Malaman Jami’a sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani
Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya wato ASUU ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga yau Litinin. Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da hakan, bayan sun gudanar da taron Majalisar Zartarwa na kungiyar, inda suka yanke shawarar daukan wannan mataki.
Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya wato ASUU ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani daga yau Litinin.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da hakan, bayan sun gudanar da taron Majalisar Zartarwa na kungiyar, inda suka yanke shawarar daukan wannan mataki.