Malamai a Zariya sun koka da kwashe makonni 10 ba Sallar Juma’a
Malaman addinin Musulunci da mazauna birnin Zariya suna ci gaba da kokawa akan kullen masallatai da ake yi wanda hakan ya jawo kwashe tsawon makonni 10 ba tare da an yi Sallar Juma’a ba a garin na Zariya. Malaman da jaridar Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa girman annobar coronavirus a birnin bai […]
Malaman addinin Musulunci da mazauna birnin Zariya suna ci gaba da kokawa akan kullen masallatai da ake yi wanda hakan ya jawo kwashe tsawon makonni 10 ba tare da an yi Sallar Juma’a ba a garin na Zariya.
Malaman da jaridar Aminiya ta tattauna da su sun bayyana cewa girman annobar coronavirus a birnin bai kai yadda za a hana mutane yin Sallar Juma’a ba na tsawon wannan lokaci.
Sun kuma kara da cewa dokar hana zirga-zirga da kuma yin jam’i ba abin da ta sabbaba a garin illa jawo wa mutanen Zariya asara da talauci da kuma rasa rayuka.
Sheikh Aliyu Abdullahi Telex, shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalitil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta jihar Kaduna, ya ce malaman da suke ba mahukunta shawarar ci gaba da rufe masallatai lallai su tanadi abin da za su gaya wa Allah a gobe kiyama.
‘Babu mai cutar a Zariya’
“Babu wani lokaci a tarihin Musulunci da annoba ta sa aka rufe daula gaba daya. Ban san wata hujja ba a kan hakan.
“Don haka duk malaman da suke ba mahukunta shawarar ci gaba da rufe masallatai, lallai su nemi abin da za su gaya Wa Allah ranar gobe.
“Babu shakka, Musulunci ya tanadi hanyoyi na hana yaduwar annoba wadanda za su iya sa a rufe masallatai amma wadannan hanyoyi ana amfani da su ne kawai a inda annobar ta faru.
“Mu a nan Zariya babu wanda zai nuna maka mutum daya wanda ya kamu da wannan cuta don ka je ka jajanta wa iyalansa ko kuma wanda cutar ta kashe don ka je ka yi wa iyalanshi gaisuwa.
“Kawai saboda hasashe, ba zai taba halasta ba a rufe masallatai a hana mutane Sallah har na tsawon makonni goma.”
A yayin da yake ba mahukunta shawara su sake nazari a kan ci gaba da rufe masallatai, Sheikh Telex ya kuma gargadi mabiya da su guji yi wa shugabanni tawaye don addinin Musulunci, a cewar shi, bai yarda da yin fito na fito da shugabanni ba.
Mutanen Zariya
Mutanen Zariya da dama da Aminiya ta zanta da su sun nuna matukar damuwarsu da wahalhalun da dokar hana shiga da fita ta haifar musu, suna masu rokon gwanatin jihar Kaduna da ta cire wannan doka don su ci gaba da gudanar da harkokin su na rayuwa da ibada.
Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ce ta fara kokawa a kan halin da al’ummar ke ciki na talauci da kuma rashe-rashen rayuka wadanda dokar hana fitar ta haifar a Zariya.
Shugaban JNI na yankin Zariya, Abdullahi Yahaya, da Sakatarensa Mahmud A. Abdullahi, sun bayyana cewa dokar ta hana shiga da fita ta janyo asarar rayuka saboda asibitoci sun yi watsi da mutane masu fama da wasu cututtuka wadanda ba coronavirus ba.