Makwabci ya lalata ’yar shekara 9 a gonar mahaifinta a Kaduna
Makwabcinsu mai ‘ya’ya biyu ya yi mata wannan aika-aika ne a yayin da ita da kannenta suke korar awaki daga gonar mahaifinsu
Wani magidanci ya yi wa wata karamar yarinya mai shekaru tara fyade a gonar mahaifinta.
An zargin makwabcin nasu mai ‘ya’ya biyu ya yi wa yarinyar wannan aika-aika ne a yayin da ita da kannenta suke korar awaki daga gonar mahaifinsu.
Wannan al’amari ya faru ne a kauyen Akilibu, kan babbar hanyar zuwa Abuja, a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Mahaifin yarinyar ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho ranar Laraba cewa makwabcin na su ya karya hannun yarinyar guda daya, baya ga raunin da ta samu a ganata a sakamakon fyaden.
- Uba ya sayar da ’ya’yansa biyar a Sakkwato
- Saurayi da budurwarsa sun sace kayan lefen ’yar uwarsa a Kano
- NAJERIYA A YAU: Mafi Karancin Albashi: Shin Me Ma’aikata Ke Fatan Samu?
Yanzu haka a cewarsa tana asibiti inda take samun kulawa.
Ya ce tsautsayi ya auka mata ne bayan makwabcin nasu ya dauke ta sa karfin tuwo ya yi awon gaba da ita a lokacin da ita da kannenta suke taya shi korar waki masu ci masa amfanin gona.
Mahaifin ya ce yawancin awakin garin a daure suke, amma akwai masu yawo suna barna a gonaki.
Sakamakon haka, “Mai unguwar ya ba ni cewa in rika tsaron gonata da rana, shi ne na sa ’ya’yana mata su kula da gonar a ranar Asabar.
“Amma abin takaici wani makwabcinmu mai ’ya’ya biyu ya far wa daya daga cikinsu ya lalata ta
“A garin haka ya karya mata hannu daya, bayan raunin da ya yi mata a al’aura, yanzu tana asibiti ana jibyar ta.”
Ya kara da cewa washegari ’yan sanda suka wanda ake zargin kuma yana tsare a hannunsu.
Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Kwamred Nura Muktar, wanda ya fara tsegunta mana labarin, ya sha alwashi ganin bin lamarin a gaban kuliya har zuwa karshe.