Malam Aminu Kano ne ya share mani hanyar zama mawaki – Hassan Nakutama

Malam Hassan Nakutama fasihin mawaki ne, wanda ya dade ana fafatawa da shi a fagen rubutattun wakoki tun zamanin siyasar NEPU da NPC, wanda saboda kwazonsa a fagen iya tsara wakoki sai da marigayi Malam Aminu Kano ya kama hannunsa ya daga sama a wajen wani gangamin siyasa a birnin Kano. A cikin wannan tattaunawa […]

Malam Aminu Kano ne ya share mani hanyar zama mawaki – Hassan Nakutama
Malam Aminu Kano ne ya share mani hanyar zama mawaki – Hassan Nakutama

Malam Hassan Nakutama fasihin mawaki ne, wanda ya dade ana fafatawa da shi a fagen rubutattun wakoki tun zamanin siyasar NEPU da NPC, wanda saboda kwazonsa a fagen iya tsara wakoki sai da marigayi Malam Aminu Kano ya kama hannunsa ya daga sama a wajen wani gangamin siyasa a birnin Kano. A cikin wannan tattaunawa da Aminiya ta yi da shi a gidansa da ke cikin garin Kafanchan, ya bayyana tarihinsa da irin gwagwarmayar da ya sha a fagen wakokin Hausa, inda ta kai ga har bindiga aka taba cirowa domin a harbe shi. Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Ahmed Ali, a Kafanchan

Ko za ka bayyana tarihinka a takaice?
Ni dai tarihina ba mai yawa ba ne, sunana Hassan Na-Kutama. An haife ni ne a garin Kafanchan a wajajen shekarar 1937.
Ko za ka iya tuna wane lokaci ka fara rubuta wakoki?
Na fara rubuta waka ne, ina jin tun a shekarar 1949.
Ko za ka fada mana abin da ya ja ra’ayinka ka fara rubuta wakoki?
Bayan na shekara tara da haihuwa sai mahaifina ya ga ya kamata ya dauke ni ya koma da ni mahaifarsa, wato Kutama (karamar Hukumar Gwarzo, Jihar Kano). Da ma dan uwan mahaifin nawa yakan zo Kafanchan. To bayan na warke daga Shayi (kaciya) lokacin ina da shekara tara, sai ya hada ni da shi, ya ce ya tafi da ni gida. To bayan zuwana gida Kutama, nan na ci gaba da zama har zuwa girmana, sai dai zuwa ci-rani da nake yi cikin birnin Kano in dawo. A cikin gari na zauna ne a dandago. To Allah cikin ikonSa a lokacin ana siyasar NEPU da NPC, to jin sautin mawaka irin su Mudi Sipikin da na marigayi Sa’adu Zungur da suke yi wa NEPU sai abin yai mini tasiri na ji cewa tun da ni ma ina cikin wannan jam’iyya, to ya kamata ni ma na kwaiwaye su wajen yin wake. Ni ban yi karatun boko ba sai dai na yi yaki da jahilci a Kutama, wajen wani malami da ake kira Malam Muhammadu Daneji; wanda aka turo shi daga birni, wanda ta kai alhamdu lillahi, har tashi na ake yi ina koyawa sauran dalibai abin da aka koya mana, wacce da ita na samu kwarewar da har nake iya rubutun Hausa.
Ko za ka iya tuna wakar da ka fara rubutawa?
Gaskiya lokacin da tsawo, ba zan iya tuna wakar da na fara rubutawa ba, sai dai zan iya cewa a lokacin wakokin NEPU ne. Ta kasance wata rana na je gidan Malam (Aminu Kano) a Gwammaja, na kai masa takardun wakokin da nake rubutawa na NEPU. Da ya karba ya duba sai ya kalle ni ya ce: Kai! Kana ina ne? Sai na ce masa ina nan ne a dandago. Sai ya ce kai haifaffen dandago ne? Sai na ce masa a’a, ni haifaffen Kafanchan ne amma ina zaune ne a Kutama. Sai ya ce da ni ka bar wadannan wakokin, yanzu in an ce in rera su nan take a wajen taro zan iya rerawa, ba tare da ina dubawa ba? Na ce masa zan iya, saboda maganar gaskiya duk wakokina ina daukar alkalami ne in rubuta, amma fa in na tashi rerawa to ba na bukatar dubawa. Daga nan ya sallame ni na tafi. To bayan kwana kadan sai Malam Aminu Kano ya aiko har gidan da nake a dandago, da ma na gaya masa. Da na je sai ya ce mini, to ka ga da ma za mu tafi Dawanau kuma da kai za mu tafi, za ka bi mu? Na ce masa e, zan bi ku. To da mu ka je Dawanau a kofar gidan da za a yi lacca, a ka dauko turmi, wanda a kansa ake tsayawa a da, kafin a koma kan tano, wato durom. A nan ne Malam Aminu ya daga hannuna ya ce kada ku raina wannan yaron da kuke gani, su ne za su yi kira a wannan hanya ta gaskiya da muke a kai, na kubutar da kanmu daga zalunci.
Bayan an gama gabatar da manyan mutane da baki, kafin a saurari jawabi, waka ake fara yi. Daga nan kawai sai aka gabatar da ni na fara waka, kuma Allah Ya taimake ni na yi iya gwargwadon waken da ya samu. A wurin na samu kyautar kudi har sule takwas da ahu. Wallahi a wancan lokacin na rasa yadda zan yi da su. A lokacin ma da na gan su jikina rawa ya fara yi. To, e mana, mutumin da iyakacinsa rike kwabo zuwa kwabo biyu ko taro, in mun yi nisa mu rike sisi, sai ga shi na ga irin wannan kudin! To, ganin haka kawai sai na kwashi wannan kudi na kai wa shi Malam Aminu Kano. Na ce to ga abin da na samu. Da ya karba sai ya debi wasu a ciki kudin ya ba ni. Kar ka dauka sauran fa ya rike ne, ka san abin da ya yi da su? Zuwa ya yi kawai ya sayo min turmin alawayyo, ya zo aka dinka min shakwara da jamfa da wando; ya ce to ka ga wannan ragowar kudinka ke nan da suka rage a wajena amma an debi wani abu kadan an zuba a asusun jam’iyya (dariya). Ka ga mutuwar Sardauna ma wallahi a bakin Malam na ji, ya zo ya tara mu ya ce mana to daga yau an kashe siyasa, an kashe Sardauna.
To bayan wucewar siyasar NEPU da NPC da kuma wucewar mulkin soja, aka sake da sa wata siyasar. Duk da dai a nan ba mu yi wani tasiri ba amma na kasance a jam’iyyar NRC ce, ina ma daga cikin tawagar ’yan kamfen din Dabo Lere.
Ko akwai wasu wakoki da kake yi bayan na siyasa?
Da ma farkon wakar da na yi, ta yabon Annabi ce. Bayan tafiya ta yi nisa kuma sai na ga ya kamata na waiwayi wasu abubuwa na fadakarwa, na dauko na yi waka a kai. Na yi wakar fadakarwa a kan matan aure, na yi a kan ilimin zamani da sauransu dai da dama, a yanzu haka ma ga ni da littattafan.
Mun ji an ce ka yi wakar ta’aziyyar kashe tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Muhammad, wanda aka ce wakar ta shahara, ko za ka yi mana karin bayani a kai?
Haka ne, domin a lokacin da na ga masu ganguna suna ta yi masa waka, sai na ce to mu ma me zai hana mu yi wa wannan bawan Allah ta’aziyya? Shi ne na dauko takarda da alkalami na yi waka a kan ta’aziyyarsa, wanda a sanadiyyar wakar har kyautar suturu wani ya aiko min da su daga Saudiyya.
Ko za ka iya fada mana ina da ina ka je a fadin Tarayyar Najeriya a sanadiyyar waka kuma ina da ina ka je a kasashen waje?
Sai dai in ce kawai muryata ta je amma ni ban yi nisan tafiya ba. A cikin gida Najeriya dai na san na je Kano, Kaduna, Legas da kuma Bauchi. Dalilin zuwa na Bauchi kuwa, mun tafi ne da Tunji Braithweight, Shugaban jam’iyyar NAP. Duk wata waka da zan yi, in dai ba ta yabon Annabi ba ce, to a bayan wakar da na yi wa NAP ce.
Ko za ka iya rera mana ita yanzu?
Ga baiti daya ka ji yadda na wasa jam’iyyar; Amshin wakar ita ce:
“Najeriya Adbance Party, Rahamar Allahu Abin Kauna.
Matar kwarai mai albarka,
Kuma ba ta auren dan iska,
Mai zage-zage ko duka,
Wannan diya kam sam barka,”
Najeriya Adbance Party.
To irin wadannan wakoki da ka yi ta zubawa haka, wani ya taba daukar nauyin wallafa su zuwa littafi?
Gaskiya akwai wanda ya so ya dauki nauyin duk gaba dayan littattafan wakokin da na rubuta. Bayan na kai masa ya dudduba sai ya ce: Malam Hassan, na ce ranka shi dade. Ya ce wannan littafi ba za mu bar shi ya tafi haka kawai a banza ba, in Allah Ya yarda za mu buga wadannan littattafan, ka san waye wannan mutumin? Shi ne tsohon Sakataren Gwamnatin Mulkin Soja ta Janar Ibrahim Babangida, wato marigayi Wazirin Jama’a, Alhaji Aliyu Muhammad; shi ne tsohon maigidana, wanda ya fara kai ni Makka.
Ya zuwa yanzu ka rubuta wakoki kamar guda nawa?
Ya zuwa lokacin dai da idona ya samu matsala, na daina rubutu, na rubuta wakoki sun kai dari da tamanin.
Wane irin alheri ka taba samu a sanadiyyar waka?
Tunji Braithweight ya taba ba ni kyautar mota, haka ma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi shi ma ya ba ni kyautar mota, sannan na je aikin Hajji har sau hudu. Dabo Lere, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ya kai ni, haka ma Kabiru Gaya na Jihar Kano da kuma mutumin Kafanchan, wato tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya na lokacin Babangida, wato Aliyu Muhammad (Wazirin Jama’a) duk sun kai ni aikin Hajji.
Bayan kyaututtukan da ka samu, shin ko ka taba haduwa da wata barazana a sanadiyyar wakokin da kake yi?
kwarai kuwa, barazanar kuwa da na samu ita ce, wata rana a Kaduna lokacin da za a kaddamar da Tunji Braithweight, fili ya cika makil da jama’a, muka shigo da kaset dinmu. Wallahi tallahi duk sai da muka rikita duk jama’ar da ke wurin, domin bayan mun isa inda ake sai aka ce mu juyo mu zo mu hau inda tsanin yake. To, a daidai wannan lokacin ne da muka hau wannan tsanin, Tunji ya ji irin kalmomin da nake fada, wallahi haka ya sa a dauko ni tun daga kan wannan tsanin. Ka ga da wani ya sabe min hakarkarina, wallahi sai da na dade ina rashin lafiya. To, a wannan lokacin ne na ga ana ta hayaniya a daya gefen, ashe wani ne aka kama ya cire bindiga karama (Pistol) yana so ya harbe ni; shi ne ’yan sanda suka buge hannunsa da sanda, sannan aka kama shi aka yi waje da shi; Allah dai Ya kare ni.
Ko ka taba samun wata lambar yabo daga wata hukuma?
A’a, ban taba samu ba.
Wace waka ce ka fi so a duk cikin wakokinka, wato Bakandamiyarka?
Ka dai ce in zabi wata wakar dai kawai a cikin wakokina amma ni ai kowacce a ciki Bakandamiya ce. Domin ko kai zan rera maka in ce ka zaba sai ka rasa wacce za ka zaba, domin kowace tana dauke da wata kalma wacce za ta iya dauke maka hankali. Yanzun dai wakokin da na mayar da hankali kawai su ne wakokin yabon Annabi.
Da yake an ce sarki goma, zamani goma, ko me za ka ce kan mawakan zamani da ake da su yanzu?
Ka ga wakokin yanzu ai ana sa musu kade-kade. Yanzu misali a bangaren yabon Annabi ai ba za ka taba hada wakokin Infiraji da ganga ba. Kuma duk abin da mai yabon Annabi zai fada wa Manzon Allah (SAW), idan har mai Infiraji zai yi nasa sai ka ga wancan ya zama koma baya. Mu ka ga a lokacinmu mukan duba wasu littattafai kafin mu yi waka kan wani abu. Misali, Infiraji wanda za ka ga ya sarrafa ilimi ne na wasu littattafan a ciki. Ka ga na je na yi hira da Sheikh dahiru Bauchi, na ce ya yi min bayani a kan Isra’i kawai. Bayan ya gama kalmomi biyu kawai na dauka a ciki, na sarrafa su. Sannan na je wajen marigayi Abubakar Gumi, wanda shi kuma na sa ya yi min bayani a kan Mi’iraji, shi ma bayan ya gama bayaninsa, kalmomi biyu na dauka na sarrafa. Sai kuma na je wajen marigayi Malam Nasiru Kabara, wanda shi kuma ya yi min bayani kan wani littafi mai suna ‘Saba’ul Mathani,’ sharhi a kan Fatiha. Shi ma na dauki wadansu kalmomi da na yi amfani da su wajen yabon Annabi.
Yaya batun iyali?
Alhamdu lillahi, na haifi ’ya’ya guda 13, yanzu akwai guda takwas rayayyu.
Ko akwai wani kira da za ka yi wa gwamnati?
Addu’a dai da fatan alheri kuma ina kira ga gwamnati ta kula da irin halin da ake ciki yanzu, kuma ta rika sauraron kiraye-kirayen da jama’a suke yi mata, ta taimaka da dukkan abin da ake bukatar taimakawa don dan Adam ya rayu. Allah Ya yi mata jagora.