin Amurka ba.

Sai dai ya ce kasarsa a shirye take ta tattauna da Koriya ta Kudu har ma ta tura tawagar ’yan wasa zuwa gasar Olympics a birnin kasar .

A kwanakin baya Majalisar dinkin Duniya ta kakaba wa Koriya ta Arewa takunkumi mai tsauri.

Takunkumin zai kayyade wa Koriya ta Arewa ikon shigo da man fetur zuwa ganga dubu 500 a shekara daya. Wanda hakan zai dakile wata muhimmiyar kafa ta samun kudaden ga kasar.

Sai dai Shugaba Donald Trump sai ya mayar da martani inda ya ce makunnin nukiliyarsa ya fi girma da karfi fiye da na Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un.