Malaman Firamare sun janye yajin aiki a Abuja 

Malaman sun janye yajin aikin ne biyon bayan wani zama da suka yi da Wike.

Malaman Firamare sun janye yajin aiki a Abuja 

Malaman Makarantun Firamare na Babban Birnin Tarayya da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Malamai ta Najeriya (NUT), sun dakatar da yajin aikin da suka shiga.

A ranar 18 ga watan Satumba, 2024, ƙungiyar ta umarci malaman daga ƙananan hukumomi guda shida, da su shiga yajin aiki.

Hakan ya biyo rashin biyan ragowar kashi 60 na albashin watanni 25, da rashin aiwatar da biyan ragowar kashi 40 na alawus na musamman, da wasu haƙƙoƙi.

A ranar Litinin, bayan taron gaggawa da malaman suka yi a Gwagwalada, Shugaban NUT na Abuja, Abdullahi Mohammed Shafas, ya sanar da cewa an dakatar da yajin aikin.

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar hakan ne bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin biya buƙatun malaman.

A cewarsa ministan ya yi alƙawarin fara da biyan ragowar kashi 60 na albashinsu.

Wike ya umarci ofishin ajiyar kuɗin Abuja da su yi amfani da kashi 1p na kuɗin shiga da ƙananan hukumomi suka tara don biyan malaman.

Shafas, ya kuma ce ƙungiyar ta yi la’akari da jajircewar ministan wajen biyan sauran buƙatun malaman, wanda hakan ya sa suka dakatar da yajin aikin.

Duk da haka, ƙungiyar ta roƙi ministan da ya gaggauta ɗaukar mataki kan sauran matsalolinsu, irin su biyan alawus ɗin kashi 40, alawus na Naira 35,000, da ƙarin albashi na kashi 25 da 35 da zarar an biya su ragowar kuɗaɗen da suke bi.

Ya bayyana damuwarsa kan halin da malaman Firamare ke ciki a Abuja, inda yana zargin ƙananan hukumomi da rashin kula da hakkokin malaman duk da mawuyacin halin tattalin arziƙi da ake ciki a ƙasar nan.

Kazalika, ƙungiyar ta buƙaci dukkanin malaman Firamare na Abuja, da su koma bakin aiki daga ranar Talata, 8 ga watan Oktoba, 2024.

Ƙungiyar ta ce ta tabbatar da cewar za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin an biya malaman sauran haƙƙoƙinsu da kuma inganta walwalarsu.

Tinubu ya buƙaci a zauna lafiya a Ribas

Malaman Firamare sun janye yajin aiki a Abuja 

Gwamnatin Kogi ta amince da N72,500 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Ma’aikatan NAFDAC sun tsunduma yajin aiki