Malama Hafsat Sa’idu: Burina ’yan Arewa su samu ilimin zamani
Malama Hafsat Sa’idu Ibrahim ita ce ta kafa makarantar First Academic Foundation da ke Legas, kuma Mataimakiyar Shugabar kungiyar ALKAWAS da ke tallafa wa matan Arewa. Ta yi fice wajen ilimantar da yara kanana da kuma matan aure a unguwar Ajegunle da ke yankin Apapa a Jihar Legas. Ta bayyana nasarorin da ta samu da […]
Malama Hafsat Sa’idu Ibrahim ita ce ta kafa makarantar First Academic Foundation da ke Legas, kuma Mataimakiyar Shugabar kungiyar ALKAWAS da ke tallafa wa matan Arewa. Ta yi fice wajen ilimantar da yara kanana da kuma matan aure a unguwar Ajegunle da ke yankin Apapa a Jihar Legas. Ta bayyana nasarorin da ta samu da kuma kalubalen da take fuskanta musamman wajen jajircewar da ta yi na ilimantar da matan Arewa a Jihar Legas.
Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Hafsat Sa’idu Ibrahim. An haife ni 10 ga Oktoba, 1981. Ni ’yar asalin Jihar Jigawa ce a kauyen Zaburan da ke karamar Hukumar Kaugama. Na yi karatun firamare da sakandire a Jihar Legas. Daga nan na yi Cibiyar Kula da Harkokin Koyarwa ta NTI, na samu shaidar zama malama mai daraja ta biyu. Bayan na gama sai na yi karatun NCE a cibiyar, inda na samu shaidar zama kwararriyar malamar makaranta. Da aurena na yi mafi yawan karatuna ba tare da wata matsala ba. Bayan na kammala ne na shiga harkar koyarwa gadan-gadan a wasu makarantu masu zaman kansu a Jihar Legas. Daga bisani na bude tawa makarantar mai suna First Academic Foundation, inda muke koyar da yara kanana tun daga matakin farko na Daycare da Nursery da kuma firamare. Sannan mun kafa wata kungiyar taimakon matan Arewa mai suna Alkawas Association, sannan na kafa sashen ilimin manya wato Adult Education inda nake koyar da matan Arewa karatun boko.
Dalilin da na kafa makarantar boko
E to kafin in kafa makarantata na koyar a sauran makarantu masu zaman kansu daban-daban. Na koyar a wata makaranta da ake kira Gost Power da bictoria Nursery and Primary School da sauransu. Kuma na yi shekaru ina koyarwa. A lokacin da nake koyarwa sai na lura an bar Hausawa a baya a harkar ilimin zamani a Jihar Legas, saboda haka na fara tunanin yadda zan taimaka musu, ni ma in bayar da tawa gudunmawar, sai na ga cewa ba zan cim ma burina ba sai na bude makarantata ta kaina. Sai na bude makarantata na sa mata suna First Academic Foundation. Na fara kamar da wasa amma cikin taimakon Allah ina samun ci gaba yaranmu na Hausawa da sauran kabilu suna samun ilimi. Ga shi har na yaye dalibai karo na hudu ke nan. Ko makon da ya gabata mun yi bikin yaye dalibanmu wadanda suka tafi sakandire. Mun yi bikin yaye daliban lafiya cikin nasara da kwanciyar hankali. Mun yaye dalibai 23. Kuma wurin taron ya ja hankalin iyaye su rika biyan kudin makaranta a kan kari, kuma su rika ba mu hadin kai don ci gaban ilimin ’ya’yansu.
Matsaloli
Babbar matsalar da nake fuskanta musamman ma wajen makarantar yara ita ce, iyaye maza musamman Hausawa ba sa ba mu hadin kai, kamar yadda ya kamata, sai ka ga duk abin da za mu yi a makaranta idan muka gayyace su ba sa zuwa sai dai su turo mana matansu. Sannan a bangaren matan aure inda muke koyar da matan Arewa karatun zamani, su kuma mazan ne suke kin ba matan goyon baya. Wani lokaci ma idan mazan suka ga karatun matan ya yi nisa sai ka ga sun cire su sun hana su ci gaba. Sai matsalar rashin biyan kudin makaranta daga iyaye, sai kuma matsalar nuna mini bambanci da wasu kabilu ke yi na kin kawo ’ya’yansu makarantarmu, saboda suna ganin ni ’yar Arewa ce. Ina da matsalar wuri saboda wurin da muke a yanzu ba na dindindin ba ne. Amma dangane da maigidana ba na samun wata matsala, domin ya ba ni goyon bayan da ya kamata. Don duk ci gaban da na samu shi ne sanadi.
Nasarori
Babbar nasarar da na samu ita ce, ta kafa makaranta don ilimantar da ’ya’yan Hausawa, tare da kafa sashen koyar da ilimin manya don ilimantar da matan Arewa da ke zaune a Jihar Legas. Sannan goyon bayan da matan Arewa suke ba ni ita ma babbar nasara ce. Tare da fahimtar da matan Arewa muhimmanci karatun zamani. Don matan da mazansu suka hana su fita nakan bi su gidajensu na karantar da su, kuma matan suna ba ni hadin kai sosai.
Samun tallafi daga gwamnati ko kuma jama’a
Gaskiya tun da nake wannan gwagwarmayar babu wani tallafi da na samu daga wurin gwamnati, sai dai na samu tallafi daga wurin wasu ’yan uwana ’yan Arewa, musamman ma mata. Duk abin da zan yi na wani taro ko na wani biki idan na gayya ce su suna zuwa ba tare da wata matsala ba. Babban tallafin da nake samu shi ne, daga wurin maigidana.
Burina
Burina shi ne in ga na samu babban filin da zan gina katafariyar makaranta mai ginin zamani wacce za ta yi gogayya da kowace makaranta a duniya. Na biyu shi ne, in ga ’yan Arewa sun samu ilimin zamani musamman ma mata. Don gaskiya an bar mu a baya sosai a bangaren ilimin zamani.
Burina na uku shi ne, in ga dan Arewa musamman ma Bahushe ya ci gaba. Ya samu ilimin zamani. Saboda ina bakin ciki duk lokacin da ma’aikatar ilimi ta Jihar Legas ta gayyace mu taron kara wa juna ilimi na malamai da masu makarantun boko, sai ka ga babu Bahushe ko Bahaushiya ko daya a ciki. Saboda haka ina so in ga Husawa sun rika barin ’ya’yansu mata suna karatun zamani.
Hada koyarwa da kula da iyali
Gaskiya abu ne mai wahalar gaske, sai mutum ya yi tsari kuma ya dage ya jajirce sosai, idan ba haka ba, bai zai cim ma burin da yake so ba. Sai abubuwa su cabe masa. Yadda nake yi shi ne, komai ina ware masa lokacinsa. Kamar aikin koyarwa, abu ne da yake da lokaci, daga safe zuwa rana, saboda haka ina dawo wa gida sai in shiga aikin gida gadan-gadan, sai ka ga na kammala ba tare da wata matsala ba, wani lokaci kuma sai da taimakon ’ya’yana da shi kansa maigidana. Shi kuwa ilimin manya na matan aure duk karshen mako muke yi, sai kuma matan da nake bin su gida-gida ina koyar da su, su ma na ware musu lokuta daban-daban da ranaku. Kuma ko da aiki ya yi mini yawa, maigidana mutum ne mai fahimta da hakuri da juriya da sanin ya kamata. Yakan taimaka mini, kuma wani lokaci yakan tausaya mini ya tsaya tsayin-daka ya ga komai ya tafi daidai. Abin da ya janyo haka shi ne, fahimtar juna da muka samu da soyayyar da ke tsakaninmu. Wani abu da nake jinjina masa shi ne, yadda ya toshe kunnensa daga maganganun da ake gaya masa a kaina. Babu abin da zan ce masa sai dai Allah Ya saka masa da alheri tare da iyayena da suke ba ni goyon baya.
Abinci da tufafi
Na fi son tuwon shinkafa da miyar kuka, sannan na fi son shigar Hausawa wato riga da zane da dankwali da kuma mayafi.