Malaman da suka halarci taron Kaduna sun yi abin kunya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce malaman da suka halarci taron da aka shirya wa kungiyoyin addinin Musulunci da limamai da malaman makarantun Islamiyya na Shiyyar Arewa maso Yamma a makon jiya gabata a garin Kaduna, sun yi abin kunya.  Sheikh […]

Malaman da suka halarci taron Kaduna sun yi abin kunya – Sheikh Jingir
Malaman da suka halarci taron Kaduna sun yi abin kunya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce malaman da suka halarci taron da aka shirya wa kungiyoyin addinin Musulunci da limamai da malaman makarantun Islamiyya na Shiyyar Arewa maso Yamma a makon jiya gabata a garin Kaduna, sun yi abin kunya. 

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da wa’azi a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya da ke garin Jos a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya
ce wadanda suka halarci wannan taro da sun yi aiki da iliminsu da ba su halarce shi ba.
Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa da mutanen da suka karbi kudi a baya, suka goyi bayan gwamnatin da take kashe jama’ar kasar nan tare da lalata komai da ba su sake karbar kudi don sake goyan bayan tazarce ba.
Ya ce abin da takaici a ce har yanzu za a samu wasu malamai a kasar nan da za su tafi har kasa Mai tsarki suna rokon Allah Ya sake dora gwamnatin da take kashe jama’ar Najeriya.
Ya ce babu shakka halin da muke ciki a kasar nan malamai masu kwadayi da sarakuna masu kwadayi sun bata sunan malamai da sarakuna. Ya ce ya kamata jama’ar Najeriya su yi tunani su kiyayi kudin wadanda suka zubar da jinin al’ummar kasar nan, su zabi wanda zai kawo musu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar nan a wannan zabe da za ayi.
Ya ce yanzu jama’ar Najeriya Musulmi da Kirista sun gane, don haka masu kulla wa Najeriya sharri su tuba su dawo don a taru a gina kasar nan.
Ya yaba wa Hukumar Zabe ta kasa (INEC) kan shirin da ta yi a kan zaben da za a yi, tare da yaba wa jama’ar Najeriya kan yadda suke ta fitowa suna karbar katin zaben.