Malamai ku guji raba kan Musulmi – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah Shiekh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga malaman kasar nan su ji tsoran Allah su guji raba kan al’ummar Musulmi. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a wajen taron yaye daliban Makarantar Horar da Limamai da Ladanai da […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah Shiekh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya yi kira ga malaman kasar nan su ji tsoran Allah su guji raba kan al’ummar Musulmi.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a wajen taron yaye daliban Makarantar Horar da Limamai da Ladanai da Alkalan Musabaka na kungiyar da aka gudanar a ranar Juma’ar da ta gabata a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya da ke ke Jos, inda ya ce “mu dage wajen karantar da al’ummar Musulmi tsantsar addini, maimakon rarraba kawunansu.”
Sheikh Sani Yahya Jingir wanda Mataimakin Shugaban Majalisar na Biyu, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya wakilta, ya yi nasiha ga Musulmi kan su rungumi zumunci.
“Mu yi zumunci mu kyautata wa danginmu, wanda duk yake son ya yi tsawon rayuwa a duniya ya sadar da zumunci,” inji shi.
Sheikh Jingir ya yi kira ga daliban da aka yaye kan su yi aiki da abubuwan da aka koya musu a makarantar. Ya ce idan aka hada ilimi da aiki akwai ban sha’awa kuma aiki da karatu shi ne ilimi.
Tunda farko a jawabin shugaban makarantar Ustaz Aminu Yusuf Nuhu ya ce Sheikh Sani Yahya Jingir ne ya bude makarantar a shekarar 2001 da manufofin samar da kwararrun alkalan gasar karatun Alkur’ani da ilimintar da limamai da ladanai kan ayyukansu da sauransu. Ya ce daga lokacin da aka bude makaranta zuwa yanzu ta yaye dalibai 1,105, inda a wannan karo ta yaye dalibai 56.