Malamai kadai nake yi wa kida – Usman Mailela

Aminiya ta samu tattaunawa da Usman Mailela, wanda yake yi wa malamai kadai kida. Usman, dan asalin garin Ringim da ke Jihar Jigawa, ya bayyana abin da ake nufi da kidan Lela da yadda ya samo asali da dalilin da ya sa kidan ya takaita ga malamai kawai. Ga yadda hirar ta kasance Aminiya: Za […]

Malamai kadai nake yi wa kida – Usman Mailela

Aminiya ta samu tattaunawa da Usman Mailela, wanda yake yi wa malamai kadai kida. Usman, dan asalin garin Ringim da ke Jihar Jigawa, ya bayyana abin da ake nufi da kidan Lela da yadda ya samo asali da dalilin da ya sa kidan ya takaita ga malamai kawai. Ga yadda hirar ta kasance

Aminiya: Za mu so ka fara da gabatar da kanka…
Sunana Usman Mailela. Ni kidan Lela nake yi, wanda malamai kawai ake yi wa shi. An haife ni a kauyen Taura da ke yankin Ringim a cikin Jihar Jigawa. Ina da kimanin shekara 50; ina da mata daya da ’ya’ya uku, dukkansu suna raye.
Aminiya: Ta yaya kidan Lela ya samo asali?
Shi wannan kida sunansa kidan Lela. Shi kuma malamai kawai ake yi wa. Mu tun asali, idan mutum ba makarancin Alkur’ani ba ne, ba za mu je gidansa ba, kuma ba za mu kada masa ba. Saboda haka babu wanda ya isa mu kada masa wannan kida sai malami, komai kudinka, komai sarautarka kuma komai matsayinka da ficen da ka yi a tsakanin al’umma. Kidan ya samo asali ne tun iyaye da kakanni.
Aminiya: Shin gadar kidan ka yi ko kuwa haye ka yi?
Gaskiya gada na yi daga wurin mahaifina kuma tun ina karami nake yi. Haka na tashi na ga ana yi a gidanmu. Saboda haka mahaifina ne ya koya mini kida da wakar Lela. Shi ne ni ma na ci gaba da yi, kamar yadda iyayena suka koya mini, kuma da shi nake cin abinci, da shi nake yin sutura na ciyar da iyalina, na yi kyauta, na yi sadaka da sauran dawainiyar rayuwa ta yau da kullum.
Aminiya: Me ya sa ka zabi ka yi kidan Lela a maimakon ka yi wata sana’a da watakila za ta fi kawo maka kudi?
To, gaskiya Allah Madaukakin sarki shi ne ya dora ni a kan wannan kida, kuma Ya riga Ya kaddara zan ci abinci a cikinsa. Amma kullum na yi addu’a ina rokon Allah Ya raba ni da shi, Ya zaba mini sana’ar da ta fi amfani. Shi wannan ka san abu ne na gargajiya, wanda iyaye da kakaninmu suka bar mana, shi ya sa barinsa yake da wahala.
Aminiya: Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu tun da ka fara kidan Lela?
Na samu nasarori da dama da suka hada da samun ’yan kudin da zan ci abinci. Sannan kuma ta hanyar wannan kida na hadu da mutane da yawa da ban taba zaton zan san su ba. Na yi suna a garuruwa da jihohi da dama, mutane da yawa sun san ni. Nakan samu Naira dubu biyu zuwa dubu biyar. Sannan a kauyuka na Arewa akan ba ni kyautar kudi da abinci da kayayyaki da sabulai har ma na kai wa iyalina.
Aminiya: Me ya sa kake kidan a Legas, maimakon ka ci gaba da yi a Arewa inda aka san kidan?
Ai nan Legas ma akwai malamai, mu kuma da ma ainihi malamai muke yi wa. Ba wai sai a Arewa ba, ko’ina ka je a duniya, ai za ka samu malamai da yawa. To shi ya sa na yanke shawarar zuwa Legas domin haduwa da jama’a, mutane su san ni ni ma na san su.
Aminiya: Da me ake yin butar da ake kidan Lela da ita?
Ana yi da duma ne, bayan an ciro sai a fafe shi, a ajiye har ya bushe, sai a saka masa karafa a wuyansa, ta yadda idan ana buga duman sai karafan su rika kara suna fitar da sauti mai dadi.
Aminiya: Ka shafe shekara nawa kana kidan Lela?
Tun da aka yaye ni ake tafiya kidan Lela da ni, iyayena sukan tafi su kamar 60 a lokaci guda kuma suna yin kidan a tare da rera wakoki daban-daban. Abin gwanin sha’awa, sai ka ji yadda ake yi. Shi kidan Lela yana da shiga jiki. Yana tsuma malamai. Ana buga wa malamai, sai ka ga sun tashi suna rawa suna buga buzu suna zagayawa, sai ka ga suna ba mu kyaututtuka daban-daban.
Aminiya: Wakoki nawa ka yi a yanzu?
Gaskiya ban san yawan wakokin da na yi ba, amma na san suna da yawa, kuma nakan yi salon sautin kidan daban-daban. A cikin wakokin da na yi na fi son wakar ‘Maijallo In ba ka labarin duniya’, ita ce bakandamiyata. Na yi wa Malam Musa saboda shi ne limamin Hausawa kuma shi ne Sarkin Hausawan Agege. Bayan haka na yi wakar ‘Sari Zubar’ da wakoki da yawa.
Aminiya: Wadanne matsaloli kake fuskanta a kidan Lela?
Gaskiya akwai matsaloli, wani idan ka kida masa, bai san abin da ake nufi da kidan ba, domin mutane da dama ba su san abin da ake kira kidan Lela ba. Wani sai ya rika yi mini kallon macuci. Mutane kadan ne suka san kidan Lela a wannan zamani, yaran yanzu ba su san shi ba.
Aminiya: Kana da burin ’ya’yanka su gaje ka?
Gaskiya ba na burin ’ya’yana su gaje ni. Ina da da daya namiji, amma ba na son ya gaje ni. Burina shi ne idan ya girma na kai shi makaranta ya yi karatun boko da na addini, ba na sha’awar ya yi kida da waka irin yadda nake yi a yanzu.