Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki
Malaman sun tsunduma yajin aikin ne domin ganin gwamnatin jihar ta biya musu buƙatunsu.

Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato, sun fara yajin aiki a karon farko tun bayan kafuwar jami’ar sama da shekaru 12 da suka gabata.
A wata sanarwa da shugabansu, Saidu Isah Abubakar, tare da Sakataren Jami’ar, Hassan Aliyu, suka fitar, sun bayyana cewa an yanke shawarar shiga yajin aikin ne a ranar Laraba.
- Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza
- Abba ya ba da umarnin bincike kan rage wa ma’aikatan Kano albashi
“Dukkanin harkokin karatu, karantarwa, jarabawa, duba ɗalibai da makin jarabawa sun tsaya har sai an cimma matsaya,” in ji sanarwar.
Malaman sun ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tilasta wa gwamnatin jihar, biyan buƙatun da suka jima suna gabatarwa.
Sanarwar, ta ce ba su gamsu da yadda gwamnati da majalisar gudanarwar Jami’ar ke tafiyar da al’amuran da suka shafi ci gaban Jami’ar ba.
Saboda haka, a taron da suka gudanar, mambobin ƙungiyar sun amince da fara yajin aiki daga ranar 26 ga watan Fabrairu, 2025.
Ƙungiyar ta ce ta kafa kwamitin da zai tabbatar da an bi umarnin yajin aikin a Jami’ar.