Addu’a ya kamata Malamai su riƙa yi wa Najeriya ba la’anta ba — Tinubu
Shugaba Tinubu ya bukaci malamai su zama masu tasiri ga al’ummar kasar nan.
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga shugabannin addini da su daina tsine wa Najeriya a tarukansu ko wa’azi.
Tinubu ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis, yayin buɗa-baki da malaman addinai da masu sarautun gargajiya.
- ’Yan sanda sun kama riƙaƙƙun ’yan daba 22 a Kano
- An kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda Junaidu Fasagora a Zamfara
“A ranar Laraba na halarci jana’izar sojoji 17 da aka kashe a Okuama, Jihar Delta. Na ga matansu masu ciki da yara kanana.
”Soyayyar al’umma tana hannunku. Ku yi wa kasarmu addu’a. Ku bai wa yaranmu ilimi da tarbiyya. Wa’azin da muke yi wa mutane a coci da masallatai suna da muhimmanci.
“Kada ku la’anci al’ummarku. Wannan ita ce kasarku; kar a yi Allah-wadai da ita a cikin wa’azi, kada ku zagi kasar nan. Shugabanci na nufin kawo sauyi.
“A ce wannan shugaban ba shi da kirki, wannan ba laifi ba ne. Amma ku bari sai zabe na gaba sai ku sauya shi, amma ku daina la’antar kasar nan. Kar ku zagi Najeriya. Wannan kyakkyawar kasa ce.”
Shugaban ya nusar da su muhimmancin sauya akidun mutane, ta hanyar cusa musu kishin kasa da dora su a hanya mafi dacewa.
Tinubu, ya bukaci shugabannin addinai da suka kasance masu adalci wajen sukar masu rike da mukaman siyasa.
A gefe guda kuma, Tinubu ya jadadda wa shugabannin aniyarsa ta magance ɗimbin matsalolin da ake fuskanta a kasar nan.
Shugaban Tinubu ya kuma bukaci shugabannin gargajiya da na addinai da su kulla alaƙa mai karfi da gwamnati domin kawo karshen ayyukan ta’addanci da sauran laifuka a kasar nan.
Taron buɗa-bakin ya samu halartar sarakunan gargajiya daga Arewaci da Kudancin Najeriya da kuma malaman addinin Musulunci da na Kirista.
Mahalarta taron sun yaba wa Tinubu kan salon mulkinsa da kuma yadda yake jajircewa wajen kawo wa Najeriya sauyi mai dorewa.