Malaman jami’a mata suna fuskantar kalubale da dama – Dokta Hauwa Muhammad Bugaje
Dokta Hauwa Muhammad Bugaje malama ce a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka a Tsangayar Fasaha ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A hirarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da kalubalen da ta fuskanta da kuma nasarorin da ta samu: Tarihina Sunana Hauwa Muhammad Bugaje, an haife ni a garin Bugaje da ke Karamar […]
Dokta Hauwa Muhammad Bugaje malama ce a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka a Tsangayar Fasaha ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A hirarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da kalubalen da ta fuskanta da kuma nasarorin da ta samu:
Tarihina
Sunana Hauwa Muhammad Bugaje, an haife ni a garin Bugaje da ke Karamar Hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina kimanin shekara arba’in da suka wuce. Amma na yi mafi yawan rayuwata ne a birnin Katsina inda gidanmu yake. Na yi makarantar firamare ta Nagwaggo da ke Katsina kafin in wuce Makarantar Sakandare ta Mata ta garin Mani inda na yi aji 1 zuwa 3 daga nan sai na koma Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta garin Charanchi inda a can na kammala. Daga nan kamar yadda al’adar Hausawa take sai aka yi mini aure aka kawo ni nan garin Zariya. Ina gidan mijina kuma sai na shiga karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Zariya a 1995. Na gama makarantar a 1998. Bayan mun koma da zama a garin Shika da mijina sai na fara koyarwa a makarantar Shika Model Primary inda na yi shekara biyu, sai na ga akwai bukatar in koma makaranta don karo ilimi.
Don haka sai na dawo na nemi gurbin karatu an Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma cikin taimakon Allah aka ba ni kwas din Hausa. Wannan ne ya sanya na yi matukar farin ciki ganin cewa na samu an ba ni wannan kwas na nazarin harshen Hausa. Domin tun lokacin da na gama NCE na yi ta neman gurbin shiga wannan jami’a don in karanta Hausa amma ban samu ba, sai su ba ni wani kwas na daban, wanda ni kuma na ki yi sai a karo na uku ne aka ba ni Hausa wanda na kammala a shekarar 2005.
Bayan na kammala sai aka turo ni aikin yi wa kasa hidima (NYSC) a nan sashen namu na Harsuna da Al’adun Afirka, inda na taimaka wa malamai wajen karantarwa da kuma gudanar da harkar dalibai. To bayan na kammala wannan aiki na yi wa kasa hidima sai suka nemi cewa in rubuto za su dauke ni aiki in ci gaba da karantarwa a wannan sashe, nan take na rubuta. Kuma a cikin wancan shekara Allah Ya taimaka takardar kama aikina ta fito na zama daya daga cikin malaman wannan sashe a shekarar 2007.
Ina nan sannu a hankali sai na fara karatun digiri na biyu a wannan sashe na kammala a shekarar 2011. Cikin sa’a, bayan na kammala karatun digiri na biyu a shekarar sai na sake samun gurbin karo karatu na digiri na uku (PhD) a wannan sashe. Na kammala karatun a shekarar 2014, ka ga duk rayuwata in ban da ta kuruciya a nan na yi ta a Zariya haka rayuwata ta karatu da aiki duk a nan ABU ne.
Rubutu
Na yi rubuce-rubuce da dama a kan abin da ya shafi harshe da adabi sun kai wajen 14 kuma suna nan ana ta nazarinsu ana karuwa a makarantu. Sannan akwai littafin wasan kwaikwayo da na rubuta a lokacin ina daliba ajin karshe a jami’a, mai suna ’Abin da kamar wuya…’ Abin da ya ja hankalina a wancan lokaci na rubuta littafin shi ne irin yadda na lura cewa akwai karancin litttattafan wasan kwaikwayo wadanda suka kunshi ainihin adabin Bahaushe da za a iya karantarwa ba tare da jin dar-dar ba wato ba tare da ganin abubuwan da suka saba wa ainihin rayuwar Bahaushe ba. Abu na biyu da ya ja hankalina shi ne a zaman da na yi a matsayin daliba a jami’a na lura da yanayin da dalibai mata suke ciki na kalubale da wahalhalu. Daga nan sai na rubuta shi a kan rayuwar ’ya mace a jami’a.
Kuma alhamdulillahi, wannan littafi na ‘Abin da kamar wuya,’ yanzu haka an yi rubuce-rubuce na digiri na uku a kansa, an yi digiri na biyu a kansa. Don digiri na daya ban ma san iyakar wadanda suka yi a kansa ba a jami’o’i daban-daban. Kai a halin yanzu ma an samu wani dalibi da ya fassara shi a harshen Larabci kuma yana nan suna amfani da shi a Sashen Larabci na Jami’a. Sannan ko shahunnan malamai na wasan kwaikwayo sun yaba da shi kuma yana daya daga cikin littattafan wasan kwaikwayo da suke tinkaho da shi.
Nasarori
To alhamdulillahi na samu nasarori sosai a rayuwa. Duk da yake gidanmu gidan ilimi ne wanda ba ni ce ta daya ko ta biyu da ta yi digiri na uku ba, amma dai ni a wajena wannan ma nasara ce. Sannan idan ka dubi yadda Hukumar Ilimi ta sanya littafina na wasan kwaikwayo na ‘Abin da kamar wuya’ cikin littattafan da ake koyarwa a sakandare da IJMB da jami’o’i wannan ba karamar nasara ba ce. Sannan kuma kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba (NGOs) suna gayyatata tarurruka daban-daban a garuruwa da dama ciki har da Abuja don in je in gabatar musu da kasida ko wata mukala a matsayina na mace mai koyarwa a jami’a kuma wacce take da digiri na uku (PhD). Kuma suna gayyata ta ce don in kasance abin misali musamman ga ’yan makaranta mata masu tasowa.
Kalubale
To an ce wai kowa ya ci zomo to kuwa ya ci gudu. Kuma a duk inda ka ga an ci nasara ba za a rasa fuskantar kalubale ba. Duk da yake watakila saboda kalubalen ya riga ya wuce an manta da yawa daga cikinsa. Da farko ban samu wata matsala ba ga daukar nauyin karatu, tunda yake yayyena a tsaye suke a kan ilimi ba sa wasa da duk wani lamari na ilimi, kuma gidan da na fito ba ni ce mace ta farko da ta yi karatu mai zurfi ba. A halin yanzu mun kai mu uku masu digiri na uku, kai ko matan yayyenmu ma duk masu ilimi ne. Matan yayyen namu sun zame mana abin koyi tunda a cikinsu akwai farfesoshi. Ga shi kuma na samu kwarin gwiwa daga mijina wanda a koyaushe yana karfafa ni da yin karatu.
Amma babban kalubalen da na fuskanta a rayuwa bai wuce na hada karatu da aure ba, wato tarbiyyar iyali. Domin a ce ka je aji kuma kana rainon jinjiri watakila ma da wasu sauran yara a gida da za ki dauka zuwa makaranta ba karamin aiki ba ne. Abu ne wanda idan mace ba ta tsaya ta tsara lokacinta ba sai ya ba ta ruwa.
Domin babban kuskuren da mata ke yi a yanzu shi ne na mayar da rainon yaransu ga masu aikin gida ko mai raino. Wannan yana debe karsashin soyayyar da take samuwa a tsakanin mahaifiya da ’ya’yanta. Don haka ya kamata mace mai karatu kuma mai yara ta san cewa karatu ba zai hana mata kula da yaranta ba, in dai har za ta tsaya ta tsara lokacinta da kyau.
Sai kalubale a matsayina na mace malamar jami’a, wanda kuma kalubale ne da yake damun mafi yawan mata masu aiki a wannan jami’a. Kamar a wannan sashe da nake akwai rashin isassun ofisoshi wanda hakan yakan sa wani lokaci ka ga an hada mace da namiji a ofishi daya. Ka kuwa san har yanzu muna a cikin al’ummar Hausawa ce wadda kuma take girmama addininsu da al’adarsu. Sannan har wa yau a nan din dai ka ga babu wani ban-daki musamman da aka ware don mata. Sai kuma maganar mukami, ban sani ba watakila don ba mu da yawa a wannan jami’a, amma dai har yanzu babu mata masu yawa da suke rike da manyan mukamai a wannan jami’a. Duk da yake an kafa kwamiti na daidaito wanda ya fito da wani tsari mai kyau. To sai dai har yanzu ban ga sun aiwatar da wani abu ba.
Akwai kalubale kuma a tsakani sauran ’yan uwa da abokan arziki, wadanda a lokuta da dama sai mun bata da su domin su suna bukatar lokacinka a koyaushe. Yayin da nake wajen wani nazari ko bincike watakila na kai koli ina shirin gangarawa sai ka ji an gayyace ni biki ko suna, idan kuma ban halarta ba, to kuwa na yi laifi. Haka za ka ga mutum ya kawo maka ziyara kana cikin wani rubutu ko aiki, kuma idan ba ka ba shi cikakken lokaci ba nan ma ka kara laifi. Ba kowa ne zai iya fahimtar irin halin da muke a ciki ba.
Sannan ka ga duk mata malamai a wannan jami’a sukan shiga kunci in dai suna raino. Saboda ba a yi wani tanadi da wurin rainon yaransu ba. Haka za ka ga muna ta hakilo a tsakanin gida da makarantar yara da kuma cikin jami’a. Ya kamata a ce jami’a ta samar da wurin rainon yara ga malamai mata da kuma dalibai mata masu raino. Yin hakan zai taimaka mana wajen aiwatar da ayyukan koyarwa da koyo a ta bangaren dalibai matan ba tare da sun raba hankalinsu ba.
Iyali
Ina tare da maigidana kuma muna da yara biyar ne dukkansu mata.
Yadd na hadu da mijina
Na hadu da mijina ne a gidan yayana wanda yake shi ma malami ne a nan jami’ar. A lokacin nakan zo hutu daga Katsina. To kasancewar shi ma a jami’ar yake aiki a cikin irin wannan zama na hutu da nake yi ne na hadu da shi.
Hali da na fi so game da shi
Hakuri, ina son wannan hali nasa sosai saboda shi mutum ne mai hakuri sosai.
Inda nake hutu
Ba na fita ko’ina zuwa hutu a gida nake hutuna tare da iyalina
Shawarata ga ’yan uwana mata
Su tashi su nemi ilimi domin sai da ilimi ne al’umma da rayuwa za su daidaita. Sannan su kasance masu gaskiya a duk inda suka tsinci kansu.