Malamai da kungiyoyin addini ku ji tsoron Allah
Abin bakin ciki ne da takaici ganin cewa a yau malamai sun mayar da addinin Allah siyasar dimokuradiyya, ita ma gwamnati ta biye musu a hakan. Dama ita gwamnati ba addini ne a gabanta ba. Ta ce ita gwamnati ce da ba ruwanta da addini. Saboda haka duk wanda ya zo da son zuciyarsa, za […]
Abin bakin ciki ne da takaici ganin cewa a yau malamai sun mayar da addinin Allah siyasar dimokuradiyya, ita ma gwamnati ta biye musu a hakan. Dama ita gwamnati ba addini ne a gabanta ba. Ta ce ita gwamnati ce da ba ruwanta da addini. Saboda haka duk wanda ya zo da son zuciyarsa, za ta biye masa matukar ta hango za ya tara mata jama’a!
A taron bikin Mauludin Shehu Ibrahim Nyass da aka gudanar a garin Kaduna, Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya tura Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Abdulrahman Dambazau ya wakilce shi. A taron Mauludin Shehu Nyass na Abuja kuma ya tura Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya wakilce shi.
Haka ma gwamnatin za ta yi da a ce bangarorin kungiyar Izala biyu ne za su yi wa’azin kasa a wurare daban-daban, ita gwamnati babu ruwanta. An wayi gari jagororin addini da malamai suna wasa da addinin Allah, ita kuwa ta biye musu, tunda ita addini ba komai ba ne a wurinta, ita kawai jama’a take nema.
Al’amari ya kasance an koma alfahari da yawan mutane da tara jama’a, a nuna wa ’yan siyasa cewa fa muna da mutane don haka dole a neme mu, kuma dole a yi da mu, abin ya koma ba Allah a cikinsa, an ajiye gaskiya a gefe.
Kuma wannan fa ba darikar Tijjaniyya kawai ba fa, a’a, wallahi dukan bangarorin kungiyar Izala haka abin yake. Su ma a yi wa’azin kasa a tara jama’a, a gayyato ’yan siyasa su gani. A nuna musu cewa fa shekarar 2019 dole ku neme mu! A gabana wallahi wani malamin Izala yake alfhari da yawansu, yake cewa ai su yanzu duk wani dan siyasa dole ya yi da su idan yana son cin nasara.
Suna ta wasa da rayukan talakawa mabiyansu. Su manyan malaman suna cikin daula da sharholiya, suna cikin jin dadi su da iyalansu, suna hawa manyan motoci, suna sa tufafin kece-raini, amma suna halakar da ’ya’yan talakawa! Sun bar talakawa cikin karuwar talauci da kunci da yunwa da rashin sanin alkibla, kuma duk da sunan addini.
Don Allah, don Allah, don Allah dan uwa ka ji tsoron Allah, ka karanta wannan rubutu nawa da idon basira, kada ka kawo wani bangaranci ko kungiyanci ko darikanci a cikinsa. Muna magana ne a kan addinin Allah da aka rabe da shi ana yin ba daidai ba. Wanda kuma na san cewa addinin Allah ya fi karfin kowace kungiya ko wata darika. Ka duba ka gani shin ba gaskiya nake fada ba?
Abin da ya kara ta da min da hankali game da wannan al’amari shi ne; jiya Asabar na kama hanya daga Abuja zuwa Keffi a Jihar Nasarawa. Wallahi idan ka ga irin wahala da galabaita da cin mutunci da hadarurruka da talakawa bayin Allah suka shiga daga Abuja zuwa Keffi bayan an tashi daga taron bikin Mauludin Shehu Nyass, za ka yi kuka da bakin ciki! Idan ka ga yadda aka jefa matafiya cikin kunci da damuwa da sunan addini, suna ta zage-zage, tsinuwa da Allah waddai, abin zai ba ka tausayi. daruruwan talakawan da suka tafi Keffi da kafar su daga Abuja kuwa, Allah ne kadai ya san iya adadinsu, saboda rashin mota. A kan wannan hanyar hadarin da ya auku jiya Allah ne kadai ya san adadinsa. An karye, an rasa rai, an yi asarar dukiyoyi, amma su manyan malaman, a lokacin da duk ake wannan, suna otel kwance su da ’ya’yansu.
Haka wannan al’amari yake a dukan kungiyoyin addinin Musulunci, wato: CI DA GUMIN TALAKAWA. Shi ya sa sam ba sa so ’ya’yan talakawa su yi karatu, su fahimci addini, su san ’yancinsu, su gane gaskiya, su san matsayin Allah da ManzonSa, su kadaita Allah Shi kadai wurin bauta, su kadaita Manzon Allah Shi kadai wurin biyayya, su so Allah da ManzonSa fiye da son da za su yi wa kowane mutum, kuma ko shi wane ne.
An wayi gari a yau, tsakanin ’yan siyasa da malaman addini ba mu san wa ya fi wasa da hankalin talakawa ba. An wayi gari a yau, yadda wadansu ’yan siyasa ke gasa wurin tara abin duniya da sharholiya da gasar hawa manyan motoci da gasar gina manyan gidaje, haka wadansu malaman addini suke yi saboda rashin tsoron Allah.
Addinin Allah ba shi ne a gabansu ba, a’a me za su samu. Sun ki yarda kan al’umma ya hadu saboda son zuciyarsu da son abin duniya. Suna ta yada karuwar rarrabuwar kai a cikin al’umma domin wannan ne hanyar cin abincinsu kuma shi ne hanyar samun kudinsu.
Sun ki yarda su dora al’umma a kan bin Allah da ManzonSa tsantsa, sai dai su a bi su, a bi kungiyoyinsu da darikunsu.
Shi ya sa aka wayi gari kullum ga mu nan sai rikice-rikicen addini, sai tashin hankali, sai zubar da jini, sai rashin zaman lafiya. Sai daba, sai sara-suka, sai kalare, sai matsalolin almajirai, sai ta’addanci da sauransu. Muna ikirarin mu ne masu addini, amma kuma matsaloli sun bi sun dabaibaye mu. Saboda ba ma tafiya a kan ainihin addinin da Allah Ya saukar wa ManzonSa, mun shigar da son rai da son zuciya a ciki. Domin babu yadda za a yi mutum ya rike addinin Allah da gaske, sannan kuma a ce ya fi kowa yawan matsaloli. Ya kamata mu koma, mu duba, sannan mu gyara.
Wallahi, wallahi, wallahi za mu mutu, Allah zai ya tambaye mu, kuma duk abin da muke yi Allah Yana kallon mu.
Allah Ya sauwake, Ya shiryar da mu hanya madaidaciya, amin.
Wassalamu alaikum
Yaushe za a gano makasan Sheikh Ja’afar?
A ranar Juma’ar makon jiya ne Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya cika shekara 11 cif da rasuwa. Kuma a yayin da muke ci gaba da yi masa addu’ar Allah Ya ji kansa Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa, har yanzu muna tunatar da hukumomin tsaro da shugabanni kan wadannan tambayoyi: “Yaushe za a gano makasan Sheki Ja’afar Mahmud Adam? Ko kuwa an sanya batun kisan gillar da aka yi masa a mala ce, sai mun je Lahira mu ga wadanda suka yi wannan aika-aika?”