Malam Nuhu: dan gatan mabaraci da ba ya karbar kasa da N200
Mutum zai yi mamakin abin da zai biyo baya a duk lokacin da ya ba almajiri Malam Nuhu wani abu kasa da Naira 200 a matsayin sadaka, domin ba zai karba ba, a maimakon haka ma, sai dai ya tafi ya bar wurin.Wakilanmu sun samu ganawa da wannan mutum, wanda ba kamar sauran mabarata ba, […]

Mutum zai yi mamakin abin da zai biyo baya a duk lokacin da ya ba almajiri Malam Nuhu wani abu kasa da Naira 200 a matsayin sadaka, domin ba zai karba ba, a maimakon haka ma, sai dai ya tafi ya bar wurin.
Wakilanmu sun samu ganawa da wannan mutum, wanda ba kamar sauran mabarata ba, salon barar Malam Nuhu ya bambanta da na sauran, kasancewar shi yake fadin abin da mutum zai ba shi a matsayin sadaka.
Wani kuma abin mamaki shi ne, almajiri Malam Nuhu, ba shi da wata tawaya a tare da shi. Baya ga kasancewarsa mai lafiya, ga shi kato majiyin karfi. A duk lokacin da danja ta tsayar da masu motoci, to shi kuma Malam Nuhu a lokacin ne zai rika bin motoci yana neman sadaka. Kuma ba kowace mota yake bi don neman sadaka ba, sai ya ga mota tana sheki, mutanen ciki kuma sun yi shiga mai kyau. Ko da ya kasance motarka mai kyau ce, amma ba ka yi shiga mai kyau ba, to Malam Nuhu ba zai zo wurinka ba. Idan ka yi shiga mai kyau, sannan kana cikin mota mai kyau, Malam Nuhu zai nemi Naira 200 ko N500 daga wurinka, haka kuma ba zai karbi wani abu kasa da hakan ba. Duk masu motoci da ke bin wanann hanya sun san wannan dabi’a ta Malam Nuhu.
Da zarar gari ya waye misalin karfe 7 na safe, Malam Nuhu, wanda dan asalin karamar Hukumar Bichi ne, zai zo wurin sana’arsa a shataletalen (rawul) din Dangi. Sai dai lokacin tashinsa ya danganta da yawan kudin da ya samu. Idan ya yi sa’a yakan tashi da misalin karfe 2 na rana. Idan kuma ba a samu yadda ake so ba zai tashi da misalin karfe 4 na yamma.
Yayin da yake tattaunawa da Aminiya, Malam Nuhu ya ce ya shiga wannan harka ne don ya nemi abin sanyawa a bakin salati. Ya kuma bayyana dalilinsa na kin karbar kasa da Naira 200, inda ya ce yana da bukatu da dama. “Kun ga a kullum ina zuwa wurin nan ne daga wani kauye a garin Bichi. Ina biyan kudin mashin a kawo ni bakin titi, sannan daga nan na hau mota ta kawo ni ’Yan Kura, daga nan kuma na hau wata zuwa nan Dangi. Sannan kuma ina da mata da ’ya’ya. Yaya kake tunanin zan karbi kudi marar kauri, idan na ce kannan kudi zan karba to nawa zan samu a rana har su ishe ni biyan bukatuna?”
Yayin da aka tambaye shi ko zai iya barin wannan harka ta bara idan zai samu aikin da za a rika biyansa Naira dubu 50 a wata, sai ya amsa cikin fushi ya ce, “Ba na son kowane irin aiki ko nawa kuwa za a rika biyana a wata. A kyale ni na ci gaba da wannan sana’ar da nake yi. Idan za ku ba ni sadaka, to ya yi kyau, amma idan so kuke ku bincike ni, to ku tafi ku ba ni wuri, domin wannan abin da nake yi shi ne sana’ar da na saba da ita.” Inji shi.
Wani direba da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Malam Abdullahi Shu’aibu, ya bayyana cewa Malam Nuhu ya dade yana gudanar da wanann sana’a, tun zamanin mulkin Janar Ibrahim Babangida, kusan shekaru 20 da suka wuce. “Wanann mutumin ya shafe kusan shekaru 20 yana gudanar da wanann sana’a, domin ina iya tunawa a lokacin ina aiki da wani kamfani mai zaman kansa ina ganinsa a rawul din Gidan Murtala, tun kafin a raba titin Kano zuwa Zariya. A wancan lokaci yakan nemi a ba shi Naira daya wai zai sayi allo. Daga baya ne sai kuma ya koma tambayar Naira biyar yana cewa zai sayi hatsi. Idan kun duba bara a jininsa take”. Inji direban.
Malam Abdullahi ya kara da cewa, “A duk lokacin da darajar Naira ta fadi, to shi kuma zai kara kudin bararsa. Tun daga Naira daya, ga shi yanzu Naira 200 zuwa 500 yake tambaya. Kowa ya san shi a garin nan. Ko da wasa idan ka ba shi Naira 10 ba zai karba ba.” Inji shi.
Ita ma wata mata da ke bin wannan hanya mai suna Halima Musa ta bayyana cewa da farko ba ta san halin Malam Nuhu ba don haka ta yi mamaki a lokacin da ya ki karbar Naira 50 din da ta ba shi lokacin da ya yi mata bara. “Lokacin da ya zo motar da nake ya yi min bara ya nemi na ba shi Naira 200 sai na dauko Naira 50 na mika masa, amma ga mamakina sai ya ki karba, inda kuma ya ce sai dai na ba shi kudin da ya nema. Shi fa masara zai saya da kudin. Jin haka sai na tausaya masa na ba shi N200 da ya nema, inda ya yi tafiyarsa”.
Hajiya Halima ta kara da cewa, “Lokacin da na je ofis sai na samu cikakken labarinsa don haka wata rana da ya sake zuwa ya nemi na ba shi N500 sai na sauke gilashin mota na ce masa ba zan ba shi sadakar ba, ya je ya nemi sana’ar karfi ya yi tunda dai babu wurin da Allah Ya rage shi.” Inji ta.