Malama Khadija Mahmud: Mata na da muhimmiyar rawa wajen gina al’umma

Malama Khadija Mahmud Kuta ta dade tana bayar da gudunmuwa ta fannonin rayuwa da dama, musamman game da al’amarin da ya shafi wayar wa mata kai game da muhimmancin da ke tattare da neman ilimin addini da na zamani. Ta yi bayanin dalilin da ya sa ta shiga fannin siyasa domin a dama da ita. […]

Malama Khadija Mahmud: Mata na da muhimmiyar rawa wajen gina al’umma

Malama Khadija Mahmud Kuta ta dade tana bayar da gudunmuwa ta fannonin rayuwa da dama, musamman game da al’amarin da ya shafi wayar wa mata kai game da muhimmancin da ke tattare da neman ilimin addini da na zamani. Ta yi bayanin dalilin da ya sa ta shiga fannin siyasa domin a dama da ita.

Tarihin Rayuwata
Sunana Khadija Mahmud Kuta wadda aka fi sani da Kudidi. Wannan sunan kakarmu ce Khadija, don haka ba a kira na da sunana kai-tsaye, sai dai Kudidi. A garin Kuta da ke karamar Hukumar Shiroro aka haife ni. Na yi firamare da sakandare a garin Kuta. Daga bisani, na je Jami’ar Usmanu dan Fodiyo inda na yi digirina na farko. Bayan na kammala ne na yi hidimar kasa a Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara. Na kuma yi karatun sarrafa Kwamfuta a fannoni daban-daban. Bugu da kari ina da takardar shaidar sanin makamar aikin koyarwa. Da na idar da hidimar kasar ne na kama aikin koyarwa a makarantar firamare ta Umaru Audi, daga baya aka canza mini wurin aiki zuwa makarantar firamare ta IBB da ke Minna a Jihar Neja har zuwa shekarar 2011. Na kuma yi wa wani Kamfani mai suna MARObIYA aiki a matsayin kwararriya a fannin ilimin sarrafa na’urar kwamfuta.
Mukaman da na rike
Na rike mukamai da dama wasu daga ciki sun hada da Shugabar kungiyar Inuwar Mata. A wannan kungiyar ce muka karkata akalar wayar wa mata muhimmancin neman ilimin addini da na zamani, sai kuma kasancewa cikin kwamitin tabbatar da farfado da kungiyarmu ta Gbabgyi Gbodogi. Na kasance cikin wadanda suka tabbatar da kafuwarta, sai dai ban tsaya takarar neman kowane mukami ba. Sannan na shiga cikin dalibai ’yan asalin Jihar Neja wadanda suka tabbatar da shugabanci nagari yayin da muke Jami’ar Usmanu dan Fodiyo da ke Sakkwato. Haka kuma mun taka muhimmiyar rawa a kungiyar Malamai ta kasa reshen Jihar Neja. Yanzu haka jama’a sun sake neman in fito takarar Majalisar Wakilai Ta Tarayya da ta hada da kananan hukumomin Munya da Rafi da Shiroro a karkashin Jam’iyyar APC. Mu hudu ne za mu fafata wadanda muka yanki takardar neman jam’iyyar ta tsayar da mu. Maza 3 da ni.
kalubale
Magana ta gaskiya, iyayena ba mutane ne masu karfi ba, ba don kawuna Alhaji Adamu Idris Kuta ba, da ban yi karatun da nake alfahari da shi a wannan zamanin da ya zame mini jagora a rayuwata ba. Shi ya yi mana hanya mu 5 muka samu babbar makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Bidda tare da takardar samun tallafin karo karatu ta gwamnatin Jihar Neja.
Mun kummala shekara ta farko za mu shiga shekara ta 2 ke nan, sai ya aiko direbansa ya dauko ni daga makarantar in cike fom din jami’a. Wannan ne ya zame mini dalilin zuwa Sakkwato domin karatun ilimin digiri na farko. Haka ya yi ta taimaka mini har na kammala.
Sai kuma damar da na samu ta zuwa Amurka koyon ilimin tukin jirgin sama a birnin Florida. Wannan bukatar tawa ba ta samu cim ma buri ba. An bubbuga ko Allah Zai sa a dace da wanda zai taimaka mini da kudin tallafi Naira miliyan 10, amma ba a samu ba, aka rika yi mini yawo da hankali, tun ina bi da kwarin gwiwa har na gaji na bari. Na nemi tallafi wuri wata kungiyar Zumunta da ke kasar Amurka, Allah bai sa na samu biyan bukata ba.
Ilimin Mata
A gaskiya mata suna da muhimmiyar rawar da za su taka wurin gina al’umma. Ka san mace ce za ta haifi ’ya’yan da za su ja ragamar al’umma. Ka ga idan ta samu ilimi, za ta ba ’ya’yanta har da na ’yan uwa da na makwabta. Shi namiji ba shi da wannan damar saboda idan ya fita daga gida tun da a wasu lokutan sai cikin dare zai dawo, kila kafin ya dawo yara sun yi barci, ba shi da lokacin da zai koya musu wani abu da za su fahimta hankalinsu kwance.
Siyasa
Jama’a daga sassa daban-daban sun yi ta kawo mini caffa, inda suka nemi in shiga harkar siyasa a shekarar 2011. Gaskiya na fahimci abubuwa masu yawa da na shiga harkar siyasa. A nan na fahimci cewa mu mata muna da sauran aiki a tare da mu. Hujjata ta fadin haka ita ce, har yanzu maza na yi mana kallon ba za mu iya bayar da gudunmuwar da za ta kai ga gina wannan kasar ba ta kowace fuska. Don haka suna ganin bai kamata a taimaka wa mace don ta samu nasara a duk mukamin da ta fito tana nema ba.
Yawon ziyartar jama’a da na rika yi ya sa na yi hulda da jama’a da dama da ke kananan hukumomin Rafi da Munya da Shiroro, wadanda suka hada mazabarmu ta Majalisar Tarayya. A lokacin aka kada ni a zaben fid da gwanin da aka yi. Na fito a karkashin rusasshiyar Jam’iyyar ANPP, dalili kuwa jama’armu sun fi amincewa da al’amarin adawa. Wannan ne ya sa na bi hakkina, daga baya manya suka sa baki in yi hakuri don in janye. Da haka na saurare su na ci gaba da harkokina yadda na saba.
Dalilin yin adawa
Rangadin da na yi a shekarar 2011 ya kara fahimtar da ni abu daya wanda yake muhimmi. Wannan abin kuwa shi ne, irin yadda har yanzu mutanenmu suka yi imanin tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ne zai zama Shugaban wannan kasar. Kakaninmu sun shaida mana cewa lokacin da ya share yana mulki, komai yana tafiya yadda ya kamata, saboda yadda ya cusa akidar da’a a zukatan al’ummar Najeriya, sun shaida mana cewa a lokacin ba ka isa ka aikata rashin gaskiya ba. Shi ma kansa yana nuna dabi’un da za a yi koyi da su. Ba zan manta da lokacin da Janar Buhari ya rike Hukumar PTF ba, ya malala mana ayyuka masu yawa da har yanzu ina ganinsu a zuciyata. Magunguna a asibiti, ga tituna ya shimfida duk fadin kasar nan. Yanzu ina jin labarin SURE-P, mutanen yankina ba su san da ita ba, don har yanzu ba ta taba rayuwarsu ba. Yankina na fama da ci baya, yana bukatar ci gaba kamar sauran yankuna.

Taurarina
Taurarina a wannan fannin sun hada da Janar Muhammadu Buhari da Marigayi Sanata Idris Ibrahim Kuta, sai mata da suka hada da Marigayiya Hajiya Laila Dogon Yaro da Gambo Sawaba da kuma Hajiya Naja’atu Muhammad. Wadannan mutanen da na yi nazarin rayuwarsu na ga cewa sun fuskanci tirjiya daga farko wasu har yanzu suna ci gaba da fuskanta, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba. Ni ma na lashi takobin ganin na bi wannan tsarin da suka runguma ta kwatanta gaskiya da rashin tsoro a duk al’amarin da suka yi imanin babu illa wurin aikata shi.
Tufafi
Ka san Hausawa sun ce tufafi shi ne mutum. Don haka ni tufafin da nake sha’awa su ne wadanda suka cika sharuddan da addinin Islama ya gindaya. Tun ina karama ba na sha’awar tufafin da za su nuna wani bangare na jikina ta yadda jama’a za su yi mini tambayoyin neman dalilin haka.
Yadda nake hutawa
Hanyar da nake hutawa ita ce, ina zuwa garinmu in zauna tare da Kakannina suna ba ni labarai masu ban dariya, musamman lokacin da nake karama sukan gaya mini wasu daga cikin dabi’un da na yi a baya. A nan kuma nakan hadu da mutanen da kan yi tattaki daga wurare da dama domin mu yi tozali da juna tare da mu’amala da juna ta musayar ra’ayoyi. Haka kuma mu kan hadu da abokan wasa mu yi ta raha.
Abinci
Na fi sha’awar cin abincinmu na gargajiya da suka hada da sakwara da tuwon kanwa da na toka. Game da abin sha kuwa na fi son damen tuwo da gautar daci. Yanzu haka da nake magana da kai ina da shi ajiye a dakina kullum sai na sha babu fashi.
Fatana
Babban fatana shi ne in gama da duniya lafiya, in kuma kasance wadda ta taka rawa wurin sa wa jama’a kaimi wurin sanin ’yancinsu. Su kuma sa wadanda suke wakiltarsu a gaba domin su yi musu bayanan irin wainar da ake toyawa a mukaman da suke rike da su.