Malamai sun shiga yajin aiki kan rashin biyan su sabon albashi a Abuja

Malaman sun ce za su ci gaba da yajin aikin har sai an biya dukkanin haƙƙoƙinsu.

Malamai sun shiga yajin aiki kan rashin biyan su sabon albashi a Abuja

Malaman Makarantar Firamare a Babban Birnin Tarayya, sun fara sabon yajin aiki, wanda hakan ya hana ɗalibai kammala jarabawar zangon karatu na farko da suka fara.

Yajin aikin na nuna rashin gamsuwar malaman kan gazawar shugabannin ƙananan hukumomi na aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da biyan bashin da suke bi.

Wannan shi ne karo na biyu da malaman ke tsunduma yajin aiki a wannan zangon karatun.

Wannan na zuwa ne bayan yajin aikin farko da suka yi a watan Satumba.

A ranar Litinin, ɗaliban da suka tafi makaranta domin rubuta jarabawa, an kora su gida.

Da yake magana kan batun, Shugaban Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT) reshen Kubwa, Kwamared Ameh Baba, ya ce, an gaza cika musu alƙawarin da aka ɗaukar musu.

“Shugabannin ƙananan hukumomi sun gaza biyan sabon mafi ƙarancin albashi da aka amince da shi kuma har yanzu muna binsu bashin albashi.

“Wa’adin ranar 1 ga watan Disamba da Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya ta bayar ya ƙare, ba mu da wani zaɓi sai mu ɗauki mataki.”

Kwamared Baba, ya tabbatar da cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi tare da alƙawarin biyansu albashin watan Nuwamba.

Sai dai ya ce wasu malamai, musamman na UBEC, ba su samu kuɗinsu ba.

“Har yanzu muna bin bashin Naira 40,000 na alawus da kuma Naira 35,000 na kyautar albashin ƙarshen shekara,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, yajin aikin zai ci gaba har sai an biya dukkanin haƙƙoƙinsu da suke bi.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta