Malam Kabir Bala ya zama Shugaban Jami’ar ABU
A makon jiya ne aka zabi Farfesa Kabir Bala a matsayin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar, Alhaji Adamu Fika ne ya sanar da zaben Farfesa Kabir Bala, inda zai kama aiki daga ranar 1 ga watan Mayun bana. An gudanar da zaben sabon shugaban jami’ar ne a Gidan Arewa da […]
A makon jiya ne aka zabi Farfesa Kabir Bala a matsayin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar, Alhaji Adamu Fika ne ya sanar da zaben Farfesa Kabir Bala, inda zai kama aiki daga ranar 1 ga watan Mayun bana.
An gudanar da zaben sabon shugaban jami’ar ne a Gidan Arewa da ke Kaduna.
Kafin zabensa a wannan matsayi, Farfesa Kabir Bala ya rike mukamai daban-daban da suka hada da Mataimakin Shugaban Jami’ar Bangaren Mulki.
Farfesa Kabir, wanda aka fi sani da Malam zai maye gurbin Farfesa Ibrahim Garba ne.
An haifi Farfesa Kabir a Unguwar Kanawa da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna a 1964, inda ya yi firamaren LEA ta Unguwar Sarki da Kwalejin Barewa, sannan ya karanta fasarar gini a Jami’ar Ahamdu Bello, Zariya, inda ya kammala digirinsa na farko a 1985.
Ya yi digirinsa na biyu a 1990 a kan fasahar gini, sannan ya yi wani digirin na biyu a 1998, kafin ya kammala digiri na uku a shekarar 2001 duk a Jami’ar ABU.
Ya fara aiki da Jami’ar ABU a watan Disamban 1987, inda har ya zama farfesa a shekarar 2007.