Malam Nazeefi Yunus da jami’an SSS suka kama ba dan Boko Haram ba ne – Jama’atu

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kasa ta nemi jami’an tsaron kasa (SSS) su gaggauta sako malamin addinin Musuluncin nan da suka kama Malam Muhammad Nazeef Yunus bisa zargin dan Boko Haram ne.A wata sanarwa da kungiyar ta JNI ta fitar dauke da sa hannun Babban Sakatarenta Dokta Khalid Abubakar Aliyu ta ce akwai bukatar […]

Malam Nazeefi Yunus da jami’an SSS suka kama ba dan Boko Haram ba ne – Jama’atu
Malam Nazeefi Yunus da jami’an SSS suka kama ba dan Boko Haram ba ne – Jama’atu

kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kasa ta nemi jami’an tsaron kasa (SSS) su gaggauta sako malamin addinin Musuluncin nan da suka kama Malam Muhammad Nazeef Yunus bisa zargin dan Boko Haram ne.
A wata sanarwa da kungiyar ta JNI ta fitar dauke da sa hannun Babban Sakatarenta Dokta Khalid Abubakar Aliyu ta ce akwai bukatar Hukumar SSS ta daina kama mutanen kirki da sunan ’yan ta’adda ne.
Ya ce labarin kama malamin Musulunci da jami’an SSS suka yi ya nuna cewa akwai bukatar su dauki matakin kare mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
“Wadanda suka san shi sun tabbatar da cewa mutumin kirki ne mai kaunar zaman lafiya. Sannan mutum ne da ke adawa da akidar Boko Haram. Abokansa sun tabbatar da cewa sun yi iyakar kokarinsu a lokuta daban-daban wajen yaki da akidar Boko Haram. Haka duk masu bin yadda al’amura ke gudana suna sane da cewa ’yan Boko Haram ba su karyata zargin kasancewarsu ’yan kungiyar. Saboda haka abu ne mai wuya a ce daya daga cikin shugabanninsu zai yi musun alakarsa da kungiyar cikin hawaye a lokacin da yake karyata zargin da ake masa,” inji Jama’atu.
Sanarwar ta kara da cewa “Ko shakka babu da shi babba ne a kungiyar kamar yadda ake zarginsa da babu yadda za a yi ya kasance malami a jami’a saboda kowa ya san cewa ’ya’yan kungiyar ba bakin adawa da boko ba ne. Kuma bayan zurfafa binciken ayyukan alamin ne, JNI ta ga ya dace ta yi kira ga hukumomin da suka dace su sake bincike sosai a kan wannan bawan Allah domin su sake shi.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Muna kara yin Allah wadai da ta’addanci a kasar nan, duk da haka za mu so mu nanata cewa a kauce wa kama mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da sunan Boko Haram, domin ci gaba da yin haka zai saka shakku a zukatan mutanen kasar nan wajen yaki da ta’addanci.”
Jama’atu Nasril Islam ta nemi al’ummar Musulmi su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, kuma su ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya sa a sako Malam Muhammad Nazeefi. Kuma ta bukaci Dokta Nazeefi ya dauki al’amarin a matsayin wata jarrabawa daga Allah.