Malala ta malala wa ’yan mata kudi don ilimi

’Yar kasar Pakistan din nan mai rajin kare hakkin mata ta fuskar ilimi, Malala Yousafzai ta malala wa ’yan matan Chibok kudi inda ta ba da gudunmawar Dalar Amurka dubu 200 (kimanin Naira miliyan uku da dubu 300) domin tallafa wa ilimin ’ya’ya mata a Najeriya.Malala ta sanar da bayar da gudunmawar ce a wajen […]

Malala ta malala wa ’yan mata kudi don ilimi
Malala ta malala wa ’yan mata kudi don ilimi

’Yar kasar Pakistan din nan mai rajin kare hakkin mata ta fuskar ilimi, Malala Yousafzai ta malala wa ’yan matan Chibok kudi inda ta ba da gudunmawar Dalar Amurka dubu 200 (kimanin Naira miliyan uku da dubu 300) domin tallafa wa ilimin ’ya’ya mata a Najeriya.
Malala ta sanar da bayar da gudunmawar ce a wajen wata lacca da ta gabatar a Abuja albarkacin bikin Ranar Malala. Tun a karshen makon jiya ne Malala ta shigo Najeriya domin tattaunawa da gwamnati kan yadda za a ceto ’yan matan da aka sace a Chibok fiye da wata uku da suka gabata.
’Yar Pakistan din ta gana da Shugaba Goodluck Jonathan da wasu daga cikin iyayen ’yan matan da kuma kungiyar #Bringbackourgirls wacce ke fafutikar matsa wa gwamnati don ganin an kubutar da ’yan matan.
Malala Yousafzai ta tsira da ranta ne a hannun ’yan Taliban bayan da suka harbe ta a kai saboda fafutikar da take yi don ganin mata sun samu ilimi a Pakistan.
Ta ce Shugaba Jonathan ya ba ta tabbacin zai gana da iyayen ’yan matan da aka sace, kuma ta ce ta zo Najeriya ne a daidan lokacin da take cika shekara 17 a duniya don ganin kowane yaro ya samu ilimi, kuma manufarta a bana ita ce ta yi magana a madadin “kananan ’yan matan Najeriya” kimanin 200 da Boko Haram suka sace.
A yayin ganawarta da ’ya’yan kungiyar #BringBackOurGirls a Abuja, Malala ta yi kira ga kungiyar Boko Haram ta guji tayar da hankali da sunan Musulunci, inda ta ce Musulunci addini ne na zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A taron Ranar Malala kuwa cewa ta yi ga Boko Haram,  “…Ku ajie makamanku, ku sako ’yan uwana ’yan mata ku sako ’yan matan kasar nan. Ku ’yantar da su ba su aikata wani laifi ba.”
A wani labarin kuma wasu daga cikin iyayen ’yan matan Chibok da aka sace, gwasale Shugaba Jonathan inda suka ce ba za su gana da shi kamar yadda aka shirya ba.
A ranar Litinin ce Fadar Shugaban kasar ta fitar da sanarwar cewa, Shugaba Jonathan zai gana da iyaye 12 da ’yan mata biyar da suka kubuta daga hannun ’yan Boko Haram a ranar Talatar da ta gabata.
Gayyatar ta zo ne bayan Malala ta gana da Shugaba Jonathan, inda ta nemi ya gana da iyayen ’yan matan.
Bayanai sun nuna cewa iyayen ’yan sun ce yawansu bai kai yadda za su wakilci dukkan iyayen ’yan mata fiye da 200 da aka sace ba.
Sai dai a wata sanarwar da fadar Shugaban kasar ta fitar, gwamnati ta ce masu fafutikar ceto ’yan matan Chibok na #Bringbackour girls ne suka sanya siyasa cikin lamarin. “Hakan abin kunya ne a gare su,” inji sanarwar da gwamnatin ta fitar inda ta nanata niyyarta ta ceto ’yan matan na Chibok.
Shugaba Jonathan ya bayar da umarnin a aika da wasiku ga iyayen ’yan matan domin halartar ganawa da shi a makon gobe kamar yadda mashawarcinsa kan harkokin watsa labarai Doyin Okupe ya shaida wa manema labarai a ranar Talata.