Malaman firamare sun janye yajin aiki a Abuja
Za a jinkirta jarabawa domin a kammala darussan da aka dakatar saboda yajin aikin
Malaman makarantun firamare a Abuja sun janye yajin aikin da suka shafe mako biyu suna gudanarwa.
Da farko malaman sun shiga yajin ne saboda hukumomin birnin tarayya sun ki aiwatar da karin albashin da suka cancanta bayan an yi musu karin matsayi.
- Daliba ta bude shafin koyar da Lissafi da harshen Hausa
- Daliban Islamiyya 20 sun rasu a hatsarin kwalekwale a Kano
Shugaban Kungiyar Malamai (NUT) reshe Kubwa, Kwared Ameh Baba, ya tabbatar wa wakilinmu cewa an janye aikin ne a ranar Laraba, kuma nan take ake sa ran dalibai su koma makarantu.
Ya ce sun janye yajin aikinne bayan Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello da Sanatanta, Philip Aduda sun sanya baki domin yi wa tufkar hanci.
Kwamred Ameh, ya bayyana takaicinsa kan yadda shugabannin kananan hukumomin Birnin Tarayya ke yi wa harkar ilimin yara rikon sakainar kashi.
“Abin takaici shi ne ana cikin wannan yajin aikin, mutum uku daga cikin suka tafi Dubai kuma har yanzu ba su dawo ba, watakila sai bayan bukukuwan Kirsimeti”, inji shi.
Ya ce kungiyar za ta nemi a jinkirta lokacin fara jarabawa da aka tsara farawa ranar 5 ga watan Disamba, domin malamai su damu damar kammala darussan da ba su yi wa dalibai ba saboda yajin aikin.
A ranar 24 ga watan Nuwamba, takwarorinsu na makarantun sakandare suka janye yajin aikinsu na gargadi na kwana biyar.