Majalisa ta jaddada aniyar dakatar da daukar ma’aikata 774,000

Shugaban Majalisar Datattawa Ahmad Lawan ya jadadda kudirin majalisar na dakatar da daukar ma’aikata 774,000. Gwamnatin tarayya ce dai ta bayyana shirin daukar ma’aikata 1,000 daga ko wacce daga cikin kananan hukumomi 774 na Najeriya. Yayin wata zantawa da manema labarai ranar Litinin, Sanata Ahmad Lawan ya ce dole ne Hukumar Samar da Ayyuka ta […]

Majalisa ta jaddada aniyar dakatar da daukar ma’aikata 774,000

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan

Shugaban Majalisar Datattawa Ahmad Lawan ya jadadda kudirin majalisar na dakatar da daukar ma’aikata 774,000.

Gwamnatin tarayya ce dai ta bayyana shirin daukar ma’aikata 1,000 daga ko wacce daga cikin kananan hukumomi 774 na Najeriya.

Yayin wata zantawa da manema labarai ranar Litinin, Sanata Ahmad Lawan ya ce dole ne Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE), tare da Ma’aikatar Kwadago su yi wa majalisar gamsasshen bayani kafin a ci gaba da shirin.

“Mun yarda an fitar da Naira biliyan 52, don haka sai an yi mana bayanin yadda aka zabo ’yan kwamitin da za su jagoranci lamarin, da yadda za a zabo wadanda za su amfana da shirin, da kuma yadda shirin zai yi nasara”, Inji shi.

Ya kuma ce majalisar tana kan bakanta na dakatar da shirin har sai jami’an gwamnatin sun yi mata bayanin yadda za su aiwatar da shirin a fadin kasar nan.

A karkashin shirin dai za a  biya ma’aikatan N20,00 a wata ko wannensu kuma za a fara ne daga ranar 1 ga watan Oktoba.

A ranar Talatar makon jiya ne Minista a Ma’aikatar Kwadago Festus Keyamo ya yi musayar kalamai da mambobin kwamitin ayyuka na Majalisar Dokoki ta Kasa a kan mutum 20 da aka zaba su kula da daukar ma’aikatan.

Majalisar Dattawan ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin har zuwa lokacin da kwamitin zai yi mata gamsasshen bayani.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos