Malam Usman Dan Is’haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakkwato

Nasabarsa Sunansa Usman dan Malam Is’haka dan Malam Umar, ana yi masa alkunya da (Dan Is’haka). Dan kabilar Toradde ne, wata kabila da ta fito daga Futa Toro ta kasar Mali suka zo suka zauna a kasar Hausa, wadanda ake kiran shugabansu da Malam Musa Jakwallo. Haihuwarsa An haife Usman bin I’shaka (Dan I’shaka) a […]

Malam Usman Dan Is’haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakkwato
Malam Usman Dan Is’haka: Tauraron ilimi kuma fitila daga cikin fitulun Sakkwato

Nasabarsa

Sunansa Usman dan Malam Is’haka dan Malam Umar, ana yi masa alkunya da (Dan Is’haka). Dan kabilar Toradde ne, wata kabila da ta fito daga Futa Toro ta kasar Mali suka zo suka zauna a kasar Hausa, wadanda ake kiran shugabansu da Malam Musa Jakwallo.

Haihuwarsa

An haife Usman bin I’shaka (Dan I’shaka) a cikin garin Sakkwato, shekara biyu da rasuwar Shehu Usman Dan Fodiyo wato, a shekara ta 1234 Bayan Hijira, wadda ta yi daidai da 1819 Miladiyya.

Malamai sun ce, kafin hakan Malam Is’haka ya yi mafarkin ya ga rijiya cike da ruwa a cikin gidansa, mutane sun kewayeta suna sha daga ruwanta. Sai Malam Is’haka ya ji tsoro kwarai da gaske da wannan mafarki. Da safiya ta yi sai ya je ya gaya wa sheikh Usman bin Fodiyo wannan mafarki, sai mujaddadi ya ce, da shi kada ka ji tsoro a kan wannan mafarki, nan gaba INSHA ALLAHU, Allah zai arzuta ka da haihuwar wani yaro mai albarka mai ilimi, wanda zai kasance madaukaki, kuma sunansa zai watsu ko’ina a cikin garuruwa saboda yawan iliminsa. Idan Allah Ya arzuta ka da wannan da, to, ina rokonka da ka sanya masa sunana.

Bayan mafarkin sai matar Malam I’shaka ta samu juna biyu bayan ta haihu sai ta haifi yaro, sai mahaifinsa ya sanya masa suna Usman domin neman samun albarka da kwadayin ya zama malami mai halayen kirki.

Tasowarsa da neman iliminsa

Bayan tasowar Usman (Dan I’shaka) a farko ya fara da daukar karatun Alkur’ani Mai girma, bayan ya kammala karatunsa yana dan karami, sai ya soma da karatun tauhidi na kadaita Allah inda ya fara da karatun littafin Sheikh Usman bin Fodiyo mai suna Usuluddin, bayansa sai ya karanci littafin Ahlari, sai littafin Ishmawi, sai Kurdabi sai littafin Iziyya da Risala ta Abu Zaidi, sai littafin Mukhtasar Khalil.

A fanin Tafsiri ya karanta littafin tafsirin Tafsirin Jalalaini na Imamaini Jalilaini wallafar Malam Abdurrahman Muhalla da Imamu Suyudi.

Fanin Hadisi kuwa, Dan I’shaka ya soma da karatun littafin Ajarumiyya sai Mulhatul-Li’irabi, sai Kadarun-Nada sai Shuruzu-Zahabi sai Alfiyya ta Dan Maliki da sharhohinta, sai kuma littafin Hisnur-Rasin na Abdullahi Gwandu.

Amma a fanin littattafan wakoki na lugga, ya fara da karatun littafin Wasa’ilul Muttakabala, wanda aka fi sani da Ishiriniya. Sai Mu’alakatus-Saba’i, sai Mukamatul Hariri da sauran littafan da ke akwai a zamanin. A fanin ilimin furucin magana (Mandik) da Larabci ya fara da karatun littafin ilimin furucin magana na Isagoji.

Domin sanin lissafi da rabon gado, Malam Usman dan I’shaka ya karanci Ilimul Badi’i da Ilmul Ma’ani da Ilmul Aruli da sauran fanonin da suke taimakawa wajen sanin lokuta (Ilimin Hisabi) da kuma ilimin gado.

Karantarwarsa

Bayan Malam Usman dan Is’haka ya kwankwadi ilimi daga mahaifinsa sannan daga baya ya zagaya zaurukan ilimi na cikin lungu da sakon wuraren da ake bayar da ilimi, an bayyana shi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka zama fitila daga cikin fitilun Sakkwato, ko turakun ilimin Sudan.

Malam dan Is’haka gagarabadau ne a fannin ilimi, gwani a tafsirin Alkur’ani, jagaba a ilimin Larabci, kuma shugaba ne a ilimin Balaga, wanda kuma ya zamo zakakuri a ilimin Fikihu.

Za a iya cewa Malam Dan Is’haka kusan wurin neman ilimi da karantarwa ya karar da kwanukan rayuwarsa, domin an ce, ya zagaye zaurukan manyan malaman Sakkwato na lungu da sako, na nesa da kusa har daga bisani ya zama wani zakakurin masani a duk fadin Sakkwato da garuruwa da biranen da ke makwabtaka da ita.

Malam Dan Is’haka ya rayu rayuwa ta neman ilimi da yada ilimi ga al’umma, musamman ilimin addini da Sallah da matsalolinta da ilimin lissafi da ilimin gado da uwa uba ilimin luggar Larabci.

Malam Dan I’shaka bayan ya gama yawon neman ilimi ya fita daga sahun dalibai ya shiga sahun malamai, sai Allah Ya karbi rayuwar mahaifinsa Malam Is’haka sai ya dawo ya zauna a zauren da mahaifinsa yake karantarwa, shi ma ya shiga bayar da ilimi ga al’umma, inda dalibai suka rika yin tururuwa zuwa zaurensa domin kwankwadar ilimin da Allah Ya ba shi.

A makarantar Malam Dan I’shaka ana daukar karatu kusan na kowane fanni, musamman a fanin addini yana karantar da ilimin tauhidi da ilimin tsarkake zuciya (Tassawuf) da ilimin Sallah da matsalolinta, da sauran abubuwan da suka shafi sauran hukunce-hukuncen addini.

Baya ga haka kuma yana karantar da ilimin gado da ilimin luggar Larabci musamman Nahawu da ilimin Tasrifi da tarihin Larabawa da wakokinsu da hikimominsu (Adabin Larabawa).

Rubuce-rubucensa

Malam Dan Is’haka ya rubuta littafai wadanda suka tabbatar wa duniya zamansa babban malami, baban masani musamman a kan luggar Larabci.

Daga cikinsu akwai littafin da ya rubuta a kan luggar Larabci mai suna Fathu Ladifu Fi Ilimil Tasrifi. Wannan littafi, sharhi ne na wani littafi mai suna Murwi-Sadiy na Muhammad bin Salihi Al-Fulatiy Al-Magarabi, littafin an buga shi juzu’i biyu a hade waje daya, inda kashi na daya ya kunshi shafi 331, juzu’i na biyu yake dauke da shafi 427.

Malam Dan Is’haka ya kara a cikin wannan littafi misalai da bayanai kuma ya sanya a cikinsa wani karin bayani daga cikin littafin Abdullahi Gwandu mai suna Hisnur-Rasin. Kuma a cikin wannan sharhi nasa ya sanya misalai daga ayoyin Alkurani da kuma wasu wakokin Larabawa, wani lokaci kuma yakan kawo karin bayani daga fahimtarsa.

Bayansa kuma akwai littafinsa mai suna Sulamul Dalibi Ila Ma’arifatul Bina’i wal Furu’i, wannan littafin an buga shi da rubutun hannu inda ya kunshi takardu 35 kowanne shafi dauke da shadara 19.

A cikin gabatarwar littafin ya bayyana dalilin rubuta shi da cewa, bayan ya samu tambayoyi da bukatar dalibai a kan sanin ilimin gina Li’irabi sai ya rubuta shi domin amsa wannan bukata ta ’yan uwa Musulmi.

A takaice dai Malam Dan I’shaka ya rubuta littafai masu dama wadanda suka zama saukakkiyar hanya ga dalibai a fanonin addinin Musulunci, luggar Larabci, ilimin gado, Sallah da sauran fannoni wadanda littafan suka taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da malamai da dalibai a kan addinin Musulunci da ilimin lakantar harshen Larabci.

Malam Dan I’shaka yana daya daga cikin wadanda suka yi wa harshen Larabci hidima ta a-zo-a-gani domin zamowarsa masanin lugar Larabci da kuma sanin wakoki da tarihinsu.

Daga cikin littafan da ya rubuta akwai:

1. Fathu Ladif-Fi Ilmil Tasrif

2. Sulamu Dulabi-Ila Ma’arifatul Bina’i Wal Li’irabi

3. Manzumatu Fi Ilmil Arul

4. Sulamul Hudati Ila Ma’arifatu Arkanu Salati

5. Tanbihul Ikhwani-Wa Ta’alimul Halani Ala-ma Yajibu Alal Insani

6. Sulamul Gawamili Fi Ilmil Fara’ili

7. Risala Fi Sirril Kadar

Rasuwarsa

Malam Usman dan Is’haka ya karbi kiran Mahaliccinsa a 1298 Bayan Hijira, wacce ta yi daidai da 1883, Miladiyya a lokacin yana da shekaru 64. Bayan rasuwarsa an binne shi a cikin gidansa da yake kusa da hubbaren Shehu Usman a Sakkwato. Da fatan Allah Ya gafarta masa. Allah Ya saka masa da alheri kan ayyuka da hidimar da ya yi wa addinin Musulunci da Musulumi, amin.

 

Nata’ala Sambo Babi (Nasaba) ya rubuto  ne daga Birnin Sakkwato, kuma za a iya samunsa ta:

08063673656, 08096967800