Makwancin Nana Khadija matar Manzon Allah (SAW)

Bayan rasuwarta, an binne ta ne a Makabartar Mu’alla da ke Makkah inda a nan aka binne babban dansu, Alkasim.

Makwancin Nana Khadija matar Manzon Allah (SAW)

Makwancin Nana Khadija (RA). Hoto: Haramain Sharifain

Uwar Muminai, Nana Khadija bintu Khuwailid (RA), ita ce matar Manzaon Allah Annabi Muhammad (SAW) ta farko.

Bayan rasuwarta, an binne ta ne a Makabartar Mu’alla da ke Makkah inda a nan aka binne babban dansu, wato Alkasim.

Tarihi ya nuna Nana Khadija (RA) ta rasu ne a ranar 10 ga watan Ramadan kafin hijirar Annabi (SAW) zuwa Madina, wanda hakan ya yi daidai da shekara ta 620 Miladiyya.

Bakuraishiya ce daga Makka, akan kira ta da Khadijatul Kubra, sannan ana yi mata lakabi da Ummul-Muminin, Amiratu-Kuraish da kuma Al-Tahirah.

Kafin rasuwarta, sun samu ‘ya’ya shida tare da Annabi (SAW) — maza 2 mata 4: Al-Kasim, Abdullah, Zainab, Rukayya, Umm Kulthum da kuma Fatima.