Malaman addini sun shirya wa matasa bitar zaman lafiya a Yobe

An yi kira ga matasa da su yi riko da kyawawan dabi’u daga koyarwar Annabi Muhammad SAW.

Malaman addini sun shirya wa matasa bitar zaman lafiya a Yobe

Malaman addini a Jihar Yobe tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da addini ta jihar sun yi wa matasa bita kan wajabcin wanzar da zaman lafiya da sulhu da juna a tsakanin kungiyoyin Musulunci daban-daban a jihar.

Wannan taro na hadin kai a tsakanin matasa mabiya kungiyoyin addinai daban-daban an gudanar da shi ne a cibiyar addinin musulunci ta tunawa da Marayu da ke garin Nguru.

A yayin taron an yi wa matasan bita kan batutuwa da dama musamman halin kirki, hakuri, da kyawawan dabi’u wajen zama da juna musamman a tsakanin kungiyoyin musulunci daban-daban.

Shugabannin Addinin da suka jagoranci taron yi wa matasa bitar a Yobe.

An yi kira ga matasa da su yi riko da kyawawan dabi’u daga koyarwar Annabi Muhammad SAW wajen gudanar da huldar su da juna a matsayin ’yan uwan da musulunci ya hada su.

Daga cikin manyan baki da suka halarci taron akwai, Mai Martaba Sarkin Machina, Alhaji Bashir Albishir Machina, a matsayin babban bako na musamman da kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na jiha, Sani Inuwa Nguru, Shugaban Karamar Hukumar Nguru da sauransu.

DAGA LARABA: Yadda Almajiri Ya Zama Mabaraci

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato