Malamai a Katsina sun bukaci ’yan siyasa su yi koyi da Tata

A ranar Lahadi ne dimbin matan da mazansu suka rasu da marayu suka yi cincirindo a filin Masallacin GRA da ke Katsina, don karbar tallafin kayan sana’a daga Alhaji Abdullahi Umar Tsauri da aka fi sani da Tata. Shirin bayar da tallafin an gudanar da shi ne a karkashin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis […]

Malamai a Katsina sun bukaci ’yan siyasa su yi koyi da Tata
Malamai a Katsina sun bukaci ’yan siyasa su yi koyi da Tata

A ranar Lahadi ne dimbin matan da mazansu suka rasu da marayu suka yi cincirindo a filin Masallacin GRA da ke Katsina, don karbar tallafin kayan sana’a daga Alhaji Abdullahi Umar Tsauri da aka fi sani da Tata.
Shirin bayar da tallafin an gudanar da shi ne a karkashin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, inda malaman kungiyar suka gudanar da wa’azi a lokacin da mata dubu 12 da 700 suka bi layin tantancewa don karbar tallafin.
Manyan malaman da suka halarci taron da suka hada da Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina da Sheikh Sani Ashir, Shugaban Kwamitin Da’awa na kuniyar Izala da Sheikh AbdulWahab Abdullah (Imamu Ahlus-Sunna wal Jama’a) da Dokta Alhasan Sa’id, sun yi kira ga ’yan siyasa da masu hannu da shuni su yi koyi da Alhaji Abdullahi Umar Tata wajen tallafa wa marasa galihu, inda suka ce babu wani mutum da ya taba tallafa wa marayu masu yawa.
“Ni dai a iya sanina, babu wani mutum da ya taba gudanar da irin wannan shiri na taimakon marayu masu yawa a Katsina. Ko a Kano ma ba mu taba gani ba. Don haka mutanen Katsina sai ku gode wa Allah,” inji Sheikh Sani Ashir.
Dokta Alhasan Sa’id, ya kawo kissar wata mata da malami ya sanya ta nemo nonon bauna ne, don ta mallaki mijinta, kuma ya ce darasin kissar ita ce, ’yan siyasa da ke neman mallakar al’umma, su mara musu baya, to su rika jansu a jika, ta hanyar taimaka wa rayuwarsu. Don haka ya yi kira ga ’yan siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi da Alhaji Tata.
Kayayyakin da aka raba a wurin taro sun hada da mota kirar fijo (806) 30 da babur mai kafa uku 70 da babura 250 da firiji da kekunan dinki 350 da injin saka 1,050 da injin nika 1000 da buhunan wake da gero da man gyada 693 da gyada 694 da injin taliya 3,534 da kuma jakuna.
An kebe kwana goma don rabon kaya ga mata dubu 12 da 500, inda wata majiya ta ce Tata ya kara adadin matan zuwa dubu12 da 750.