Malamai 6,000 daga kasashen Afirka 10 sun halarci taron addu’a a Bauchi
Malaman addinin Musulunci dubu shida suka gudanar da addu’o’in na kwana hudu don yi wa Najeriya addu’o’in neman zaman lafiya da aka gudanar a Dandalin Babangida da ke garin Bauchi.Addu’ar Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda ne ya jagoranta, inda mahaddata da limamai da almajiran da suka fito daga kasashen da suka hada da Masar da […]
Malaman addinin Musulunci dubu shida suka gudanar da addu’o’in na kwana hudu don yi wa Najeriya addu’o’in neman zaman lafiya da aka gudanar a Dandalin Babangida da ke garin Bauchi.
Addu’ar Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda ne ya jagoranta, inda mahaddata da limamai da almajiran da suka fito daga kasashen da suka hada da Masar da Kamaru da Chadi da Senegal da Muritaniya da Aljeriya da Moroko da Ghana da Nijar da Najeriya.
A jawabinsa a yayin rufe karatun, Gwamna Isa Yuguda ya ce addu’a ce kurum maganin matsalolin tsaro da zamantakewa da suka damu kasar nan, don haka ya ja hankalin Musulmi da Kirista kan su himmatu wajen yin addu’a tare da jan hankalin mabiya domin a roki Allah Ya kawo daidaituwar al’amura a kasar nan saboda sai da zaman lafiya kowace harka za ta gudana.
Ya ce addu’a ce za ta taimaki shugabanni su iya tsayar da adalci kan aikinsu tare da yin abin da ya dace wajen shugabanci domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare rayuwa da dukiyar wadanda suke jagoranta da kuma rike amanar dukiyar kasa su gudanar da ita yadda ya kamata.
A jawabin Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce irin wannan taro domin yi wa kasa addu’a shi ne zai taimaka wajen magance matsalolin kasar nan, kuma addu’a ita ke zaunar da Najeriya lafiya ba ta kai ga wargajewa ba kamar yadda ake ganin wasu kasashe a duniya na fuskanta. Don haka ya ce addu’ar bayin Allah ke taimakawa ake samun lafawar matsalolin rashin tsaro da suka damu kasar nan.
Darakta Janar na Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Bauchi Sayyadi Ali dahiru Bauchi ya ce malaman sun yi saukar Alkur’ani Mai girma 1,111 domin neman Allah Ya kawo zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
’Ya’yan Sheikh Ibrahim Nyass wato Sheikh Ahmad Tijjani Nyass da Sheikh Umar Nyass sun jagoranci addu’ar zaman lafiya ga Najeriya da Syria da Masar da Iraki inda suka roki Allah Ya tsamar da su daga tashin hankalin da suke ciki.