Malaman Firamare sun sake tsunduma yajin aiki kan rashin albashi a Abuja
Shugaban ya ce ba za su janye yajin aiki ba har sai an biya buƙatunsu.
![Malaman Firamare sun sake tsunduma yajin aiki kan rashin albashi a Abuja Malaman Firamare sun sake tsunduma yajin aiki kan rashin albashi a Abuja](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/FCT.png)
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), sun umarci malaman makarantun firamare da ke ƙarƙashin Sashen Ilimin Ƙananan Hukumomi (LEA) da su sake tsunduma yajin aiki.
Haka kuma an umarci ma’aikatan ƙananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, da su dakatar da aiki daga ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025, sakamakon rashin biyan mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da shugabannin ƙananan hukumomi suka yi.
- An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe
- Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf
Shugaban Ƙungiyar NUT reshen Abuja, Kwamared Mohammed Shafas, ya bayyana cewa ƙungiyoyin sun yanke shawarar sake komawa yajin aikin ne saboda gazawar shugabannin ƙananan hukumomi shida wajen aiwatar da mafi ƙarancin albashi.
Ya tunatar da cewa malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi sun dakatar da yajin aiki a ranar 12 ga watan Disamban 2024 ne, bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da shugabannin ƙananan hukumomi.
Ya ce an yi yarjejeniyar ne domin fara aiwatar da biyan albashin Naira 70,000 daga watan Janairun 2025.
Sai dai, duk da hakan, shugabannin ƙananan hukumomin sun yi watsi da yarjejeniyar.
Kwamared Shafas, ya ƙara da cewa ba wai rashin aiwatar da mafi ƙarancin albashin ne kaɗai ya jawo yajin aikin ba, har da gazawar shugabannin wajen biyan wasu haƙƙoƙin ma’aikata.
Ya ce buƙatun da ba a biya ba sun haɗa da kashi 40 na alawus-alawus, ƙarin albashi na kashi 25 da 35.
Ya ce, sai an biya waɗannan haƙƙoƙi kafin malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi su koma bakin aiki a Abuja.