Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi 

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya zargi malaman addini yaudarar mabiyansu domin samun abin duniya.

Malaman addini na yaudarar mabiyansu saboda abin duniya — Sarkin Musulmi 

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya zargi malaman addini yaudarar mabiyansu domin samun abin duniya.

Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya gargaɗe su a kan hakan sannan ya umarce su da su tuba, su riƙa gudunar da wa’azi ta hanyar ingantacciyar koyarwar Musulunci don gina al’umma ta gari.

Ya bayyana haka ne a wajen taron yankin kan rikicin da ke haifar da sauyin yanayi a Arewacin Najeriya, wanda aka gudanar ranar Litinin a Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ofishin kula da addinai na Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar International Alert ne suka shirya taron.

“Ina shawarar shugabanninEFCC ta tsare tsohon Gwamnan Delta kan badaƙalar tiriliyan N1.3 addini da su guji yaudarar mabiyansu don amfanin kansu. galibin mabiya suna daukar malaman addini a matsayin jagorori kuma suna dogara sosai a kansu.

“Ku yi iyakar kokarinku wajen bauta wa Allah, kuma ku bar maSa komai. An samu ƙalubale da dama a ƙasar nan, amma mun yi imanin cewa komawa ga Allah da yawaita addu’o’i a wuraren ibada zai kawo abin da ake fata.

“Wahalar nan ta ɗan lokaci ne, kuma babu abin da ke dawwama har abada. Mu ci gaba da yi wa shugabanninmu addu’a, mu guji la’anatar su, muna da imanin cewa Allah zai kawo mana sauƙi kamar yadda Shi ne masani kuma mai gani,” inji shi.

Sarkin ya bukaci ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanninsu, maimakon haka, su damka su ga hukuncin Allah.

A yayin da yake ƙarfafa ’yan ƙasa da su ci gaba da yi wa shugabanninsu da al’ummarsu addu’a don samun zaman lafiya da haɗin kai da ci-gaba, Sarkin Musulmi ya ce: “Babu wani abu, mai kyau ko mara kyau, da ke dawwama har abada.”

Da yake jawabi ga shuwagabannin, Sarkin Musulmi ya tunatar da su irin hisabin da Allah zai yi musu a gobe kiyama, “inda za ku fuskanci bincike kan ayyukanku ba tare da wani ya kare ku ba.

“A ranar karshe, kowa shi kaɗai za a tsayar a gaban Allah, babu mataimaki ko mai ba da shawara da zai kasance a wurin don tallafa muku.

“Mu yi wa kanmu hisabi, mu yi kokarin ganin mun samar da kasa mai inganci ta hanyar imani da juriya,” in ji shi.