Malamai sun yi watsi da ka’idojin bude masallatai a Ilori
Majalisar Malaman Birnin Ilori a jihar Kwara ta yi watsi da ka’idojin da gwamnatin jihar ta sanya na bude masallatai a jihar. Malaman sun bayyana ka’idojin gwamnatin a matsayin tsaurara da babu yadda za a iya cika su. A sanarwar da Sakataren Majalisar Malaman, Mai Shari’a Salihu Olohuntoyin Mohammed (mai murabus) ya fitar, Majalisar ta […]
Majalisar Malaman Birnin Ilori a jihar Kwara ta yi watsi da ka’idojin da gwamnatin jihar ta sanya na bude masallatai a jihar.
Malaman sun bayyana ka’idojin gwamnatin a matsayin tsaurara da babu yadda za a iya cika su.
A sanarwar da Sakataren Majalisar Malaman, Mai Shari’a Salihu Olohuntoyin Mohammed (mai murabus) ya fitar, Majalisar ta ce:
“Kayyade shekarun masu halartar Sallar Juma’a zuwa kasa da 65 abu ne mai wuya, domin a Musulumci limamai su ne jagororin addini, kuma akasarinsu sun haura shekaru 65.
“Mun kuma lura daukacin ka’idojin na da matukar tsauri wadanda zai yi wuya a tursasa jama’a su cika su.
“Don haka muke kira ga gwamnatin da ta ci gaba da rufe masallatan Juma’a har sai ta sake duba a kan ka’idojin”.
A kwanakin baya ne Kwamitin Yaki da Annobar COVID-19 na jihar Kwara ya zayyana ka’idojin da za abi a yunkurin gwamnatin jihar na bude masallatan Juma’a daga ranar Juma’a 5 ga watan Yuni.
Sai Majalisar Malaman ta ce sun yi tsauri matuka duk da cewa tana sane an yi hakan ne domin dakile yaduwar annobar a jihar.