Malaman Kaduna sun fara yajin aiki

Yayin da ake komawa makaranta a yau Litinin kungiyar malaman makarantu reshen jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na fara yajin aikin sai baba-ta-gani don nuna fushinsu kan korar malaman firamare dubu 22 da gwamnatin jihar ta yi.   Da take mayar da maratani, gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk malamin da ya shiga yajin […]

Malaman Kaduna sun fara yajin aiki

Yayin da ake komawa makaranta a yau Litinin kungiyar malaman makarantu reshen jihar Kaduna ta bayyana aniyarta na fara yajin aikin sai baba-ta-gani don nuna fushinsu kan korar malaman firamare dubu 22 da gwamnatin jihar ta yi.
 
Da take mayar da maratani, gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk malamin da ya shiga yajin aikin za ta kore shi.

Gwamnatin jihar ta bayyana korar malamai dubu 21 da dari 780 wadanda ta yi zargin sun fadi jarabawar aji hudu da aka shirya musu don gano kwarewarsu